page 27

1.9K 122 1
                                    

🌹🌹 DEEDAT🌹🌹

Writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

page 27




Kaga malam bamason shirme, ka karba ku cire kud'i ku.

Mama dan Allah kiyi hakuri wlh bazai yu mu karba ba.

To ai sai mu fasa siyen kayan  tunda baza a siyar mana ba.

Bashiri yasako kan kujerar sa, k'asa ya duka yana rokon Innah,mama kidubi girman Allah kar kusa akore ni wlh dakyar nasamu aikin nan nasha wahala sosai sanan kuma inada iyali, ga mahaifinta a asibiti, wlh yace in har na karbi kud'i ko kuma baku d'auki kayan ba abakin aikina.

To zamu d'auka amma ka gaya mana wanene ogan da yabaka wanan umarnin?

Kiyi hakuri hajiya ya gar gadeni akan kar na kuskura na fada.


To  munji zamu dauki kayan ko dan kai amma ka Kira man shi inason magana da shi.


Shiru yayi sanan yace to bari nakira shi, wayarsa ya janyo  wayar sa yana dubawa, sanan ya kara akunne sa, bugu biyu ya d'aga.

Hello sir saida suka gasai sanan yace oga dama hajiya tazo  itada maman ta  sunyi siyayya nagaya masu kace kar akarba.

Shiru yayi yana sauraren abunda ake gaya masa.

Nidai banaji mai oga yake cewa.

Eh gasunan ok sir, wayar ya mikama Sa'imah, babu abinda gabata keyi sai dum_dum saida ta dafe kirji, cike da sanyi jiki ta kara a kunne.

Shiru tayi batayi magana ba, idan bazakiyi maganaba meyasa kika ce akirani?

Daram taji gabanta ya fad'i batasan dalili ba, amma tanaji kamar tasan muryasa.

Ko bakijana ne?

Taji muryasa ta katse Mata tunani.

Shiru ta k'ara yi sai can tace dama inason insani dalilin da yasa kace kar a karbi kud'i mu bayan bamuma sankaba koda ma ace mun sanka bazamu karb'a ba dan kud'in yayi yawa.

Shine dalilinki to kar ki damu hajiyata .............

Bata bari ya karasa ba tayi saurin cewa you dama kaine kake man yawo da hankali?

Dariya da bai taba yiba ya kwashe da ita yama manta da cewa a airport yake.

Kinga adana mamakin ki sai nazo.


Baki tasaki jin yana dariya ita dai zata iya cewa ko murmushi bata taba gani yayi ba bare dariya.....

Hajiyata ina airport yanzu me zaki shirya man idan nazo?

Baki ta murguda kamar yana gabanta, bata bashi amsaba ta kashe wayar tamika ma carshea wayarsa.


Waye ne ?taji muryar Innah

Deedat ne Innah, idanu ta rufe da tafin hanunta tana murmushi kawai jinta takeyi cikin farin ciki marar misltuwa.

Ikon Allah dama shine mai wanan shagon, kaga yaro kud'in sunyi yawa ka karb'i ko rabine.

A a mama ya riga yace kar a karba,  kai kuzo ku kai masu kayanan a mota, yayima ma aikatan gurin magana shikuma sai faman saka kayan yake a leda.

DEEDATWhere stories live. Discover now