🌹🌹DEEDAT🌹🌹
Writing by RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page 28
Fitowar su kenan daga lecture, suna zaune k'ark'ashin bishiya suna duba abunda aka yimasu.
Dama kuna nan nake ta ne manku, "cewar maman Afnan da yanzu suka zama k'awaye" ya akayi ko tasamune?
Babu wani abu da ya samu kawai dai inaso a k'ara yi man bayani karatun mu na yaune dan wlh ban ganeba.
Wanan kuma aikin Sa'imah ne ko M Sani.
Ga dukkan alamu gulmata kukeyi, cewar m Sani da ya karaso.
Kinga d'an halak ana maganarsa sai gashi"cewar maman Afnan"
Eh gulmarka mukeyi sai ka yanka naman mu kaci.
To aunty bala'i sai ki bari mutane suyi magana.Ku kam kan bani ko ina sai kun nuna hali, sauki na d'aya Zarah ba' a makarantar nan takeba da kunsa man ciwon kai.............
Bata k'arasa ba wata mota tazo da mugun gudu ta wuce ta fallatsa masu ruwan da suka kwanta kasacewar jiya da dare anyi ruwa.
Gaba d'aya fararen kayansu sun baci har ta karsun hunun su, musan man Sa'imah datake gefen da motar ta wuce Azafafe ta, tashi wanan wane irin mahaukaci ne da yake tuki sai kace dabba.......
Dan Allah Sa'imah kirufa mana asiri kiyi hakuri kar ki tanka masa wlh zaki iya rasa gurbin karatun ki dan Wlh zai iya sawa a kore ki.
"Cewar maman Afnan"Ai wlh sai naje inyaso ya kashe ni karewar yasa a kore ni.
Sarah kuwa aranta take cewa lallai yau akwai kora, antabo zuciyar fulani saidai yanda hali yayi .....
Maganar da M Sani keyi shiya dawo da ita daga zancen zucin da takeyi, kinga bestee ki yi hakuri ki rabu dashi.
Bangane na rabu da shiba shi din d'an gidan uban waye da har zai fallatsa ma mutane ruwa amma kuma ya ga gara tsayawa.........
Shiru tayi ganin motar tayo reverse ta dawo, kugu ta rike tana jiran fitowa wanda ke ciki.
Maman Afnan kuwa hannu ta d'ora a kai, tace mun shiga ukku.
Motar na tsayawa m Sani yayi saurin zuwa gurin sa , dan Allah munawwar kayi hakuri bata sanka bane.
Cike da takama da isa yafito daga motar gurin Sa'imah ya nufa yace na dawo ne domin naji me kike cewa.
Cewa nayi hala kai makaho ne baka ganine kana driving sai kace dabba.
Wani murmushin mugunta ya saki sanan ya tsuke fuska yace ga dukkan alamu ke bakuwa ce a makarantar nan idan ba haka ba da kud'i ma akace ki tanka mani bazaki yiba amma bakomai zan koya maki hankali.
Itama murmushin tayi tace dame kake ta kama dashine inaso kasan wani abu ba komai kake so kake samu ba, haka idan kanayiwa wasu kana cin nasara to kasani, ni nafi karfin duk wani iskancin ka.
Tabas da kinsan koni wanene da kuma had'ari na ko da wasa bazaki tsaya a gabana kina gaya min magana son ranki ba.
Wani uban tsaki taja ta juyar da kanta gefe.
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...