© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

472 29 1
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO..._*

Wattpad me on @MaryamAbdul559






{ 12 }



Kwance take  saman jikinsa ashe ashe, tana sanye da wani munafikin mini sket dako cinyoyinta bai gama rufewa ba, da wata kafurar rigar da ita da bra ba banbanci, fuskar nan Tasha kwalliya irin ta gogaggun yan duniya, hadda taron hancinta da sarka a k'afa da hannu irin dai na yan barikin nan kawai.....

Tunda ta fito daga dak'inta ko gefen da suke batayi gigin kallo ba, saboda sanin mugun halin amaryar gidan haka ta tasa k'eyar 'yar tata bayan ta doka mata gargadin kar ta yadda ta kallesu.....

Har ta isa tsakiyar falon taji muryar sa daga sama "da izinin wa kike fita gidannan kullum? Waima tsaya ina kike zuwa Dan nidai iya sanina baki da kowa a garinnan right?"

Duk da cewa taji zafin maganan haka ta dake ba tare data juyo ba ta bashi amsar da ta dace dashi "Naga kamar bakasan ma da dasuwa ta a cikin gidan ba bare kasan kwanciya da tashi na, naci ko banci ba, ciwo nake ko lafia akwai Wanda ka damu dashi a ciki?"

"Ke! Rashin kunya zakimin ne, waye sa'anki anan da har kike da bakin gayamin magana, bayan ina sane da ba abinda ke kaiki gidan bayan zaman munafurcin mu keda munafukar k'awar taki(abinda Sofie ta gaya masa kenan)....

"Well! Duk yadda kace hakane" ta amsa masa Kai tsaye, cike da kosawa da tsayuwar, kamar walkiya haka ta ganshi a gabanta yana huci kamar jaririn zaki, cikin dakewa da basarwa, tare juyar da kanta gefe tana tab'e baki...

Cikin ranta tana ganin shine best solution gareta na kwatarwa kanta 'yanci, a gefe d'aya tana kallon mugun k'arfin hali irin na d'a namiji, lallai namiji baida tabbas.....

Saukar Marin da batasan da zuwansa bane ya ankarar da ita tare da dawo da ita daga duniyar tunanin da taje, dafe gurin tayi da duka hannayenta biyu tana Mai bin fuskarsa da kallon Mai cike da ma'anoni da yawa bayan dinbin tsoro da mamakin da suka  bayyana akan fuskarta ta....

Gogan naku sai huci yake irin an b'ata masa rannan tare da sake d'aga hannu da niyyan k'ara wanke Mata d'ayan gefen da mari.....

Hannun aka rike Gam "haba my dear ai bai kamata ka mareta ba!" Sofie wacce ta iso gurin tace bayan ta r'ike masa hannun...

Salamah kam kuka take sossai ganin yadda ake tashin hankali a gidan nasu, hadda wakke fuskar uwarta da mari duk da bawai tana fahimtar duka abinda ke faruwa bane amma dai tasan ana cin zarafin mamarta ne, tuni zuciyarta ta tsani Dadyn nata da aunty amaryarsa.....

"Don me zakice kar na mareta, kina gani fa irin rashin kunyar da take min sai kace kanta aka Fara Karin aure, halan kishi hauka ne?"

Zaraf tace "kaida da amaryar taka duk bakwa cikin matsalata, daku da babu duk d'aya ne a guni, yo Allah na tuba ina abun yake da zanyi kishinsa dama wata abar kirki ce ka auro sai kayi tak'ama da fad'i yadda kake so ba wannan shaken ba" ras ras gaban Sofie yake dukawa, dama ance kowa yay xagi a kasuwa yasan Wanda yay dominsa, dake da gasken ita shaken ce, shiyasa taji zafin kalaman na umm Ruman....

"Ashe baki da mutunci bansani ba Umm Ruman, ashe baki tsotsi tarbiya ba?" Tofa na yan maid ta motsa wato rashin hakuri da kin barin kota kwana(inji su ali jita fa atoh hhhh)

"Kai ka isa kace banda mutunci banda tarbiya Harun? Aiko bakinka yayi kad'an ya fad'an haka muddin ni ban gaya maka kaidin butulu bane butulun ma bak'i, bance maka mara sanin halacci ba, ban kiraka mayaudari ba, ban kiraka mara adalci ba, ban ambaceka maciyin amana ba, Kai bakinka yayi kad'an ya kiramin rashin tarbiya"

Da yatsa ya nuna kansa cike da dacin rai da zafin zuciya "Rumana Ni kika Kira macuci, mayaudari mara Amana yau, nine mara adalci koh?"

"Koda Wanda na fad'a ba daidai bane a ciki?" Ta amsa masa Kai tsaye, Dan zuciyar ta riga ta gama cinta a yau sokoto da duk abinda ke cikinta sun fice Mata akai ta gaji, ta gaji da auren gaba d'ayan sa(Mata ayi hakuri dole ne fa a jarabceki ta yadda bakya zato a daidai wannan gabar hakuri ne kawai jigo kuma mafita a garemu, idan aka daure tare da mayar da al'amarin gurin Allah, to tabbas zai wuce domin duniyar kanta batazo Dan zama ba, Allah yasa mudace).

"Hakane kam, kamar yadda baki da amfani a gareni dan haka kije, kije na sakeki saki uku!!!"

"Innalillahi wa'innah ilairrajiun, ka sakeni fa? Nice yau umm Ruman ka saka Harun? Allahumma ajirni fi musibati wa kallifni khairun minha" cike da rud'ewa da rashin sanin me take fad'a tayi maganar......



😭😭😭😭😭  _wlh ba abinda yafi kalmar na sakeki zafi a zuciyar Mata, saki mummunar illah ce a rayuwar 'ya mace, yana daga cikin kaddara Mai tayar da hankalin 'ya mace, Allah subhanahu wa ta'ala yana cewa, halal ne kuma abinda na kyamata wato saki_


Allah ya datar damu duniya da lahira...




*_Maryam Abdul_*

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now