🌹🌹 DEEDAT🌹🌹
Writing by RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarraka
🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛Page 32
No jamcy bazan iya yimata maganar ba inajin kunyarta wlh ke koke bazaki iya yimata magana gatsau ba duk kuwa rashin kunyarki.
Mtswww kindai ji haushi wlh.
Naji nidai muyi magana akan yar iskar yarinyar nan da akace man angansu tare.
To me kikeso ayi Mata yanzu?
Ni kawai kisa mutanen ki suyi mata gargadi ta fita harkar Deedat.
Shikenan zansa a sato maki ita a kawota har nan Abuja sai kiyi yanda kika so da ita.
Shikenan nagode aunty jamcy. Babu abin korawa a gidanan?
A kwai mana je ki dauko ni bak'o ma zanyi inaga Kuma gidanan zai kwana.
To kisha shagalinki ni yanzu wlh inajin kishirwar Deedat amma ni nasan ko karen mahaukata ya cije ni bazan tun kare shi da wanan maganar ba.
Dariya jamcy tayi tace wlh bake kadai ba nima mugun tsoronsa nakeyi.
Dairaya Jiddah tayi tace wlh ko mamar shi haka take da kwarjini dan dai baki santa bane shiyasa kike cewa na tun kareta da magana.*********
Mamy dan Allah ki fahimce ni wlh babu wanda yayi man komai kawai dai a kwai aikin da yataso man ne shiyasa nakeson nagoma wancan gidan.
Haba Deedat taya zakace haka banyi tunani wani abuba.
Tasowa yayi ya dawo kusa da ita yace haba mamy wlh babu wanda yayi man komai banason a taba man lfy ku ne shiyasa zanyi nisa daku dan Allah ki fahimce ni.
Shikenan Allah ya bada sa'a. Amin my mamy insha Allah zan rika zuwa kullum muna gaisawa.Daga haka ya bar falon part dinsa ya nufa a falon sa ya samu Saif yace yawwa Saif ka tatara komai?
Eh na hada komai.
Ok Kira su Sagir su fita da kayan.
Kiransu Saif yayi suka fita da kayan gaba d'aya ba abar ko tsinke ba Wanda ya kasance na Deedat ne.Blue eyes angama kwashewa.
Wata uwar jarara ya banka masa yace badai bazaka daina ceman hakan ba ko?Murmushi Saif yayi yace inako zandaina wai ko kasan Ilham tanata damuna a kan na had'a ta da kai?
Mtswww yaja tsaki yace wacece Kuma Ilham?
Yar gwamna kaduna mana kardai kace man baka santaba.
Kusan haka gaskiya ni kama tunamin ban kira hajiyata ba naji ko tana lfy.
Jakar laptop dinsa ya d'auka yace muje idan naje can na kirata .Fita sukayi saida yaje yayima mamy sallama sanan ya dawo bud'e masa baya sukayi ya shiga sukabar gidan wata ajiyar zuciya ya sauke.Sir wane gidan zamuje?
Muje na G.R.A zaifiman.
Ok sir.*********
A gidan Habiba suka wuni sai gurin 5 suka dawo.
Sarah tace bari naje gida wlh duk a gajiye nake.
Sa'imah tace aikin me kika gaji ?
Hmm bazaki gane bane nidai bari naje.
Shikenan anjima mu hadu a chart, ranar nan kin fara bani lbr baki k'arasa ba kika bari.Kinma tunamin zanhau idan nayi wanka na huta sai nabaki lbr yanda mukayi dashi.
Daga haka ta fita ita kuma Sa'imah ta k'arasa gida.
Sa'imah tadan jima a cikin motar sanan ta fito hanayenta rike da jakarta ta rataya lab coat.
Da yar wakarta ta shiga babban falo Innah tasamu zaune ga tv kunne amma ba kallon takeyi ba ta dai dasashi gaba ita kuma ta banka tagumi.Dafata Sa'imah tayi firgigit ta dawo hayacinta nanauyar ajiyar zuciya ta sauke ganin Sa'imah ce.
Lfy dai Innah kika zauna kina tunani haka tun d'azu nake ta sallama amma bakiji ba.
Hmmmm yar nan gida nake tunani inason ganin yan uwana.
Innah bakince ba'a san inda sauran yan uwan naki suke ba?Eh to amma a kwai wata gwaggo na wacce tasan inda suke inaga kawai shiryawa zanyi naje inda take sai ta fad'a man inda suke.
To wai Innah meya faru ne kuka tar watse haka?
Lbr ne mai tsawo yanzu dai kitashi ki je ki huta idan na samu lokaci zan baki lbr asalinmu har na baffan ki duk zan gaya maki.
To Innah bari naje na watsa ruwa amma dan Allah kidaina wanan tunani.
To na daina.*************
Address din gidan sa ya turama number din da matashin yabashi.
Baifi 30 minutes da tura wa wayarsa tayi k'ara alamar shigowar sak'o kanar bazai duba ba sai Kuma ya duba number ce.
