🌹🌹DEEDAT🌹🌹 Wattpad rashmarrka Writing by (maman khady) Page 20 Washe gari gu

1.9K 108 9
                                    

🌹🌹DEEDAT🌹🌹
Wattpad
rashmarrka
Writing by (maman khady)
Page 20
Washe gari guraren 10 jirgin su DEEDAT yadaga zuwa Australia  sun sauka cikin dare bai fadama yaransa zaizoba dan haka babu Wanda yazo daukarsa taxi suka hau shida saif hotel suka sauka dan asirance yashigo garin shiyasa bai nufi gidan saba  saida yayi wanka yaci abinci sanan yakira Ammah yagayamata yasauka sunagama waya yakwanta sai baccin gajiya bashi yatashiba sai gurin 6:30 dasauri yadiro daga kan gadon dan yamakara wanka yafarayi sanan yayi Alwala yafito daure da towel daure a hugunsa sanan yana rike da daya yana tsane jikinsa jalabiya yasaka sanan yayi sallah asuba yana gamawa  yanufi gurin kayansa baima shafa maiba yasaka wando 3 quarter yatsayamasa dai 2 guiwa yasaka riga mai karamin hannu yaje gaban miro yataje sumarsa yafesa turare  fesin cap yasaka bakaramin kyau kayan sukayimasa ba fita yayi yakule dakinsa tafiyarsa yayi batare da yaje dakin da saif yakeba  kamfanin karafuna ogan su Alhji bala yanufa handkerchief yasaka yarufe rabin fuskarsa  yana shiga security suka taso suna tambayarsa   yacemusu shi bakone yanaso yaga gurarene  cemasa sukayi to zasu hadashi da wadanda suke nunama baki gurare  office din wani yakaishi  mutumin da aka nunamasa yataso yana murmushi yace sunana johsif DEEDAT ma yamika masa hannu yace nikuma Ahmad johsif yace kabiyoni duk da turanci sukeyin magana yakaishi gurare da dama amma bangare daya yaki kaishi  gurinma  matakan tsaronshi yayi yawa dakallo DEEDAT yabi gurin johsif daya lura sai yace masa kayi hakuri ba ashiga gurin murmushi kawai DEEDAT yayi yace shikenan nizantafi sukayi sallama DEEDAT yadawo masaukin su bai dade dashiga dakisaba saif ya kwankwasa masa yabashi izinin shigowa zaune yasameshi akan kujera laptop nasaman cinyarshi yana dannawa da alama aiki mai muhimanci yakeyi saif yace man inah kajene nazo bakanan baidagoba kuma bai bashi amsaba hakan baidami saif ba dan yasaba da halin DEEDAT  saida yagama abunda yakeyi sanan yace kashirya gobe da safe zamuje kamfanin ogansu Alhj bala na karafuna amma ni bazan shigaba zakaje kai daya zakacemasu kazo daga Nigeria ne kanaso kaga gurare zasu nunamaka amma akwai bangaren da bazasu kaikaba zan tsaya get din baya zanyi amfani da camera metashi kamar jirgi gurin yanada tsaro sosai  bazasu bari jirgin yashigaba zasu maida hankali agirin jirgin nikuma zan nemi muhadu da ogansu zancema inah son sayen karafunane jinjina kai saif yayi yace to amma meye amfani shigata tashi DEEDAT yayi yaje gurin wendor yasaka duka hannaye sa cikin aljihu  sanan yace idan kaje zakaga ammfanin zuwan naka saif yace shikenan zan danfita DEEDAT yace saikadawo saif yace bazaka jeba girgiza kai yayi saif yace to sainadawo yace adawo lfy
****
Ayau su SA IMAH suka fara weac da neco sarah ce tashigo gidansu SA IMAH sallama tayi innah ce kadai afalo tana kallo gaida innah tayi tace innah ina wanan yarinyar SA IMAH dake bayanta tace kambu wacece yarinya Sarah ta tsuke fuska tace yodawa nake bayanke kanta SA IMAH tayo dagudu Sarah tabar falon tana dariya SA IMAH tace zankamaki ai yarinya  sallama tayiwa innah addu a innah tayimasu sanan tafito koda tafito tasamu Sarah da driver dinsu sunajiran tace gaida driver yana ciki da fara a ya amsa shidai yarinyar tana burgeshi shiru shiru da ita batason magana ko kadan abakin get ya ajiyesu yajuya yakoma gida sukuma suka shiga makaratar suna fira dangane da exam dinda zasu fara Sarah ce kecewa Allah yasa sit daya za a ajiyemu dan nasan kinshanye komai SA IMAH tace kinganni nan babu abunda nakarata baccina nasha Sarah tace wlh banyarda wata classmate dinsuce maisuna khadija tace S.S juyowa sukayi dan hakanan ake kiransu wasuma cewa sukeyi yanbiyune   khadija tace tundazu nake jiranku muje library mukaratu kafin time yayi SA IMAH tace inah m sani ko baizo bane khadija tace yazo mana tare muke yanzu yashiga SA IMAH tace shikenan mushiga danni babu abunda nakarata khadija tace ai ko bakiyi karatuba zakici hmmm kawai SA IMAH tace Sarah tace rabu da ita dan Allah yaza ayi tace batayi karatuba muyarda hmm kawai SA IMAH tace dan tasan duk yanda zatayimusu bayani bazasu yardaba  duk makaratar kowa yasansu su khadija Abubakar sai Sarah umar SA IMAH Abdullahi saikuma Muhammad sani kowa yasansu saboda kokarinsu sanan gaji dakai basa kula kowa kaf makaratar babu wanda baisan suba
gunrin wani matashi suka nufa Wanda bazai wuce 20 years ba zama sukayi dagowa yayi yace S.S sai yanzu kuka karaso hararsa Sarah tayi tace kaga makaho bamason iyayi dan yau karigamu zuwa murmushi yayi dan yasaba da wanan sunan datakeyimasa sbd bayagani sosai said a glass shiyasa takecemasa makaho shikuma bakaramin burgeshi takeyiba shidai yana sonta SA IMAH takatse masa tunani dacewa M sani rabu da ita muyi harkar gabanmu  tsuke fuska Sarah tayi basubi takantaba yace kinga wlh wanan topic dinne banganeba SA IMAH tace muganshi mikamata book dinyayi taduba sanan tace wanan ai bayada wuya nan take tafara yimasu bayani  shuru dukan su hankali sukamaida gurinta babu wanda yasake magana saida takai aya tafi sukayimata khadija tace wlh bangane abunda malamin nan yake nufiba sai yanzu m sani yace bare ni SA IMAH tace kunga kutashi mutafi lokaci yakusa sarah tace ahaka kikecewa bakiyi karatuba SA IMAH tace wlh banyi karatuba tattara kayansu sukayi suka nufi class dinsu 

