🌹🌹 DEEDAT🌹🌹
Writing by RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah))🤜🤛Wanan shafin nakine my Balkisu 🅱️K kiyi yanda kikaso da shi{my Bulkiso🤪🤪🤪}.
My momy Maryam Z.A.W Allah ya baki lafiya yasa kaffara ne i miss You so much😭😭😭😭😭😭😭😭
BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page 35
Mota Saif ya buɗe masu suka shiga ya maida ya rufe.
"Kai idan baka tashi ba zamu tafiyar mu."
Kutafi ina?
"Cewar Deedat da yake tun karo su"
Yaro babu inda zakaje.
Kama isa ai wallahi ƙafata ƙafarka."Kaikam ka shiga tara.
Waini sa'an ka ne da ko ina zanje sai kabini?
Eh mana nidai muke kana ɓata man lokaci.
"Makullin ya miƙa masa yace to gashi kayi driving.Bayan motar ya buɗe yace ma Sarah " ke fito ki koma gaba dan nasan danke ya maƙale sai ya bimu"
Sum_sum ta fito. "Saif yayi saurin buɗe mata gaba ta zauna.
Deedat yace munafuka ai ina kallon ki, kina kallon sa ta ƙasan ido.Saif yace to kai me zai kaika baya?
ka dawo gaban kawai ka zauna.
"Wata uwar harara ya banka masa, baiyi magana ba ya shiga ya zauna.Shima Saif shiga ya ja suka bar gidan.
Sun ɗanyi nisa da tafiya. " Deedat yace kar ku gayama su mama abinda ya faru ɗazu."Sa'imah tace saboda me zakace kar mu gaya masu?
Sanan kuma me zance mata idan ta tambayi mota na?
Kai ya dafe sanan yace anya ba ƴar jarida zaki koma ba wanan tambayoyi haka. " Baki ta turo"
Bata an kara ba taji ɓal a bakinta da sauri ta saka hannu ta rufe baki.Ai na gaya maki indai kinka ƙara turo mani baki sai nayi maganinsa.
Ƙasa_ƙasa tafara magana "mugu kawai sai Allah ya saka mani haka kawai"
Ganin bakinta yana motsi shi ya nuna masa alamar magana takeyi.
"Magana kikeyi?"
Da sauri ta girgiza kai.
Aiho na ɗauka magana kike yi.Firar soyayya kuke yine muke jin magana ƙasa_ƙasa?
"Cewar Saif"
A 'a ta ƙiyayya mukeyi ina ma ruwanka da maganar da mukeyi?
Allah yanzu zaka fita daga motar nan.
Sarah tace cab........."Deedat yace magana kikeyi ne?"
Girgiza kai tayi tace a'a banyi magana ba.
Aiho nasha kinyi magana ne.
Kallon sa ya maida kan Sa'imah yace karfa ki gaya mata abunda ya faru kinsa hankalin ta tashi zai yi.
Sanan kuma motar ki ni zan gaya mata tana wajena tasamu matsala ne za'a kaita gyara.To Nagode da ƙoƙarin da kakeyi a kaina bansan da wace kalma zan gode maka ba.......
Bata ƙarasa ba ya katse ta da cewa bashi fa na baki kuma zaki biya banason godiya.
Uhmmm ni me nake dashi da zan biyaka bashin?
Ƙasa_ƙasa ya ƙara yi da murya yace keko kike da abin biya.
Allah dai ya kaimu lokacin biya yayi zaki gani." To Allah ya kaimu lokacin"
Amin yace."Haka suka ci gaba da fira har suka kawo ƙofar gidan su Sa'imah.
A ƙofar gida Saif yayi parking."Deedat yace oya ku fita ku bamu guri muyi sallama" Sarah ce ta fara fita sanan Saif yabi bayan ta, dan bai tsaya tanka masa ba.
Sun ɗan jima a cikin motar duk da ba wata firar kirki sukeyiba.
Ganin motar Innah ta shigo layin shi yasa Sa'imah fitowa daga motar shima fitowa yayi suna jiran ƙarasowar ta.
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...