🌹🌹 DEEDAT🌹🌹
Writing by RASHIDA USMANWattpad
rashmarrka
🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page 29
Wai munawwar me yasa baka jin maganane nace ka rabu dashi amma sai kunfar baki kakeyi kamar idan aka barka dashi zaka iyayin wani abu to kasani, idan kace zakaja da shi daga ni har kai sai ya gasa mana aya a hannu.
Wai me kake cewa ne Abba kasan ni fa kuma kasan babu mai iya ja dani to meyasa kake tsayar dani akan wanan k'aramin alhakin. Taahi yayi yana huci yabar falon.
Kiransa baban yakeyi amma ko ya waigo bare yayi tunanin zai dawo.Direct part dinsa ya nufa yana huci kamar namijin zaki yana shiga freezer dake girke a falon ya nufa ya d'auko kwalbar giyar sa, marfin ya b'alle kai ya kafa ya fara kwan kwad'a saida ta k'are sanan ya d'auko wata a takaice dai saida yasha kwalba 3 sanan ya baje a falon kamar matacce.
*************
Saif kasamu wani information a kan wanan yaron da nace ku rike.
A a haryanzu bai yi magana yaron yanada taurin kai.
Hmmmm shikenan ku ajiye man shi nida kaina zan masa tambaya.
Tab lalai wanan tasa ta k'are sai yayi dana sanin kin gayamana.Canza maganar yayi da cewa, Saif inason a bama gidan su Sa'imah tsaro sanan inaso duk inda zataje ya kasance akwai wand'an da suke tare da ita.
Sanan ka tattaru man wad'an can sokayen.Ai tunjiya na saka wasu su basu tsaro dan nasan munawwar bazai hakura ba, sukuma wad'an can sokayen zasuyi bayani inda sukaje har haka ta faru.
Hmmm kar kasamu damuwa indai akan munawwar ne duk motsinsa akan idona, yanzu dai ba wanan ba a kwai kayan da zasu shigo cikin garin nan misalin 2:30am za'a shigo da kayan ta barauniyar hanya dan haka ka gayama su captain Jawad su zama cikin shiri anjima zan gaya maku imda zamu hadu, kuma kar kabari kowa yasan maganar nan saga ni sai kai sai kuma captain Jawad da captain Sageer.An gama ranka ya dade Allah ya k'ara girma yasa Kuma afi haka."amin" kawai yace, bari naje gida tun safe na fito yanzu mamy tanacan duk ta damu.
Shikenan nikam ai sai dai zuwa gobe tunda zamu fita da dare kaga kenan bai kamata mu fita tare ba sbd tsaro.Hakane kam shikenan sai mun hadu anjima.
**********
Sai kaida kawowa Innah keyi bata daki bata kitchen, Sa'imah kuwa tana kwance chart takeyi da maman Afnan suna magana akan abunda ya faru dazu da safe.
Innah wai lafiya kike wanan sintirin me kikeyi tun dazu kin k'agara zama?
Hmmm kedai bari y'ar nan baki zanyi kuma narasa me za'a girka masu.
Ah lalai wad'anan bakin masu muhinmanci ne.
Shine ko a gayyace ni ko ?
Eh baza a gayyaceki ba me kika iya bayan danna waya.
Tasowa Sa'imah tayi ta nufo Innah tace haba my sweet Innah ki gaya man mana idan baki gaya minba to wa zaki gayama.Hmmm Sa'imah hajiya Fatima ce zatazo kawomin invitation din bikin su, ni wlh banason shige matan manya.
Wacece hajiya Fatima Kuma?Matar sarki garinan mana wacce mukaje gidan maman Anwar muka hadu dasu.
Oh Innah dama matar sarki ce ai na d'auka matan sarki basa fita.
Suna fita mana da farko cewa tayi a d'auko ni, ninace ba inda zani dan banson raini.
Wlh ko gwanda da bakije ba da kinje kallon k'ask'antacciya zasuyi maki.
Aikam gashi da naja girmana zasu biyoni har gida, ke bari ki gani inga abinda Fa'iza ke yi yanzu.Nikam Innah kibari inje gidan aunty Habiba.
Ba yauba kibari sai weekend sai kije yanzu yamma tayi.
Shikenan Innah bari naje gidan su Sarah kafin bakin naki su tafi.
Oh ni Aisha yanzu bakin nawa kike gudu ki tsaya ki gaishe su. No bahaka bane bana son intakura maku ne shiya sa amma bari na zauna , najirasu.
Daya fimaki.
To bari nima nashigo kawai sai muyi tare.A tare suka shiga kitchen din.
Fa'iza me kika fara yine waigowa tayi tace hajiya farar shinkafa na fara d'orawa.
