page 25

1.8K 119 0
                                    

🌹🌹 DEEDAT🌹🌹
Writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

BISIMILLAHIR_RAHAMNIR_RAHIM

page 25

Mr Bashir bai fitaba sai 1  pm sanan yafita, Sarah dan Allah muje naci abinci kafin wani ya shigo, gashi lokacin sallah yayi.

Maman Afnan ce ta bata amsa da cewa ai yanzu sai 2 za'a shigo mana.

Alhamdulillah itama kanta k'wakwalwa zata huta, kutashi muje muba ciki hakkin sa.

Yanzu ansamu sabuwar k'awa anmata Dani ko"cewar M Sani"

Bahaka bane bestee kasan idan ina jin yuwa bana tuna kowa.

Au ashe fa haka ne ashe har yanzu baki canza ba.

Inafa zan canza kasan bana wasa da d'a'amu, to muje nima yunwa nakeji.
Tare suka jera suna tafe suna fira, Sa'imah tana rike da Afnan , wlh maman Afnan kinga su, subiyu nan  idan karatu yayi nisa gaba daya class dinan yan kallo zamu koma.

Kai Sarah akwai sharri nida nake daukar na karshe inah kokari yake anan, haka suka ta musu da juna, maman Afnan tana saka masu baki kadan _kadan a afirar tasu, ba k'aramin burge ta sukeyi ba, kan atashi makaranta har sun yi sabo kamar sunyi shekara.

Basu bar makaranta ba sai gurin 5pm sanan suka fito ko wanne su agajiye yake, Sarah uwar surutu, baki ya mutu akan gajiya, jingina wa tayi da kuran mota ta lumshe idanu, Sa'imah kuwa driving takeyi, motar tayi tsit babu abinda ke tashi sai karatun Qur'ani, rage volume Sa'imah tayi tace Sarah ashe da gaske kike yi da kika ce ana binmu.

Bude idanu tayi da suka fara ja, hmmm ba nagaya maki ba kika maida abun wasa.

Mtsww taja tsaki sanan tace su suka sani, zasu gaji da bin namu subari.

Daga nan suru sukayi har suka kai gida abakin get din gidansu Sarah ta sauke ta sanan ta nufi gida, horn tayi da sauri baba maigadi yabude mata, sannu da zuwa hajiya k'arama, yawwa baba ina wuni?

Lafiya lau andawo lfy ya makaranta,da lfy kawai ta amsa tashiga ciki tayi parking, sanan tanufi babban falon su, da sallama tashiga babu kwa sai tv dake kunne bata nemi Innah ba, tashiga dakinta saida tayi wanka ta saka kaya marar nauyi sanan tafito falon, yanzu kam Innah tana zaune, sannu da gida Innah, juyowa tayi tace ke wagga aljannaru yaushe kika dawo?

Murmushi Sa'imah tayi tace Innah nice aljannaru?

Eh mana banga shigowar kiba saidai kawai naga kin fito.

Zama tayi kusa da Innah tanacewa wash wlh nagaji da yawa.

Sannu raguwa, Innah babu abinci ne wlh wata mahaukaciyar yunwa nakeji jima nake tafara tsinke man hanji.

Kekam kin bani da ci mijinki yaga takansa watakilama duk sati zai rika siyo buhun shinkafa.

Kai Innah sati fa haba saikace wata randa.

Bari intashi inje gurin maman Aliyu, ina shago  ta kirani tace man motana ta iso, dole insanu driver da mai aiki tunda yanzu kin fara zuwa makaranta, babu Wanda zaiyi aiki, gashi nima kwanan inada aiki sosai.

Saida Sa'imah tabari takai aya sanan tace hakan yayi Innah, amma dan wlh Innah idan ankawo motar nan muyi musanya.

To uwata bari nabaki gaba d'aya ki hada ki rike nikum sai in dinga hawa adai _daita.

Haba my Innah batakai canba, amma jeki ki dubo motar idan tayi man sai muyi musanya,lalai yarinya bakida kai, daga haka ta fice ita kuma Sa'imah ta nufi kitchen.

********

Dan Allah yaya kasaka baki yaron nan yasakar mana kaya.

