page 43

1.9K 132 0
                                    

🌹🌹 DEEDAT🌹🌹

Writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah))🤜🤛

PAGE 43

Lokacin da nazo na gaya maki zamuje farauta......

An kira nine akan an kaima wani ƙauye dake kusa da Asokoro, ana ce masa kasuwar dare.

Koda mukaje an karkashe wasu sai mata ukku masu ciki da akayi ma kisan gilla, ɗayar ta ƙasan ta akasan ta suka janyo abinda ke cikin ta, sai ɗayar ita kuma yan kata sukayi daga saman ta har ƙasan ta, sai ɗayar ita kuma cikin suka farka suka cire abinda ke ciki da wasu sassan jinkin ta.
Duka matanan ba wacce aka bari da abinda ke cikin ta saida suka cire suka tafi da shi, mazan kuwa an kashe wasu, wasunsu kuwa sun tafi dasu, amma basu tafi da yara ba, mata ma sun tafi da wasu.

Mun samu nasarar kashe wasu, mun kama wasu, sauran kuma sun gudu.

Ya ƙarasa basu labari yana hawaye, Ammah da papa ma hawaye sukeyi.
Papa yace wai har yaushe za a daina  irin wanan kashe_kashen a ƙasar nan?

Deedat yace papa ko dan matan nan da aka yi masu irin wanan kisan sai na ɗauki mumunan mataki akan duk wanda yake da hannu akan wanan al'amari.

Ammah ta share hawaye sanan tace "my son ina bayan ka Allah ya baka sa'a akan duk wani aikin alkhairi da kasa gaba."
Amin Ammah, Deedat ya amsa.

Papa ya kalla sanan yace ya jikin Jiddah?

Numfashi ya sauke sanan yace da sauƙi za'ace, amma har yanzu bata iya magana, ɗazu ma munyi shawara da maman ku akan adawo da ita gida amata na gargajiya kawai.

Nisawa yayi sanan yace bari zu anjima sai naje nadubo ta.

Ammah tace Allah ya kaimu mukam tunda ɗiyata tasa ɓacin ran naka ya sauka yanzu za muje.

Murmushi yayi sanan yace to bari kawai na shirya mu tafi tare ya fimin intafi nikaɗai.

To kayi sauri dan nasan shirin ka sai an ɗauki lokaci.

Kai amma kin cika ƙorafi kamar gwaggo.

Kamace ita ɗince ai yanzu da kamin laifi ita kaɗai zan kira tamin maganinka.

Dan Allah ki rufa min asiri ina zan iya da masifar gwaggo.

Papa yace wai ya zakazo kana zagar mana uwa zanfa saɓa maka.
Tab papa indai gwaggo ce bakayi komai ba yanzu zata watsa ma ƙasa a idanu.

Daga haka ya shige bedroom ɗinsa domin ya canza kaya, Ammah da papa kuma part ɗin suka nufa do min shiri.

Yariga su fitowa sanye yake da ƙanan kaya sun masa kyau sosai, tsaye yayi yana ma yaran sa magana daga ni umarni yake basu.
Saiga Ammah da papa sun jero suna tafe suna ƴar fira, gurinsu ya nufa yana zuwa kusa dasu ya tsaya, yace kai amma fa kunyi kyau kamar na sace ku na gudu.

Duka Ammah ta naɗa masa abaya, da sauri ya sosa yana kwaɓe fuska haba  Ammah da zafi fa, kuma ma wai yaushe zaki daina dukana nafa girma.

Au haba ni kam ban ga girman ba tun da baka haihu ba.

Ahaka suka shiga mota shi ya ja su yaransa na hindu abaya har suka kai asibiti, koda suka shiga ɗakin da aka kwantar da Jiddah, momy tana ta fama da ita akan taci abin ci ita kuma taƙi ci.

Deedat na ganin yan da ta koma saida yaji wani iri, da mamkin wai Jiddah da yasani ce ta koma haka, Jiddar da yasani ƴar gayu mai kwalliya da ƙamshi da jida kai,  wai itace ta koma haka kamar mai cutar ƙanjamau, duk hallitar ta ta canja, karon farko da yaji yana jin tausayin ta.

DEEDATWhere stories live. Discover now