page 38

1.8K 116 0
                                    

🌹🌹 DEEDAT🌹🌹

Writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah))🤜🤛

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

PAGE 38

Tundaga lokacin na ɗauki ɗamarar gamawa da duk wani makusan cin Alhaji Mubarak.

Kallon Jiddah tayi da zufa da fitsari suka gama jiƙata.

Wata mahaukaciyar dariya tayi, tafar kusan to Jiddah ita kuma sai matsawa baya takeyi saida takai da bango ta tasaya, roƙon ta tafara yi.

"Dan Allah kiyi hakuri  kiyiman rai wallahi ni bansan komai ba"
"Baki yiman komai ba amma mahaifin ki yayi mani."

Matsowa tayi dab da Jiddah, wata razananniyar ƙara tasaki take ta faɗi sumammayi.

*********

To maman Sa'imah ki karɓa kawai tunda shi yabaki ba kuma roƙon sa kikayi meye naki na ƙin karɓa, tunda har suka gaya maki dalili.

Sarah ta gayamin duk abunda yake faruwa, shiyasa nace ki karɓa kodan ƴar ki tasamu tsaro.

Nisawa tayi sanan tace "to zan karɓa amma wallahi har ga Allah banason tashi daga kusa daku."

Murmushi mamy tayi tace "kijiki da wata magana ai dai muna gari ɗaya zamu dinga zuwa ai."

"To shikenan maman Sarah gobe sai muje muga gidan."

"To Allah ya kaimu goben."

"Yawwa maman Sarah kintuna wacce ta shigo damu garin nan?"

Eh na tunata  marar mutunci ɗinan.

Murmushi Innah tayi tace "aikuwa kintuna ta, to itace tazo ta kawo gwaggo na."

Oh natuna mun haɗu dasu a unguwar su  aunty Hajara shine ta matsa mani inda kike har ta nunamin wata mata tace ita take neman ki shine nabasu address.

"Ai kuwa dai sunzo ɗazu sunama  nan yanzu haka."

"Ok bari nayi sallah sai nazo mu gaisa da gwaggon taki."
To sai kin shigo, bari intafi na barsu su kaɗai.

To kigaida su kafin nazo.
" To zangaya masu" daga haka ta fita.

Koda ta shiga gidan a falo ta samesu har Sa'imah suna kallo.

Assalamu alaikum.

Wa, alaikumussalam, Innah har kin dawo?
"Eh na dawo ƴan matana , ya ake ciki ya makarantar?"
Lafiya lau alhamdulillah.
" Masha Allah my doctor." Dariya Sa'imah ta yi tace kai Innah harda tsokana haka.

Juyawa Innda tayi ta kalli gwaggo Halima, tace gwaggo kizo Sa'imah tayi maki allura.

"Cab allu me?" Innah tace allura.

Tab ai wallahi idan kin ganni lahira kaini akayi.
Haba gwaggo karfa kizo kina roƙonmu.

Dan Allah ki bari maza su kaini ba mata ba.
Gwaggo ai dama mazane zasu kaiki kawai ki bari ayi maki guda ɗaya.

Ni kam Indo yaushe na fara wasa dake bansaniba?

Sa'imah tace kawai ki bari nayi maki babu wani muzurai da zakiyi daga gani baki son allura.

Mur gwaggo tasha tace ungo naki nan mai kai kamar ƙwallon mangoro.

Kai_ kai gwaggo kaina fa yafi naki kyau.

DEEDATWhere stories live. Discover now