🌹🌹DEEDAT🌹🌹
Wattpad
Rashmarrka
Writing by (maman khady)
Page 16
Saida yagama yawon unguwar talakawa sanan yayima driver magana yace muje gida OK sr kawai driver yace suka nufo gida lumshe idanunsa yayi yana tunani Wai Anwar aure zaiyi duka Anwar nawayake baikarasa tunani ba yaji gabadaya motocinsa sun tsaya yabude idanun sa wani matashi yagani tsaye yanata masifa Wai andakar masa mota sai hakuri akebashi amma kamar kara tunzura ran DEEDAT yafara baci gashi yagaji yanaso yaje yayi wanka ko zaiji dadin jikin shi amma saurayin nan yaki basu hanya har idanun DEEDAT sunfara canja kala akan bacin rai baima jira abude mai mutar ba yafito kowa yana ganin sa sai yakauce dumin tsira da mutunci sa dan duk Wanda yaga yanayinsa yasan ba mutunci afuskarsa gaban matashin yatsaya bakaramin kyau yayiba Amma fukanar kamar an aikomasa da manzo mutuwa matashin bakula da wanda yake gaban saba sai masifa yakeyima wani tsoho yanacewa talakan banza talakan wofi wlh ko gidan ka zaka sayar saikabiyani motata take ran DEEDAT yakara baci alama yayima yaransa da sukaraso mutane kuwa sai cewa sukeyi idan kana karyar rashin mutunci kazo hanun DEEDAT kagama yawo duk da rashin mutunci da saurayinan yayi saida suka tausayamai Dan sunsan bakaramin hukunci zaiyimasaba da wata irin murya yabuga masa tsawa duk mutanen gurin saida tsorata sanan yace waye ubanka Kalmar da tafito bakishi kenan atsorace matashin yace Alhj Ibrahim jinjina kai DEEDAT yayi yace to ko ubanka bai isa yatare min hanyaba barekai kakira ubanka kagaya masa katarema DEEDAT Hashim hanya kaji mai zaicema ka sanan yakalli yaranshi yace kudagamin wanan motar kwasar sharar Ku konata inga ta iskanci tunda gogeta akayi yakeyiwa mutane masifa ni zankonata saurayin yace ka kona ingani tunda uban.. Bakarasaba yaji wani mugun bugu abaki take jini yaballe masa yaba yaransa umarni dacewa kuyanko min harshen sa mai kokarin zagina ko Ibrahim bai isa ya zageniba barekai
****
Har malam yazo Aliyu bai farkaba wani magani yabama mamy yace ta bashi yasha ko kadanne sanan yadauko ruwan zam zam yace abashi Kofi Sarah ce taje takawo masa addu a yayi sanan ya shafa masa afuska Ajiyar zuciya Aliyu yasauke sanan yabude idanu dasauri yatashi zaune kofin malam yamika masa yace kasha ba musu yakarba yasha yana dire kofin yafara kakarin amai wani irin bakin Amai yadingayi saida yagama sanan yajingina da kujera yana sauke numfashi sanan yafara tuna komai dayafara hawaye suka dinga gan garowa yana danasanin sanin sadiya arayuwarshi malam yace Alhmdulillahi mikama mamy wani magani yayi yace yarika shafawa idan zai kwanta godiya mamy tayi sosai sanan tace meye goro dazan bayar murmushi malam yayi yace a a hajiya yata tabiya komai har magani sallama yayi musu sanan ya fita kallon SA IMAH mamy tayi tace ya akayi kikayi kikasan babban malami nan SA IMAH tace wlh nima bwata yar ajinmu sumayya ita tahadani dashi danacemata inah neman malami zanmasa tambaya sanan mamy tace ainah kika samu kudin biyanshi tace innah ce tabiya kallon innah mamy tayi zatayi magana innah tace bari kigani indafama yarona wani Abu murmushi mamy tayi tace dawo muyi magana masu aiki zasu hadamasa innah tace to bari inje inhada kayanmu kinsan gobe zamu koma gidan mamy tace ai gobenma saida dare dan haka dawo Sarah tace inah zasuje mamy tace gidansu zasukoma sunsayi gida Aliyu baisan abunda akecikiba dan wani irin bacci yayi gaba dashi innah tace wace magana zamuyi mamy tace ya akayi kika biya kudin magani bansani innah tace idan zan biyawa SA IMAH kudin magani sai nazo nagaya miki gyaran murya SA IMAH tayi duk juyowa sukayi tace innah dan Allah kibani mutafinyanzu mudawo mamy tace inah zakujene Wai dabakuson zama guri daya Sarah ce takatsesu dacewa mamy wai inah zasu komane innah ce tabata amsa dacewa nan kusane makotanku najikin gidanan da murnah Sarah tace Alhmdulillah gabaday dariya sukayi dan yanda Sarah tayi maganar mamy ce tace yawwa kutashi na aikeku gidan hajiya bilkisu kukaimata sako daganan kuje shopping din damurna SA IMAH tace yeee zanga my twice tsuki Sarah tayi tace zakidaiga marasa jin magana wlh yaranan basaji ko kadan ga barnar tsiya SA IMAH bata kulataba tace mamy kawo sakon tashi tayi tanacewa bari indauko tashi SA IMAH tayi tace bari indaukowa my twice gift part dinsu ta nufa dasauri koda tadawo tasamu mamy afalon karba sukayi SA IMAH tanacewa wlh zuwa zanyi inkoyi mota innah tace yakamata dariya sukayi duka banda SA IMAH datasan bakar magana innah tayi mata driver suka sama zaune shida baba maigadi suna fira fada masa inda zasuje tashi yayi yace to baba sainadawo maigadi yayimusu adawo lfy get yabude masu ahankali yake tuki har suka isah gidan
