🌹🌹 DEEDAT🌹🌹
Writing by RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah))🤜🤛BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
PAGE 50
Sallama sukayi Mairo ta amsa masu daga ciki sanan ta fito tana cewa "kwaɗɗo mingaɗi?" (baƙi mukayi ne)
Murmushi Innah tayi tace" jam wali minta wi'on jam?" (Ina kwana mun sameku lafiya)
Jam felam.(lafiya lau)
Amma mihitaimah (amma ban gane kiba.)Murmushi Innah tayi tace "mihinnon Innah wuro.(nice Innah wuro)
A'a Innah wuro ahan wanni? (A'a Innah wuro kece haka)
Ta fara zagaye ta tana taɓa kayan jikin ta.Sanan ta shiga ɗaki ta ɗauko tabarma ta shin fiɗa tace Innah wuro joɗa (ku zauna)
Accu ɗun yaha ɗun nadowa Baffa Aminu. (Bari na aika a kira Baffa Aminu).
Bata tsaya jiran abinda Innah zata ce ba ta fita bata jima ba sai gata ta dawo, ɗaki ta shiga ta ɗauko masu abinci da fura da nono.Ita dai Innah duk mamakin abinda mairo ke masu takeyi, mutanen da ko ruwan gidan su babu mai sha wai yau itace aka tarama wanan abubuwa haka...........
Shigowa Baffa Aminu ya katse mata tunani, tana ganinsa gaba ɗaya jikin ta ya ƙara yin sanyi kai da gani kasan yana cikin wahala, idanun ta suka cika da hawaye sai ta tuna Baffan Sa'imah......
I meen ɗon moiwan non darta'am? (Gani wa yake nemana?)
Mairo tace " daro mana ahi taimo?" (Duba ka gani mana baka gane ta ba)
Kallon sa ya maida ga Innah ya kafe ta da kallo sanan yace "moinon muitaimo"(wacece ban gane ta ba) mairo tace To Innah wuro ce.
Jagwab ya zauna a inda yake tsaye sai hawaye yace ikon Allah kenan yanzu Innah wuro kece kika koma haka?
Dan Allah ku yafe Mani abubuwan da nayi maku marasa kyau wallahi tunda kuka sa ƙafa kuka bar garin nan ban sake samun kwanuka hankali ba kullum sainayi mafarki da ɗan uwana yana kuka yana ce mani na wulaƙanta masa iyali a she bazan iya kula masa daku ba, kullum cikin damuwa muke.
Gwaggo ta taɓe baki sanan tace wanan zancen ƙarya ne ko ka manta me ka gaya min ne?
Soke kai yayi ƙasa a ransa kuwa ba abinda yakeyi Allah_Allah yakeyi kar gwaggo ta faɗi abinda zai ɓata shi a gurin Innah.
Ɗagowa yayi gwaggo ta antaya masa harara ya ƙara soke kai ƙasa.
Innah tace ai ba komai duk abinda ya faru da
Yawuce Allah ya yafe mana.Washe baki yayi yana cewa nagode sosai inah ƴata Sa'imah?
Nuna masa Sa'imah tayi da duk ta takure guri ɗaya Fa'iza na kusa da ita.
Masha Allah Sa'imah Baffa an girma, zo ƴata.
Tashi tayi taje kusa dashi kamar da gaske duƙawa tayi a gaban sa tabama su Innah baya ba abinda takeyi sai antaya masa harara, sanan tace kar kayi tunanin na manta da duk abinda kayi mani yanan a raina kuma ɗaya bayan ɗaya sai na rama sanan nasan duk abinda ka faɗa ba gaskiya bane ko dai dan kaga bamu wulaƙanta ba kamar yanda kaso kaga kuɗi ko kuma dan ganin jami'an tsaro ne yasaka yi mana ladabi. Bayan shi babu maha lukin da yaji maganar da tayi masa.
Yawu ya haɗiye dan maganar gaskiya da aka gaya masa sunzo yazo yayi masu rashin mutunci kwando_kwando amma yana zuwa ƙofar gida yaga sojoji da bindigogin su yasa shi kama kansa.
Innah tace Sa'imah zo ki kaima su Sagir ruwa a waje.
Miƙewa tayi tace Fa'iza tashi mutafi daga nan sai mu zaga gari.
***********
Gidan da Saif ya ɗauko Mubarak ya nufa yana faka motar ya fito ya nufi gurin mai gadi yace masa baba akwai wanda yazo nan?
Eh Saifullahi yazo yace kai ka aiko shi ya ɗauki mutumin da ka kawo kwanaki baya.
Jin_jina kai yayi ya juya ya nufi cikin gidan shikuma baba ya koma ɗakin sa.
Dama yayi hakan ne dan yaga idan da sa hannun sa a ciki.
Uncle Mubarak Kawai ya shiga dashi ya bar su Abdul a mota sai Saif da yake nishi ɗai_ɗai, saida ya maida shi ɗakin da yake yace kawo ka kwantar da hankalin ka me kake ma sauri ai na gaya ma bazaka fita ba saidai gawar ka.
Murmushi Mubarak yayi yace baka sanni ba yaro indai ina numfashi sai na bar gidanan.
Har Deedat ya kai bakin ƙofa ya tsaya ya juyo da murmushi yace ni kuma ina jiran mahalukin da ya isa ya fitar da kai, daga haka yasa kai ya bar ɗakin inda yayi parking ya nufa yaja suka bar gidan, Abdul Majid yace to ya za'ayi da wanan ɗan iskan?
Saina gama masa hukunci sanan na miƙa sa ga hukumar mu nasan suma bazasuyi masa da wasa ba.
Kana ganin zasu hukun tashi kuwa?
Eh mana ai yanzu ba a matsayin soja zasu ɗauke shi ba a matsayin ɗan ta'adda za'a ɗauke shi.
A haka suka nufi gidan da ya ɗauko motar fitar da Saif yayi yasaka shi cikin wani ɗaki dake ta baya, sanan suka nufi gidan part ɗinsa ya suka nufa gaba ɗaya.Kuyi maneji Please bana jin daɗi ne.
Don't forget to:
Comment
Share
Vote
FollowIt's Rashma
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...