page 52

2K 125 8
                                    

🌹🌹 DEEDAT🌹🌹

Writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah))🤜🤛

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

PAGE 52

Miƙama Iya wayar yayi  karɓa tayi ta kara a kunne tayi sallama, amsawa Sa'imah tayi ta gaida ita.

Iya tace kishiya kullum anata yimana rowar ki sai yau Allah ya nufa.

Murmushi mai sauti Sa'imah tayi tace hakane kam ya gida da mutanen gida?

Lafiya lau gida mutanen gida kuwa gasunan sun zagaye ni suna son na basu.

Wani irin daɗi Sa'imah taji jin ana son magana da ita sai taji Deedat ya samu gurbi a zuciyar ta.

To iyar mu duk ina gaida su nima ina son magana dasu.

To duk zasuji.......
Abdulsamad yace wane zamuji bamu zakiyi mu gaisai da wacce tafi mata sa'a.

Sa'imah najiyo maganar sa tagane baya jin Hausa sosai, dariya tayi tace to iyar mu bashi mu gaisa.

Iya tace anƙi a baka ɗin.

Ummi tace nidai iya kibani mugaisa da ƴata.

To ƴar nan nagode bazasu bari muyi fira ba ga mamanki idan nazo har gidan ku zanzo na wuni muyi fira.

A'a iya insha Allahu idan kuka zo zanzo na maki wuni.

To nagode ƴar albarka ga ummin ku, ta miƙa ma ummi  ƙasa tayi da muraya cike da ladabi suka gaisa sanan ta miƙa ma Ammah tace gashi ki gaisa da ita.

Murmushi Ammah tayi tace aini na santa dan haka kuyi kawai.

Abdulsamad ya karɓi wayar yana cewa bani ki gani kafin wanan ya karɓe wayar sa ita bakiga ɗan fari bane tanajin kunya.

Tashi Ammah tayi tace kanku akeji ni dai nayi gurin mijina saida safe.

Haka sukayi ta waya da ita saida Deedat yaga basuda niyar bashi wayar sa yace kai nidai bacci nakeji ku bani naje na kwanta.

To ƙanwar mu sai munzo saida safe kifa shirya mana abu mai daɗi kafin muzo.

Sa'imah tace me kake so?
Abdulsamad yace nidai dambu nakeso dariya tayi tace an gama babban yayanmu.

Deedat bai bari ya sake magana ba ya karɓe wayarsa ya bar falon.

Da harara Abdulsamad ya raka shi oho shi baima san yanayi ba.

Iya tace bara naje na kwanta kunsa halinsa ai meye na ɓata rai.

Ummi ma tashi tayi ta nufi ɗakin ta tana shiga ta kira mijin ta suka fara fira.

Sun daɗe suna fira sanan sukayi sallama.



Washe gari tun asuba maman Afnan ke kiran ummi tana tambayar ta sun taso, saida tayi cikin ta da faɗa sanan ta maida akalan kiranta ga Deedat.

Misalin ƙarfe shida ta sake kiransa da taji ko sun fito, yana ɗaugawa yace mrs damuwa ya ake ciki.....

Kun fito ne?

A'a yanzu dai nafito daga wanka.

Ok Allah ya kawo ku lafiya.

Amin ya amsa, sanan yace dan Allah kije ɗayan gidana da ke kusa da na su Sa'imah kiduba kiga ko an gyara mashi dan anan zamu sauka.

DEEDATWhere stories live. Discover now