****
DEEDAT mota yakoma yanacewa kai yisauri kajamuje sauran yaran sa ne suke budamasu hanya har sukafice aransa kuwa cewa yakeyi bakaiba har ubanka saiyasan wayeni dan inah tunanin baisanniba suana shigowa layin jiniya kawai kakeji kamar gwamna ne yashigo unguwarZaune suke afalo twice duk sundamesu da surutu SA IMAH kuwa sai biyemusu takeyi hajiya bilki tace Wai bazakusauka ba kunwani zo kundami mutane HANEEFA ce tace haba mamy kinsan fa kwana biyu bamuje gurinta ba murnan ganinta mukeyi hmmm kawai mamy tace jiniya sukaji dagudu haneefa tasauka akan cinyar SA IMAH tanacewa yeeee ya DEEDAT yadawo zamuje shopping da gudu tafita Sarah kuwa zaro idanu tayi tanacewa kashinmu yabushe yau SA IMAH kuwa duk da batajin tsoronsa amma jin ankira sunan shi saida gabanta yafadi fuskewa tayi
DEEDAT kuwa ranan ahade yake tun shigowar su Anwar yakeyimasa magana amma yayi masa banza amma gashi daganin haneefa hardasu dariya yanacewa my baby I miss u yadagata yanajuyata sunata dariya da mamaki Anwar yake kallon su part din mamy suka nufa Anwar yana biye dasu imani duk yacika masa ciki DEEDAT yanasaka kafarsa yaji gabansa yafadi lumshe blue eyes dinshi yayi sanan yasake budewa murmushin mugunta yayi ganin wacce ke zaune cike da makirci yanufi gurinta yanacewa A a hajiyata harnan kika biyoni ainace zanzo ko nifa banason naci nace kirabu dani amma kinki bude baki SA IMAH tayi kamar wawuya tana mamakin wanan sharrin itada ko saurayi yace yanasonta batada lokacinshi bare tace tanason wani Sarah kuwa da mamaki take kallon SA IMAH Murmushi Anwar yayi dan yasan sharri yakeyimata dan koshi yace yana sonta amma sai tabashi hakuri dacewa ita babu soyayya atsarinta mamy kuwa kallonsu kawai takeyi Rana nazarinsu shikuwa gogan yace haba hajiyata yakikeyi kamar bakisan komaiba yanayi yana murmushi yana shafa gemunsa nagayu ko kunyar mamy bayaji ya matso kusa da ita yanacewa yakikaga kafcen nawa haka zanta kuntata maki tare da baki kunya hararar sa tayi kamar idanunta zasu zazzago baki yabude yanacewa karkisa hantar cikina tafito wanan hararar haka yana dariyar shakiyanci Sarah tayi karfin halin gasheshi fuska asake ya amsa yanacewa kawar budurwata kunzo gaida surukarku mamy kuwa aranta addu a takeyi tanacewa Allah ya tabbatar SA IMAH daker tace mamy zamu tafi caraf haneefa tace sweet aunt bakince sopping zakujeba gyada mata kai kawai SA IMAH tayi duk tamatsu subar gidan haneefa tasake cewa to kibari mutafi da baby karfin hali SA IMAH tayi tace no sweetheart tare muke da driver yayi caraf yace haba hajiyata kinajin kunyane kizo muje kawar mu taso muje duk jikin SA IMAH yayi sanyi da wanan iyashegen nashi tunani takeyi meyake nufi da tuzarta ta dayakeyi haka gaba tayi batace masa kalaba bayanta yabi yana yaba mata bakaken magan ganu kuma yana dariya saika rantse da Allah maganar kirki sukeyi nan kuwa Alkawarin nakasa mata rayuwa yakeyi sanan agaban kowa zan nuna kince kina sona Nima inah sonki kirubuta ki ajiye sai na wulakantaki kamar yanda kika wulakantani bana yafiya bana daukar iskancin kowa kuma sai kinyi danasanin sanina arayuwa azafafe tajuyo tace kadaina ganin inah yimaka shiru nima banda sauki banadaukar raini muje zuwa zanga wanda zaicinye wanan game din kuma na tabbata sainayi ma game over murmushi yayi yace really tace yes yace OK mufara daga yau amma ki gargadi zuciyarki karta fada son dan kya kyawan gaye irina tace abunda nakeson gayama kenan
Sarah da haneefa ne suka karaso sanan suka Shiga mota tare suka zauna da DEEDAT kowanen su yana shan kanshi Anwar da ya makale sai yazauna dasu yana gaba yana kunshe dariya saif kuwa yana motar da Sarah take sai surutu yakeyimata dama saif badai magana ba ita kuma sai aji take jamasaMore comments
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...