page 39

1.8K 107 1
                                    

🌹🌹DEEDAT🌹🌹

Writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah))🤜🤛

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

PAGE 39

oga ka tsaya ka sauraren i............
Indai matsalar yarinyar kace wanan kai kajawa kanka, nidai nagayama ka bar ƙasar nan kafin komai ya lalace.

Daga haka ya yanke wayar, wayar ya bi da kallo sanan ya sauke numfashi kansa ya ɗora kan sitiyari yana tunani abubuwan dake faruwa da shi a cikin  ƴan kwanakin nan, ga Jiddah da ya ɗora duk wani buri nasa akai gata kuma abinda yasameta, numfashi ya sauke sanan ya yima motar key sai gida yana shiga ɗakinsa ya nufi gurin da yake ajiye biza, ɗauka yayi ya fito ya shiga motar sa da mugun gudu ya bar gidan  bai tsaya ko ina ba sai airport batare da yayi tunani zuwa gurin su Jiddah ba a ganin sa yanzu  batada amfani tunda bata iya komai, cikin awoyin da basu wuce ukku ba jirgin ya ɗaga sai Brazil.


Yau kwana biyu kenan da kwanciyar Jiddah a asibiti, tun momy nasa ran dawowar mai gidan nata, gashi duk ta kira wayar sa aka she ake cemata, hawaye masu zafi take sharewa, kallon Jiddah tayi da duk ta juye bakin ta yana ta dalalin yawu, wasu hawayen tasake share wa na tausayin ƴar tata.

Shafa kanta tayi tace "my  Jiddah kiyi hakuri jarabawa ce daga Allah, Allah yasa kicinye wanan jarabawar"

Kawar da kai Jiddah tayi hawaye masu zafi suna zobo mata, tanaso tayi magana amma ba hali, sosai takejin ciwo a rayuwar ta,  dana sani takeyi marar iyaka tasan dai ko ba'a faɗa mata ba tasan Dady ya gudu ya barta tunda yaga batada amfani.

*********

Wai Ammah nayi missing ɗinki.

Ba wani missing ɗina da kakeyi bayan ka koma Kano kayi zaman ka.

Murmushi yayi yana matsowa kusa da ita yace haba my Ammah kiyi hakuri aiki ne ya tsayar dani.

Ya kabaro mutanen can, koda yake sister tace mani kabar gidan yanzu.
Kansa ya shafa yace eh hakane Ammah yanzu ba 'a gidan nake ba yanzu.

Kuma nasan kana da dalili.
Uhmmmmm.

Bawai uhmmmm zakace mani ba dalili zaka gaya mani.

Kawai Ammah mu bar maganar.

To naji ɗazu Hajiya Nafisa ta kira ni wai Jiddah batada lafiya tana asibiti kuma baban Jiddah ya gudu ita yanzu bata ma san yana wace ƙasar ba.

To Allah ya kyauta ya kuma bata lafiya.

Amin thumma amin, sai ka shirya anjima idan anyi la'asar sai muje mudubo ta.

Gaskiya Ammah inada aikin yi wasani ma ko shaye_shayen ta taje tayi ya..............

Murtuƙe fuska mamy tayi tace "dakata malam idan bazaka ba shikenan amma bawai kata zaginta ba, ciwo Allah ya ɗora mata ba ita ta ɗorama kanta ba."

Ganin ranta ya ɓaci yasa shi cewa "wasa fa nakeyi my Ammah ni na isa nace bazanje na dubo sister na ba."

Da dai ya fima.
Ammah to ina baban Jiddah ya tafi ne?

Allah masani babu wanda yasan inda ya tafi.

To Allah ya kyauta, bari inje Saif yana jira na fita zamuyi .

To adawo lfy.

Yana fitowa motar da aka buɗe masa yashiga, suna ƙoƙarin fita motocin papa na shigowa, alama yayi musu da su dakata.

DEEDATWhere stories live. Discover now