Wai Mubarak meye tsaka ninka da Deedat da zai rike maka kaya sanan wane kaya ne wad'anda bansan da shigowar suba?

Yaya kasan Ni d'an kasuwa ne to nayi order ne daga waje ya rike min kaya, Shiba custom ba yana matsayin soja amma yana shiga hurumin da ba nasaba.

Hmmm Mubarak kenan aishi Deedat ba ruwansa da wanan tunda kaga ya rike su, to barima kawai na kirashi tunda kamar yana gida.........

Bai karasaba  yayi saurin ce a a yaya basai ka kirasaba sauri nakeyi kadai yimasa magana ya daina shiga sabga ta.

Aida kabari ankira shi muji dalilin sa dan bana son rigima ta rika shiga tsakaninku..........

Assalamu Alaikum, sukaji sallamar Deedat, papa ne ya amsa masa ya k'ara dacewa kamar kasan neman ka mukeyi.

Saida ya gaida papa sanan yace tasamu ne ake nemana haka?

Bakaga babanka ba halan da bazaka gaida shiba?

Lah banma ganshi ba oga MBA Inah wuni, da murmushi mugunta kwance a fuskarsa ganin yanda duk kanin mahaifinsa duk ya rude, lafiy kawai Mubarak yace shima duk a rude yake "a ranshi kuwa cewa yake a inah wanan yaron yasan sunan nidai nasan idan ba k'ungiyar mu ba babu wanda yasan wanan sunan"

Dafashi da akayi ne shiya dawo dashi daga duniyar tunani, wai hankali ka yana inah anata magana bakaji ba?

Hmm yaya inah tunanin wani a abune , bari inje yaya sai naske zuwa....

Katseshi papa yayi yace ina kuma zakaje bayan magana mukeyi zauna mu karasa tunda gayanan yazo sai ya gaya mana meye dalilin sa na na kama maku kaya da yayi.

Ah papa dama maganar kayansa ta kawo shi?

Eh meyasa ka kama masa kaya alhalin kai ba jami'in custome bane?

Bai bawa papa amsar tambayar sa ba ya maida  kallon sa ga uncle din nasa yace Oga MBA wanne daga cikin kayanka kake magana kasan nakama kashi _kashi kusan guda 10 to wanne kake magana akai?

Shiru yayi ba amsa, idan ka manta in lissafo ma su ne?

Bai tsaya magana ba yabar falon yana tafe yana tsinewa Deedat da mahaifinsa, tabas idan ban halaka yaya da wanan yaron ba zasu hana man rawar gaban hantsi.....

Jiyayi ance uncle kafita idona in rufe kar kasake sako mahaifina acikin wanan al'amari domin kasanni akan family na zan iya komai kaci sa'a kana amsa sunan uncle dina da yanzu nasaka bin diga na tashi kanka.

Daga haka bai bari ya kara wata magana ba ya wuce part din Ammah.

**********

Yau takama Saturday su Sa'imah basuda lecture, shiyasa tasha baccin ta sai sha biyun rana sanan ta, tashi saida tayi wanka sanan ta fito Innah tagani zaune ,kusa da ita ta zauna sanan tace ah Innah baki fita ba kenan?

Eh ban fita ba zanje unguwa ne, sanan inah jiran maman Aliyu ne tace yau za' akawo mai aikin da nayi magana.

Ok har ansamu kenan to driver da kikace fa?

Har shima an samu yana ma waje an riga da an samu yau zai fara aikin sa.

Allah ya taimaka, amin Innah tace, ki tashi ki karya ki shirya sai ki rakani .

Wai Innah wace unguwa zakije ne?

To yar jarida idan bazaki je ba shikenan sai intafiya ta basai kin tsareni da tambaya ba.

A a my Innah zanje bari ma kigani inshirya sanan na karya dama nayi wanka , sanan nazo na karya dan san zaki iya canza ra'ayi.

Tana shiga tajiyo haniyar Sarah tana zuba sanan kuma tanaji bakin muryoyi sauri ta dinga yi dan tasan halin Innah zata iya tafiyar ta kuma ta riga ta saka Mata rai, bata wani dauki lokaci ba ta fito ........

Muje zuwa

Don't forget to comment
And vote
Follow

It's Rashma

DEEDATWhere stories live. Discover now