Innah wuro harara ta tayi tanacewa munafuka kuka me kikeyi tace inna kudin dazan aka kawo inba baffa suka bata gwaggo shiru tayi dan tadauka dagaske ne tacewa innah wuro bakomai yara sai hakuri tajuwa tabar gida ajiyar zuciya tasauke tanacewa innah har yanzu baffa baidawoba bataceman kalaba tayi gaba
DEEDAT yanzu baka yimana ko sati dayaba lumshe below eyes dinsa yayi yasaukesu akan Ammah sanan yacije lebensa nakasa sanan yace kiyi hakuri Ammah insha Allah 2 weeks kawai zanyi indawo tace shikenan Allah yakaika lafiya gashi wanan karon bakama hadu da dady ka ba sai jibi saidawo daga Dubai yace bakomai har yatashi tacemasa yawwa DEEDAT namata bangayama ba kanwar ka jiddah yar gidan kawunka zata dawo nan da zama rumtse idanun sayi sanan yabude aranshi yana cewa za akawo jaraba dai dan aduniya yatsani yarinyar batada tarbiya ko kadan bayason mace marar kamunkai Ammah takatsemasa tunani dacewa DEEDAT Allah yanuna man aure ka take ya tsuke fuskarsa kamar baitaba dariyaba fitayayi ranshi duk abace yake tsawa yadakama yaransa duk saida suka tsurata daganin yanayinshi sunsan basauki mai gadi kam saida cikinshi ya murda dagudu yaje yabude get tunkan ace yabude danyasan zasu iya tatakashi masu aiki ne suke gulmarsa lauratu nacewa wlh duk bakin ran oga DEEDAT yana burge ni wlh dazaisoni danaji dadi koda kullum zai dinga yankan namanjikina zaliha tace dan Allah rufa mana asiri karkisa wadanan murdadin yaran nasa suji sananko ayi fatenmu agidanan tsuki lauratu tayi takama gabanta suna isa airport yafita ko kallansu baiyiba ya wuce cikin jirgin lumshe idanunsa yayi wata budurwace tazo tazauna kusa dashi tanace masa hy ko kallo bata isheshiba aran shiko cewa takeyi duk mata haka suke basuda aji tsuki yasakeyi akaro na ba adadi takatse masa tunani dacewa am laila and you kala baicemataba aranta tana yaba kyanshi tanacewa kodai kurma ne wata zuciyar tace kai ba kurma bane amma gaskiya yanada kyau guy dinan karshene
inna wuro nashigowa dakin tasamu sa imah tana dungura kai tana dagowa wai sallah takeyi innah wuro tace ke mekikeyi haka tace sallah fa nakeyi batace mata komaiba tafita dan jiyo sallamar maigidanta tana amsa masa tare dayimasa sannu dazuwa ya amsa yanacewa inah yar baffa sa ima tafito tana murmushi tace gani baffa shima murmushi yayi yakamo hanunta yazaunar da ita yace sa ima dan Allah kidaina rashinji kinji ko tace to baffa yace wlh banaji dadin yanda mutane garin nan suka tsaneki inah ji ajikina zaki zamesu Alkhairi nan gaba koba raina ki rike mutumciki kinjiko yar baffa dukda karanci shekarunta dan bazata wuce 13 years ba amma ta fahimci baffanta bayajin dadi dagowa tayi tanacewa baffa bakada lfy ne shiru kawai yayimata dan Allah kadai yasan yanda yakejin jikinshi ledar dake gefenshi yamikamata yanacewa tashiga ciki tashi tayi duk jikinta yayi sanyi da kallo yabita har tashiga ciki ajiyar zuciya yasauke yana mai jingina kansa da bango inna tace masa sannu malam Allah yabaka lfy ya amsa da amin
Yau litinin takasancewa sa ima bakar rana agareta dan yaune tarasa jigonta kuma masoyi agareta wato baffanta kuka takeyi kamar ranta zaifi duk mutanen dake cikin gidan tabasu tausayi gabadai mutuwar baffa yasata tayi sanyi
Kwance yake a gidanshi daya sauka yana huce gaji dan 4pm yanada meeting tsuki yayi tare da janyu wayar sa yana kiran Ammah yake gaya mata yasauka lfy tayi hamdala tare da fatan samun nasara yayi mata godiya tare da tsinke wayar number dady shi yalalibu yakirashi bugu biyu ya dauaka papa anwuni lfy tadayan mangaren Ahj Hashim ya amsa cike da farin ciki shidai aduniya babu abunda yakeso kamar dansa deedat dan sunan mahaifinsu ne akasa masa wato AHMAD shine sukecemasa deedat dady yace masa Ammah ka tace yau kakoma India deedat yace eh papa 2 weeks kawai zanyi indawo shima addu a yayimasa tare da yimasa sallama baidadeba baccin gajiya ya ibeshi
Ta bangare sa ima kuwa wata irn nutsuwa tasaukar mata bata magana tazama shir 2 bata shiga mutane suna zaune atsakar gida innah wuro nayimata fadan kin cin abinci kuka tafashe dashi innah tsaye kawai tayi tana kallonta cikin kuka sa ima tace innah dan Allah mubar kauyen nan mukoma birni innah wuro shiru tayi tana tunani wasiyar da malam yabar mata nacewa duk abunda sa ima keso indai tanada karfin yimata idan kuma baisaba ma addini ba to tayimata jijigata da sa ima tayine takatsemata tunani tasauke ajiyar zuciya tacemata toshikenan indai zaisakaki farinci dariya sa ima tayi tace zamukoma birni
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...