🌹🌹 DEEDAT🌹🌹
Writing by RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page 56
Oh abun ne ya tashi kenan.......
Idan bakada abin cewa na kashe waya na... No ango mu kar ka kashe, kana ina?
Wai meye ne ina gida. Ok zanzo muyi magana. To sai kazo daga haka ya kashe wayar. Tashi yayi ya shiga banɗaki ya watsa ruwa masu ɗumi, ya saka wando wanda ya tsaya masa iya gwuiwa da farar riga, sanan ya taje sumar kan sa ya fesa turare sanan ya fito waje gurin da yaran sa suke zaune ya nufa, tunda ga nesa Captain Bilal ya hango sa, yace Allah yayi hallita acan gurin, Vector yace cikin gwaran ci hausar sa ai duk wacce ta aure oga ta more.Wai baku san anyi Engagement ɗin oga ba?
Haba yaushe akayi?Hmmm nima a barack naji wai anyi kuma za'ayi biki nan ba da daɗewa ba.
Isowar sa gurin shi ya katse masu firar sa da sukeyi. Ga dukkan alama gulmata kukeyi, dan naji ana........ A'a oga dama muna magana ne wai munji anyi Engagement ɗinka shine muke magana, cewar Vector.
Mintsilan shi Bilal keyi amma baiyi shiru ba saida ya ƙarasa maganar sa, dan sun ma manta da ba'a gulma da Vector yanzu zai tona asiri yaja masu wahala.
Murmushi yayi yace eh haka ne insha Allahu nan ba da daɗewa ba za'ayi......
Kan ya ƙarasa suka yi shewa, shi Vector harda tashi yana rawa yana waƙar su ta yarbawa. Murmushi Deedat keyi har fararen haƙoran suka bayyana, idan ka gama rawar kaje ka yiman take away.
Oga abin farin ciki ya samemu zamuyi Madam.
To naji yi sauri. Karɓar kuɗin da yake miƙa masa yayi sanan ya kama hanya fita, Deedat yace to a ƙafa zaka tafi ne?No sir zan samu taxi...... Zo ka ɗauki mota kayi sauri, angama ogan mu, kuma ango.....
Ganin yana kusan toshi yasa cewa sorry yana dariya ya nufi gurin da ake parking ɗin motaci. Girgiza kai kawai Deedat yayi ya koma part ɗinsa, wayar sa ya ɗauka ya kira wanda yake gadin Saif yace masa suzo tare yana gida.
Sanan ya kira wanda yake masa biza ya masa maganar biza su Innah, ya ce zata samu nan da sati biyu amma sai sunzo da kansu.
Bazaka yimana ƙoƙari musamu kafin satin biyun ba, to zanyi iya ƙoƙarina naga ko za'a samu cikin sati ɗaya. To nagode insha Allahu zasu zo kayi mani ƙoƙari. Daga haka sukayi sallama, ji yayi ana ƙwan ƙwasa masa ƙofa, izinin shigowa ya bada, da sallama ya shiga tashi yayi zaune yace yadai Adnan har ka iso? Ba dole na cikama bujena iska na zo ba kafin anjima na nemeka narasa. Meka maidani me?
Nafa san halinka yanzu zamu iya jinka London ko US, dariya yayi yace wato har kun samin ido ko?
To ai kai ɗin ne ƙasashe ƙalilan ne bakada office.
Naji ya akayi ne kace kanason magana dani?
Eh dama wani sabon case ne ya taso.......Inajin ka. Wato wata mata muka kama jiya a airport tana ƙoƙarin fita da wasu ƴan mata waje da sunan karatu zata kai su da koya masu sana'a, to sai gashi da muka bin cika ba haka bane.
Yanzu ina ƴan matan suke da kuma matar?
Duk sunan cikin barack. Ok shikenan zuwa gobe zanzo nagan su daga nan sai mu maida su gun iyayen su....... Shiru yayi jin ana ƙwaƙwasa ƙofa tashi yayi dan yasan Vector ne ya dawo, buɗe wa yayi ya karɓi abinci, yadawo ciki bisimilla yayima Adnan.
Ahaka zaka ci bazaka zuba a filet ba?