Dubawa yayi yaga ansa "gani k'ofar gidan"
Wani abu ya danna saiga wani soja ya shigo, Deedat yace kaje k'ofar gida zaka ga bak'o ka shigo man dashi.
Ok sir.Bai jima da fita ba sai gashi sunshigo da wanan matashin.
Tsaye Deedat ya tashi ya bashi hannu suka gaisa sanan ya nuna masa gurin zama gaisawa suka karayin.
Deedat yace amma koda na tura ma kana kusa?
Eh ranka ya dad'e ina kusa shiyasa kawai nace bara na k'araso.
Yayi kyau inajin ka me kakeson gaya man ne?Gyara zama yayi yace da farko dai ni sunana Anas ni d'an yola ne a wata ruga dake gefen gari. Family muna cikin farin ciki da kwanciyar hankali gaba d'aya rugar tamu ana cikin farin ciki da kwan ciyar hankali kwatsam, Wata rana da bazan taba mantawa ba a rayuwata.
Naje kiwo naji ihun mace tana neman temaka, hankali na ya tashi kwarai da gaske.Da k'yar na taimaka mata na kaita gidan mu sbd naga mawuyacin halin da take ciki gata da tsohon ciki.
A she hahuwa zatayi bata d'auki wani dogon lokaci ba ta haifi yar ta danta kyakyawa bata jima da haihuwa ba Allah ya amshi ranta naji mutuwar baiwar Allah nan.
Gashi ban samu na tambayeta lbe ta ba.
Munan muna jimamin mutuwar ta sai jin haniya mukayi dabobi sunata kuka alamr a kwai tashin hankali.
Lekawa nayi naga wani alhaji yana nufo bukkarmu take hantar cikina ta kada ganin hannu sa rike da makami ,da sauri na shige cikin kayanmu ina kallon su suka kashe man yan uwana da mahaifiyata da ita kad'ai ta rage man babu halin nafito ga yaron hanuna ya fara mutsu_mutsu yanason yin kuka haka Allah ya taimakemu koda nafito gari yayi tsit alamar bakowa a cikin sa duk sun gudu wasu Kuma an kashesu.........Tsaya wa yayi ya share hawayensa yaja majina sanan ya cigaba da cewa.
Haka na fito ina ta tsallake gawawaki har nasamu na fita bakin titi jikina duk jini dak'yar nasamu wani bawan Allah ya taimakemu ya shiga damu cikin garin yola.
Haka ya tafi damu gidan matar sa mai mutunci haka ta karbi yaron hanuna ta masa wanka tanada goyo sai ta zabo mana kayan yaronta ta bamu ta dama masa madara ta bashi ta ke bacci ya yi ba dashi.
Nima wanka nayi babban yaron gidan da bazai wace sa'a na ba yabani kayansa nasaka a d'akin sa na kwana.
Washe gari saida muka karya sanan na basu lbr abunda ya faru damu, sun tausaya mana sosai sanan yaron gidan da ake cema Bilal yace ma babansa dan Allah ya barmu muzauna da su.
Baban su bai wani jaba yabamu gurin zama.
Hankalina ya kwanta ga jariri na da nazamar masa uwa da uba Wanda Alhaji ne ya yanka masa rago yatamayeni wani suna zan saka masa.
A kwai wani soja da nake jin sunan sa sunan Kuma yana burgeni wato Ahmad Deedat.
Saidkawai nasama yaron sunan.Murmushi Deedat yayi yace ah kace ta kwarana ne.
Shima murmushi yayi yace hakane kam.
Yaron yanada shekara d'aya a duniya nikuma har nafara zuwa makaranta.
Wata rana mama ta aikeni bakin titi siyen kati kwatsam Wata mota ta faka gabana budewa akayi ban ankara ba sai kawai najini cikin motar.
Mutane salati kawai sukeyi. Wani tanfatsetsen gida aka kaini muna shiga hoton alhajin da ya kashe man mahaifiya naci karo da shi bin hoton nayi da kallo jana suka rika yi harsaida aka kaini wani d'aki matasa ne daya wa aciki mafi yawa bazasu wuce sa'aninaba, haka suma ingiza kiyata cikin su.Bamu jiba saiga wad'an da suka satoni sunshigo wai muzo Alhaji yanason ganin mu.
Fitar damu akayi zauane muka sameshi akan kujera hakimce.Kallonmu yayi d'aya bayan d'aya.
Nikuma babu abinda nake masa sai kallon tsana ji nakeyi kamar na kasheshi na huta amma babu hali.
Sbd dan zamana da nayi gidan Alhaji na fahimci cewa wanan babban mutum ne dan ana yawan nunashi a tv.Haka aka kwashemu aka maida mu ban sa me suke kullawa ba, kawai washe gari naga an fitar damu an fara bamu training bansan ko na meye ba.
Muje zuwa
Don't forget to:
Comment
Share
Vote
FollowIt's Rashma
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...