Sa'imah tace ok bari nayi vegetable soup, sai mi hada masu da pepper chicken, ai a kwai sauran kaza a freezer ko?
Eh hajiya k'arama a kwai.
Ok kawai kije zanyi kawai.
Yawwa Innah kibata kud'i taje ta siyo fruit, Wanda muke dashi bazai isa ba.To Fa'iza zo kije Ibrahim ya kaiki kiyi sauri kar ki tsaya.
To hajiya" kud'in ta karba ta fita da sauri a zaune ta sameshi shida mai gadi ta gaya masa aiken da hajiya tayi masu.Innah na falo zaune ta fara jin kamshi yana tashi, hanci ta k'ara budewa dan ta shaka da kyau kasa hakura tayi ta,tashi ta nufi kitchen din .
Kai hajiya Sa'imah irin wanan kamshin haka har kinsa na fara jin yunwa Allah dai yasa ba kamshin banza yakeyiba?Waigowa tayi tace kai Innah ban gane zaiyi dadi ba kina nufin baiyi dadi ba ko mai?
Ni banceba kar kikaini inda yan kuda ka salati.
Dariya Sa'imah tayi tace to Innah kibari har kici sanan ki fara santin.Kinci tuwon gidan ku ni nake santi dan kin rainani........
Assalamu alaikum, sukaji sallamar Sarah.
Sa'imah tace naahiga ukku wanan magana disun yanzu zata zo ta dameni.
Fita Innah tayi tana amsa mata sallamar.
Innah wai sabon kuku kika samune tundaga bakin get nakejin kamshi na tashi. Tana maganar ta nufi kitchen din.
Lah Sa'imah kece kike wanan girkin ?Eh nice da wani abune.
Amma wlh Sa'imah ke muguwa ce dama kin iya irin wanan girkin kika yi mana, a dai_dai Sa'imah tana juye pepper chicken a cikin kula.
Hannu Sarah takai tanacewa bari na taba naji yawuna sai tsinkewa suke.Wlh kina samin hannuki saian dan gwala maki praying pan dinan.
Dasauri ta cire hannunta jin dumin praying pan a hanunta, tace wlh kwdai Sa'imah muguwa ce dan Allah ki bani d'aya na maida yawuna.
Yawun sundad'e basu dalalo ba.
Wai dan Allah wakike yiwa wanan girkin ko dai ya Deedat ne zai zo?Ba Deedat ba Dudeet sai kawai na zauna ina yima kato abinci.........
Shigowar Innah shiyasa tayi shiru bata k'arasa ba.
Wai har yanzu Fa'iza bata dawo ba sun kusa k'arasowa .
Eh haryanzu bata dawo ba nima nagama bari naje nayi wanka kafin ta dawo.....
Bata rufe bakiba saiga Fa'iza ta shigo.
Wai a ina kuka tsaya haka kuka dad'e?
Hajiya wlh bamu samu bakin hanya ba saida mukaje kasuwa.Shikenan Sa'imah yi sauri ki hada sun kusa bari nasa kaya.
To Innah, Sarah dan Allah jeraman kayanan a darning kafin nagama had'a juice d'in.
Dan Allah waye zaizo?
Kai wlh kincika tambaya kamar yar jarida nima bansaniba.
Tsuki tayi tace kada Allah yasa kisani, ta figi kula shinkafa ta nufi darning, tana k'unk'uni.
Sa'imah bata d'auki wani dagon lokaciba ta gama had'a penappel and watermelon juice, sanan ta had'a fruit salad, kanara ta fasa masu gaba d'aya, juice din ta d'auka Fa'iza ta dauko fruit salad din.
A falo sukaga Sarah sai cika take tana batsewa.
Yadai hajiya fushin ne to yi hakuri je ki d'auko mana ki kaimana daki zanzo na miki bayani.
Tashi tayi tanufi kitchen,itakuma Sa'imah ta k'arasa darning, ta ajiye sanan ta gyara gurin da kyau Fa'iza ta dauko sauran abubuwan saida taga komai yayi mata sanan ta bar gurin.
Innah ce ta fito sanye take da doguwar riga ta shadda bata shafa komai ba, amma tayi kyau sosai, kallon Sa'imah tayi dake k'ok'arin shiga d'akin ta, tace hajiya Sa'imah sannu da aiki, yawwa hajiya Innah.Dan Allah a taimakeni da abinci mutun daya idan a kwai yarona ne yazo gaida ni.
Shiru tayi tana tunanin wanene yaron nata.......Kiyi sauri yana bakin get sai ku kai masa keda Sarah ganinan zanzo mu gaisa kafin su k'araso.
Muje zuwa
Don't forget to:
Comment
Vote
Share
FollowIt's Rashma
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...