Ammah basa nan kuma banason shiga part ɗinsu waɗannan ƴan iskan masu aiki suyi ta kallon mutum, shiyasa banason shiga dan zan iya halaka su.Dariya Adnan yayi yace ai kai ɗin ka cika kyau kamar kai kayi kanka. Mtswwwwww ai bakuda aiki sai faɗin wanan nada kyau wancan bayada kyau....... Wayarsa da ta ɗau ƙara shi ya katse masa zancen da yakeyi, da sauri ya kai hannu dan yaji ringin ɗin da ya sakama Sa'imah ne, wa, alaikumussalam, kwantawa yayi yana lumshe ido dan ba ƙaramin farin ciki Muryar Sa'imah ke sashi ba.
Sai yanzu kika tunani ko?
Murmushi tayi har yanajin sautinsa, sanan tace haba my D kaima kasan ba haka bane, tun ɗazu inaso na kira ka amma sai nace bari na barka ka huta. Ai kinsa bana jin gajiya indai dake zanyi waya. To yayi me kakeyi yanzu?
Ganinan an siyon abinci zanci. Allah sarki gwauro har kabani tausayi. Kutt ni kike kira gwauro kuma ma kima daina jin tausayi na dan kice abin tausayi bari kishigo...........
Ƙit ta yanke wayar dariya yayi ya shafa kansa yace zakiyi bayani da harshen hausa.
Gyaran murya Adnan yayi, kallon sa yayi ya zabga masa harara yace magulmaci meye ne ka zuba ma mutane ido ka saurare....
To dan kana soyayya saina toshe kunaina ai bazasu zanyi nima ɗau darasi ashe haka ka mace bamu sani ba. Kai tashi ka tafi yamma tayi.
Oh korata zakayi dan naji kana soyayya.
Saif ne yayi sallama ya, amsa masa sukayi hannu ya bama Adnan suka gaisa sanan yabama Deedat zama shima yayi suka ci gaba da fira ba laifi bai rame ba dan Deedat yasa doctor yana kula dashi.
A tare suka yi sallan magariba suna fitowa Adnan ya musu sallama, ya tafi jerowa sukayi suka nufo gida saida suka shiga ciki sanan Deedat yace kayi haƙuri da abinda nayima. Haba my man meye na bani haƙuri bayan laifi nayi ka hukun tani.
To duk da haka dai kayi hakuri.
Bakomai ya wuce ya hajiyar mu? Murmushi Deedat yayi yace Hajiyata dai ta kusa zama tawa anyi baiko sati biyu da suka wuce.Cikin jin daɗi yace kace ka kusa angwan cewa kabar mu da kwanan shago.
A gurguje
Bayan sati ɗaya su Innah suna ta shirye_shiryen tafiya, satin su ɗaya da zuwa Abuja dan tare da su Ammah suka dawo Innah na ganin gidan su Deedat na Abuja duk sai ta raina kanta taga wanda ya basu ba komai bane.
Ana gobe tafiyar su suna zaune gaba ɗaya suna kallo Deedat yace ya AbdulMajid dakai ga za'ayi wanan tafiyar. Mene? Kayi hakuri ya Abdul kafini sanin ciki da wajen Dubai ni ban san Dubai sosai ba shiyasa na haɗa mana tafiyar da kai.
To basai ka gayaman da wuri ba na shirya kayana ba. Ai nariga na shirya mana komai. To dan kaine da ba wanda ya isa yayi mani irin haka. Nagode my babban yaya.
AbdulMajid bai kula shiba ya maida kallon sa ga gwaggo yace Gwaggo ya sunan mahaifin maman ku dan dashi zamuyi amfani wajen bincike?
Sunan sa Umar ibni Yusuf. Shiru yayi na wani lokaci sanan yace babu wani laƙabi da ake kiransa wanda zamu samu sauƙin bincike?
Anace masa Nuur. Sunan mahaifin ku fa da sunan yayan naku, da ƙanwar ku?
Sunan mahaifin ku Alhassan fari, sunan yayana kuma Abddallah Alhassan fari, sai Sa'imah Alhassan fari. Miƙawa yayi tsaye yana cewa Alhassan fari fa kikace?
Eh ka sanshi ne?
Niko nasan sunan dan sunan family mu ne.Deedat yace kai tsaya kanada tabbacin sunan family kune tunda ba kukaɗai ne masu irin sunan ba. Haka ne ba mu kaɗai ne masu irin amma da mamaki sunan da ta faɗa na ƙarshe sunan kakar mu ne.
Muje zuwa
Please kuyi haƙuri da wanan abubuwan ne suka min yawa insha Allahu gobe zaku samu more typing.
Don't forget to:
Comment
Share
Vote
Follow
Follow
FollowIt's Rashma
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...