🌹🌹 DEEDAT🌹🌹
Writing by RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allahu))🤜🤛BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
PAGE 37
Ƙwafa tayi sanan ta fita.
Kutashi muje kafin ya shigo."Tashi sukayi suka bi bayanta."
"Koda ta fita yana waya saida tajira ya gama sanan "
A tare suka shigo kan kujera mai zaman mutum ɗaya ya zauna, itama zama tayi.Wai dagaske yau zaka koma Abuja?
Da mamaki ya kalle ta, sanan yace bakiso na tafi?
Shiru tayi ba amsa.
Murmushi da ba koda yaushe ya keyinsa ba, yayi yace ah kice kin fara missing ɗina tun kafin na tafi."Baki ta turo tana ƴar shagwaɓa wacce batama san tanayiba"
"Dariya yayi" aiko baki tasaki tana kallon shi ganin yana dariya zata iya rantsuwa bata taɓa ganin yana dariya ba saidai murmushi, shima ba koda yaushe ba.
Gira ɗaya ya ɗaga yace wanan kallonfa na, nawane?
Sunne kanta tayi ƙasa saboda kunya.
Wanan kunyar taki a hankali zan cire ta.
Da sauri ta ɗago kanta, kanne mata ido ɗaya yayi."Baki tasaki, a ranta kuwa cewa takeyi wai dama haka yake bayada kunya?"
Ah yarona sannu da zuwa.
Yi hakuri na barka kana jirana.Bakomai mama ashe yau baki fita ba?
Eh wlh baƙi nayi shiyasa ban fita ba.
Naga ankawo mana sojoji shine nace ko lafiya aka kawo su?
Lafiya lau mama kawai naga bakuda security ko guda shiyasa nace suzo nan su baku tsaro."Yaro na gashi gidan namu babu gurin da zan sauke su shine nace kawai a barshi."
Shiyasa ma nazo ai mama, hannu yasa a aljihu ya fito da makullai, yace mama gashi gida nane dake G.R.A ku koma can kawai wanan gidan yayi maku kaɗan.
A'a bazan karɓa ba kawai abar security ɗin kawai.Mama dama ashe baki ɗauke ni a matsayin yaron ki ba, ni a tunani na duk ɗaya kika ɗaukeni da Sa'imah, mama duk wanan ba komai bane indai inada matsayin zama yaron ki to duk abunda na baki bazaki ƙi karɓa ba.
Bahaka bane yaro na idan na karɓi gidan kai kuma fa?
Karki damu mama ni inada gidaje dayawa a garin nan dan haka kawai kusa rana ku koma can ɗin.
Murtuƙe fuska Innah tayi tace kaga Deedat tun muna shaida juna ka sanƙami makullan ka ka ɓace ka bani guri.
Tashi yayi yace mama ni sallama nazo maki zan tafi Abuja yin wani aiki, kuma zan ɗauki lokaci kafin na dawo kano idan takama ma aikin ba'a ƙasar nan zanyi shi ba dan haka ga makullai nan ni bana kyauta aki karɓa, na bakisu a kyauta badan komai ba sai dan ina kallon ki a matsayin mahaifiyata.
Ni na tafi kiyiman addu'ar samun nasara."Daga haka ya ɗora makullan a kan kujerar da ya tashi ya fita"
Da sauri Sa'imah tabi bayansa, jimana tace da shi.
Tsayawa yayi batare da juyo ba, ƙarasowa tayi gaban sa, tace meyasa kabamu gida alhalin munada shi?Nasan kunada shi madam ki tuna abunda ya faru dake jiya sanan kuma kina tunanin duk wanda ya turo a sace ki bazai shigo nan gidan bane?
Bakisan meyasa nace ku koma canba inada dalilin cewa ku koma can ɗin.
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...