🌹🌹 DEEDAT🌹🌹
Writing by Rashida usman
Wattpadrashmarrka
Page 22
Bangaren jiddah kuwa tacika tayi fam batama bari taron yatashi ba tawuce sbd yanda ranta yake bace
SA IMAH kuwa tana isa gida ko magana da Sarah takeyimata bata kuba ta wuce cikin gida tanaji yanda ranta yake bace DEEDAT bakaramin shige Mata hanci yakeyiba batason mu amala damaza sai burinta yacika naganin bayan baffa Aminu da sauran mutanen rugarsu shigowar innah shiya katsemata tunani bakin gadon innah tazauna tadafata tace yar baffanta meke damunki kundawo shine baki shigoba niswa SA IMAH tace innah wlh tunanin yanda rayuwa ketafiya inah tunanin yanda kauyen mu suka tsaneni kinga yanzu rabonmu da kauye 8 year's amma wlh har yanzu inatuna yanda family dinmu suka watsar damu nisawa innah tayi tace kiyi hakuri kimaida hankali akan karatunki watarana sai lbr sai sunyi danasani SA IMAH tace innah wai ni yar rugar jauro wacce babu mai kaunar ganina yau nice wai nake gogawa da yayan gwamnoni innah tace ki godewa Allah Dan gaskiya da baffan ki baiyi tunanin tattara dukiyarsa guri dayaba dayanzu hamma Aminu bazai barmana komaiba SA IMAH tace insha Allahu zanyi karatu sosai sainazama likita innah tace Allah yataimaka kwanta kiyi bacci gobe kema zaki rika fita shagonmu kema kiga yanda akeyi kafin jarabawar ku tafito murmushi SA IMAH tayi tace innah nima inason indinga zuwa sbd banason inah hada kaina da yayan masu kudi kekai nakeda aduniya shafa kanta innah tayi kikwanta gobe da wuri zamufita dan akwai wadanta zamuyi magana dasu gyadamata kai kawai SA IMAH tayi saida takashe wutar dakin ta rufomata kofar
tana ganin innah tafita cike da murna takira Sarah tagayamata gobe itama zata fara fita daya ke itama Sarah tanada shagon datake shagonsu na make up take zuwa kafin sukoma makarata
sosai Sarah ta tayata murnaWashe gari
takama daurin auren Anwar domin DEEDAT yahana duk wata bidi a dakyar ya yarda ayi kamu da dinner bakaramin haushi Anwar yajiba dan dai gabaday mamy da dady sun goyi bayan maganar DEEDAT
Karfe 2:30 duban mutane suka shaida daurin auren Anwar damasoyiyar sa muneerat
Anagama daurin aure DEEDAT yace shi zai wuce Abuja babu yanda ba ayi dashiba yatsaya ayi dinner Amma fir yaki yace shi yanada aiki agaban shi ba wanan sha shanciba bakaramin baci ran Anwar yayiba ko kamu dakyar yashawo kansa ya yarda zaije saif yace haba blue eyes meye haka katsaya ayi dinner dakai mana tsuki yayi yace wlh kasan banson kallo dariya saif yayi yace kaidinne kacika kyau kamar kai kayi kan ka tsuki yayi yace kafin kusake ganina garin nan bayanzuba tsuki Anwar yayi yace karma kadawo Dan iska kawai ai wlh matar ka tashiga ukku ya tabe baki yayi alamar ko ajikinsa🤷🏻♂️ saif ya kalla yace ya zakazo mutafi ko sai angama bidi a dariya saif yayi yace nikam bamuyi sallama da new baby dinaba tsuki DEEDAT yayi yace kai kasani adai ji tsoron Allah namamajo kawai sai yace najidai basake magana ba yafita daga hotel din da suka koma sbd jama a da suka cika gidan baije gidanba kawai yakira mamy da Ammah yace masu yawuce yasha fada sosai gurin Ammah dan wani lokaci tanajin takaicin halin dan nata da takeso tamkar rayuwa saidai kawai tayimasa fatan sauka lfy
Tare da tarin sojojin sa suka wuce saif yaraka shi airport Anwar kuwa ko kallon shi baiyiba bare yaraka shi
Suna cikin tatiya saif yace wai kunyi sallama da SA IMAH kuwa baki DEEDAT yatabe yace ni har namanta da anhaliceta adoron kasa saif yace Allah yashirya mana kai baicemasa komaifa yafita daga motar yanufi gurin jirginsu da aketa announcement din tashinsa nan da 10 minutes yana shi ya nemi number din sit shi yazauan yajawo laptop dinshi yafara aiki domin yana ya gwadama su Alhj bala matsayinsu domin duk wanda yace zai taba masa family bazai barshiba bare kuma abban shi koda yasauka anzo daukarshi gidanshi yanufa baije gidan mahaifin Saba wanka kawai yayi yacanza kaya marar nauyi boyayar hanyarsa yanufa wacce babu Wanda yasan da zamanta hular rigar daya dora saman kayansa yajanyo yarufe rabin fuskarsa sanan yasaka handkerchief yarufe daga hancinsa zuwa bakinsa yafara shiga kwantaina kwantaina din daya gani yana bude daya bayan daya duk maganin da kwanan watasu suka kare ne camera yafito da ita yafara dauka can wani kilatacen guri mutane yahango sunata fitar da magani suna sakawa acikin sababin kwalayen da sukazo dasu wani malala cin murmushi yayi yace wlh saina durkushe company dinka na magani har yagama daukar abinda zai dauka yayi gaba batare da kowa yaganshiba*********
Yau su SA IMAH zasuje suduba ko sun samu admission a teaching hospital dinda suka cika
Alhamdulillah duk sun samu gurbin karatu amakaran SA IMAH tafi kowa murna burinta zai cika zata zama likita
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...