🌹🌹DEEDAT🌹🌹
Writing by RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page 31
Tunani ta fara yi wanenenya turo mata wanan sak'on, kodai ba ita za a turoma sak'on ba kuskure a kayi?
Babu mai bata amsa.
Kwanciyar ta, tayi tacire tunani message din a ranta.Misalin 1:00am yafito daga d'akin sa, sanye yake da kananu kaya suka bakake da facing cap ta rufe masa rabin fuskar sa handkerchief ya rufe daga hancin sa zuwa bakin sa shima baki ne.
Wata yar k'arama wardrobe ya nufa bud'ewa yayi ya shiga wasu numbobi ya daddana take wata kofa ta bayyana.
Idan ba sani kayiba bazaka taba cewa kofa bane dan kamar bango haka gurin yake bazaka taba cewa a kwai kofa a nan ba.Yana fita k'ofar ta maida kanta ta rufe tafiya ya cigaba da yi saida ya danyi nisa sanan ya cimma wata mota, bud'e wa yayi ya shiga bangaren mai zaman banza.
Kai_kai oga irin wanan shiga haka.
Saif yanzu ba lokacin wanan bans yi sauri mu tafi banason mu rasa wanan damar.
Shikenan oga. Tada motar yayi yafara tafiya sunyi tafiya sosai sanan suka zo wani daji cikin dajin suka dinga kutsawa a cikin dajin tafiya sukeyi babu alamar gari daji ne sosai,wani gida suke hangowa, sun kusa zuwa gidan Deedat yacema Saif ya faka motar.
Parking yayi yace sir kana ganin suna ciki kuwa agogon hanunsa ya kalla yace inada tabbacin suna ciki. Yanzu dai ka jirani a nan bari na k'arasa.To Allah ya bada sa'a .
"Amin" yace sanan ya fita cikin sanda yake tafiya ko fitila bai yarda ya kunna ba duk duhun nan haka yake tafiya har ya kai kofar gida.
Hasken dake cikin gidan shi ya haske maska masa yake ganin tsawon ginin gidan. Gidan ya fara zagaye wa yana neman ta inda zai haura.
Saida yazo bayan gidan inda ya tabbata babu kowa a nan ya kama ginin cike da kwarewa ya fara haurawa duk tsayon ginin nan saida ya haye shi a hankali yafara dirgowa har ya sauka k'asa. Wasu samudawan bodyguard ya gani amma su basu kula dashiba a hankali yake takawa har yazo bakin window din daya gani duk babban gida nan daki d'aya ne ga dukkan alamu anyi shine dan yin taro.
Lekawa yayi baki ya bud'e sanan yana jin jina kai.A cikin d'akin kuwa sha'anin su sukeyi ga naman kaje da na rago ga giya a gefe dayan gefe kuwa yan mata ne wad'an da baza su wuce 18 year's ba kusan su biyar.
A ran Deedat kuwa cewa sukeyi wai wad'anan sune shuwa gabanni mu to tayaya k'asar mu zata gyaru.......
Maganar da sukayi ne ta katse masa tunani.Kafin musa giya ta bugar damu ya kamata muyi abinda ya kawo mu.
Ya cigaba dacewa kunga jiya na tura kauyuka a sato man kananun yara da mata, zan tura su saudiyya matan zasuyi karuwan ci yaran kuwa zasuyi bara.
Eh hakan yayi amma kasan k'ungiya tana bukatar Mata ko Mata sunyi kasa sosai.
Eh a kwai wad'anda zan cire ma k'ungiya.Amma bari zan kira oga MBA nayi masa maganar naji mezai ce dan wanan karon zamuyi sabon d'auka a kungiyar tamu.
To ya maganar shigowa da cocaine din kasan kasan wanan dan iskan yaron yasa mu gaba so yake sai ya bankad'o duk wani sirri namu.
Haka ne amma karka damu zamu dauki mataki a kansa zamu tura sunan sa gurin boss shiya san yanda zaiyi dashi.
Tab kace a kwai shagali kenan tunda sunan zaikai gurin boss ai shikenan.A gogon sa ya kalla yaga har 3:30am tayi juyawa yayi da nufin ya haura ginin ya koma.
Wani matashi ya gani mai kalan kayan security din da ya gani.
Saurayin ya dakatar dashi da cewa zo tanan ka fita idan ba haka ba danye zasu cinye namanka.
To kai waye ba gadinsu kakeyi ba?
Kaidai kayi sauri kazo idan mun fita zan ma bayanin komai da a keyi cikin gidan nan.
Bai yarda da maganar da matashin keyi masa ba yafara k'ok'arin haura ginin.
Na roke da Allah ka tsaya ka taimaki dubban yara da matan da ake halaka masu rayuwa.
Dakata wa yayi yace me kasani?
Kazo mufita kafin su ankara damu kayi sauri dan lokaci kadan ya rage mana.
Ba musu Deedat ya bi bayansa, wata boyayar hanya ya bi dashi sai gashi sun fito waje.
Yace kabani address dinka kokuma ka fad'a man inda zamu hadu zanzo na gayama duk wani sirrin kungiyar nan, bazai yu na gayama yanzu ba sbd sunkusa ne manmu Kuma lbr da tsawo idan suka kula bana nan za su fito nemana Kuma idan suka ganmu tare zasu kashe mu ga number ta ka turo man inda zamu hadu kar ka kirani domin idan aka kiramu sunajin duk abunda zamuyi magana a kai.
Bai bari Deedat yayi magana ba ya juya ya koma inda ya fito.
Shima Deedat gurin da motar su take ya nufa koda ya je Saif yanata kwasar baccinsa.
Kwankwasa masa yayi firgigit ya farka bude masa yayi, yashiga ya zauna sanan yace yi sauri ka tada motar mutafi sun kusa fitowa da wani irin mugun gudu Saif yaja sukabar gurin.
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...