page 53

2.1K 123 7
                                    

🌹🌹 DEEDAT🌹🌹

Writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah))🤜🤛

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

PAGE 53

Hmmm yaro kenan kai kana tunanin zaka iya ja damu a cikin wannan al'amari.........

Dawowa yayi yace inga ba amfanin na tuna maka waye ni da kuma abinda zan iya ka zuba ido ka gani abin da zai faru da kai kwanan ni Ahmad Hashim nayi ma maka alƙawarin tarwatsa duk mumunan ƙudurin ku, kuma ka zuba ido ka gani.

Ke kuma ba sai nayi maki magana ba ki tattara komatsanki ki koma gurin iyayen ki idan kika bari na sake karo dake saina tar watsa kanki da bindiga.

Ai baima kai ƙarshe ba ta antaya da gudu ɗaki domin tattaro kayanta.

Yanzu kam da zai fito baiyi wani ɓoye_ɓoye ba kai tsaye ya fito yana tafiyar sa.

Abban Anwar ne ya fito yana cewa kar ku bari ya fita ku tar watsa Mani kansa.

Har ya ɗaga ƙafa ya cigaba da tafiya sai kuma ya tsaya ya fito da bin digarsa ya samu wani dakali ya zauna yace duk wanda yake so uwar sa tayi kwanan baƙin ciki matar sa ta zama bazawara ƴaƴan sa su zama marayu to bisimilla yazo.

Du tsaye sukayi babu wanda yayi gigin tunkara sa dan wani ƙwarjini ya musu da yanda suka ga yana magana, da gadara sai suka ji shakkar tun karar sa.

Tashi yayi murmushi kwance a fuskar sa yace Abba idan kana son ganin baya na to ka nemi maza ba mata ba dan waɗannan basu da ban_banci da mata kafaɗarsa ya bubuga ya juya yayi tafiyar sa cike da izza da ƙadaita, suna ji suna gani ya tafiyar da babu wanda ya iya cemani koda uffan.

Motar sa ya ja yabar gurin  gudu yake kamar zai tashi sama duk inda ya wuce mutanen dake gurin sun bisa da kallon wanan lafiya yake kuwa.

Cikin ƙan_ƙanin lokaci ya kawo gida dan ba ƙaramin gudu yayi ba, tunda yaransa suka ga yanayin shigowar sa suka san ran oga a ɓace yake yasa suka kama kansu tun kan ya huce akan su.

A bakin ƙofar shiga babban falon gidan ya ci karo da Iya, yawwa ɗan albarka muje ka rakani gidan su maman Sa'imah.

Fuskar a haɗe yace kije mana bakiga yanzu na dawo ba......

To sai kaje ba gajiya kayi ba komai kayi sai ka raka ni.

Kansa ya dafa dake sara masa kaɗan_kaɗan, juyawa kaiwa yayi ya nufi hanyar fita, bayan sa tabi tana cewa yau miskilanci naka akai na ya sauka?

Banza yayi da ita ya ci gaba da tafiya, kai wai haka ake rakiya kawani wuce gaba zungura_zungura.....

Tsaya wa yayi yace"Allah Iya da bake bace da yanzu......"

Ka ƙarasa mana da yanzu ka sa anmin mugun duka ko.

Nidai banceba kuma kin isheni da surutu, zaman ki da Gwaggo ta koya maki surutu ko.

Bansaniba aku ta dafa mani naci shiyasa nake surutu ƙarewar ta koya mani haka suka tayi har suka kai bakin get, yace " oya shiga ni gida zanje inada abunyi."

Ƙwafa tayi tace kai ka sani daga haka ta shiga ciki shi kuma ya juya ya koma.

Koda ta shiga Sa'imah ce kaɗai a falon itama ta shirin tashi sai taji sallamar Iya.

Ah tsohuwa kece da ranar nan?

Ban saniba aini faɗa nake dake tun zuwan ki na farko baki sake zuwa ba.

DEEDATWhere stories live. Discover now