🌹🌹DEEDAT🌹🌹 Wattpad rashmarrka Writing by (maman khady) Page 18 Basu dade da

2K 107 0
                                    

🌹🌹DEEDAT🌹🌹
Wattpad
rashmarrka
Writing by (maman khady)
Page 18
Basu dade da isa airport dinba jirginsu Ammah yasauka cike da kasaita take saukowa abayanta kuwa jiddah ce tasha make up tasaka wasu kananu sai wani shan kanshi takeyi DEEDAT yanaganin Ammah sa yanufi gurinta ya rungumeta yanacewa I miss u Ammah dariya tayi tanacewa bawani bayan kazo kano kayi zamanka dariya yayi yana hade hanayensa yanacewa sorry my Queen kina raina kullum murmushi irin nasu namanya tayi tare da dangwara masa kai tace miss u too wata murya yaji abayan Ammah tana gaisheshi yawani irin hade rai kamar bashi bane yakeyin dariya yanzuba wani banzan kallo ya wurga mata saida tashiga taitayinta  tsuki yaja yabudema ma Ammah mota tashiga  jiddah matsowa tayi zata bude wata uwar tsawa yadaka mata saida ta tsorata taja dabaya Ammah tace meyake faruwane dan tasan basa jituwa yanzunan zasu saida hali tsuke fuska yayi yace bazata shigarmin mota ba saidai tashiga taxi Ammah tace haba DEEDAT duk motocin nan kace bazata shigaba yace nafa gayamata bazata shigaba idanko tashiga tasan sauran idan shiga zatayi ga fili gamaidoki amma tasani saina yimata mumunan hukunci Ammah kuwa shiru tayi dan inyakafe akan abu tosai ya aikata itakuma batason wani tashin hankali kallon ta damaida gurin jiddah tace to kisamu mai taxi sai yakawoki gyada kai tayi kamar saliha aranta kuwa cewa takeyi zan dauki duk wani wulakancika idan kashigo hannu zaka San ka wulakantani

Mamy nagani su SA IMAH cike da mamaki take kallonsu tayidai shiru taji ko mamyn tasuce ta aikosu Sarah ce tace sorry mamy munbata miki lokaci bamu tashi da wuriba mezamuyi yanzu mamakinta ya karu daurewa tayi tace babu komai angama abunda za ayi ai Sarah tace to Allah yakawota lfy mamy tace amin SA IMAH tace to bari mutafi mamy tayi murmushi tace meye kukeyima sauri haka kujira ta karaso kugaisa mana shiru sukayi dakansu sbd basason yima babba musu SA IMAH duk atakure take mamy na ankare da ita tadai kyaletane kawai aranta kuwa cewa takeyi to ko DEEDAT ne yace suzo
Jin bude get dakuma jiniya yasa mamy cewa gasunan sunkaraso ta shi tafita dan taro aunty tata  cike da murna murmushi ne kwance afuskarta tanzuwa ita tafude mata kofa tafito hugging din junansu sukayi kowanensu murnan ganin dan uwansa yakeyi falo suka nufa DEEDAT nabayansu yana dariya jindadi bakaramin dadi yakejiba idan yaga iyayensa ahaka  falo suka shiga yana shigowa idonsa yasauka akan SA IMAH murmushi yayi zaifara magana jiddah tayi sallama amsa mata su Ammah sukayi tagaida mamy bayabo ba fallasa ta amsa mata dan itama batason yarinyar ko kadan Ammah tace ah Sarah kece inah umman taki dukawa sukayi har kasa suna gaidata ta amsa da fara a DEEDAT yace Ammah ingaya miki wani abu kuwa Ammah tace eh gayaman  kallon SA IMAH yayi yace hajiyata infada mata atsorace tadago duk idanunta sun cika da hawaye Ammah tace menene wai yace hmm Ammah dama cewa tayi tanasona shine nikuma na amsa mata nima inah sonta ammafa akwai naci wlh kulum tana hanyar nemana SA IMAH kuwa tuni hawaye sun wanke mata kyakyawar fuskarta baki yarike yanacewa nashiga ukku ni Ahmadu meyafuru hajiyata Ammah girgiza kai tayi tace wanan itace daidaida DEEDAT ko sallama bata iya yiwa su mamy ba tafita da gudu bayanta yabi  jiddah kuwa kamar ta hadiye zuciya tamutu dakin baki tanufa ranta duk abace aranta kuwa tace wlh saikingane kinason wanda nakeso dan saina dauki mumunan mataki akanki bayan wucewar jiddah Sarah ta tashi itama domin tasamu SA IMAH sukoma gida Ammah ta tsayarda ita tace wai dagaskene Sarah bata boyemusu komaiba tagayamasu takara dacewa itah SA IMAH babu abunda tatsana kamar kace kana sonta bare ita ce tanasonka abune mai matukar wahala  ta tsani soyayya shiyasa kalmar inasonki take matukar batamata rai har tayi kuka jinjina kai Ammah tayi tace to kigaida ummantaki kicemata zanzo da to ta amsa tafita kallon mamy Ammah tayi tace me kika fahimta nan murmushi tayi tace ai yarona yakamune amma yaki yarda da haka Ammah tace shiyasani maitauarin kan tsiya

Sunafita tatsaya tace wlh wlh wlh haduwarmu tagaba bazatayi kyauba kafita hanyata menatare maka bana son ka kuma bazantaba sonkaba yace to wayake son nakine ko angayamiki raina bays baci aduk nanu ki amatsayin budurwata mtswwww bagidajiya dakema mezanyi dake to kisani nawani lokacine zamana dake kuma inagama abunda zanyi dake zan koraki dallah matsa inwuce yar kauye kawai nice bagidajiya ai wlh zakaga gidadanci wlh da sainayima rashin mutunci daga haka tajuya tafita daga gidan da dan gudu Sarah takaraso gurinta tace sister sorry SA IMAH ko kallonta batayiba motace tafaka agabnsu yace oga yace kushiga nasaukeku tsuki SA IMAH tayi tace ogan banza ogan wofi dagaku har ogan naku saina ci kaniyarku masu zubin samudawa kawai shidai ko gizau baiyiba dan gwanda zaginta da rashin mutunci oga yace yihakuri kishigo tace idan baso kakeyi nayima rashin mutunci ba ka kama gabanka aranshi kuwa cewa yakeyi daba dan yarinyar boss bace dababu abunda zaihana yabi takanta damota sai tamutu  binsu yadingayi yana cewa dan Allah kirufa min asiri kishigo mutafi dan Allah badan halinaba dama tagaji da tafiya  dan akwai nisa kafin sukai inda zasu samu abun hawa amma taki shiga Sarah kuwa sai magiya takeymata tanacewa kiyi hakuri mana mushiga wlh nagaji dakyar da sudin goshi suka samu tashiga ajiyar zuciya driver din yasauke yanace kintaimakeni hajiya batakulashiba har suka kawo gida yasaukesu yajuya

DEEDATWhere stories live. Discover now