yau sauara sati daya bikin Anwar shirye shirye kawai akeyi innah ce tahadamasu Mayan lefe yayi kyau sosai Ammah tayaba sosai har suka kulla kawance da ita yanzu sun sakata acikin hidimarsu

Tabangaren Amarya suma suna shiri sosai iyakar karfinsu Sosai suke gyara yarau sai zumudi sukeyi danginsu kuwa sai cewa sukeyi auren jari ne zasuyima yarsu kwadayine yasaka ya aurar da ita  ga dan gidan  mataimakin gwamna hakadai suketa zaginsu amma cikin iyayen nata babu wanda yatankasu

Jiddah kuwa kwana biyu bataga DEEDAT ba tarasa wanda zata tambaya bataganin Ammah bare ta tambayeta sanan ita Ammah basakarmata fuska takeyiba bare ta tambayeta tarasa yanda zatayi gamaganin da mamanta tabata tabarbada masa lemo   gashi batagan shiba bare ta aiwatar da aikinsu duk tarasa mafita yaude ta kudi niyar saita ganshi koda samudawan yaransa zasu kasheta
****
Ayaune su DEEDAT zasuyi meeting da sugaban kamfanin karafuna  yana zaune agurinda baki suke zama yana danna laptop sanye yake da blue suit sai wani glass da yamannah a idanunsa yayi kyau sosai wata bauturiyace tace yashigo yace to wani abu yadauko yamakala akunneshi sanan yace saif kashirya yace ok sr kofar office din yaturo yashiga    nunamasa gurin zama akayi yazauna john yace meya kawoka kasarnan DEEDAT yace nine director na   TONNELL INVESTMENT L.M.T laptop din yamika masa yadu sanan yace to mekakeso nayimaka DEEDAT yace  inah son sayen karafunane agurinka dan ance sunada kyau sosai sanan inah so ka tayani neman wani john yace tayaya zantayaka nemansa DEEDAT yace  Kanada karfi anan shiyasa zan hada kaida kai naci kaniyar wani jaki dabba marar hankali sanan nakoyamasa hankali jinjina kai John yayi yace kajira awaje zan sake kiranka OK DEEDAT yace yana fitowa yadafa abunda yasaka akunnesa yace saif kanajina tabangaren saif yace eh yace kayi sauri kafito inah fatan kahadamana kayanmu yanda  nagayamaka dai ko yace eh DEEDAT yace OK muhadu airport baijira amsawar saif baijira amsawar saif ba yacire abun daga kunnesa mota yashiga yacema driver daya dauko yace yakaisa airport
DEEDAT yanafita john yace akiramasa Alhj bala yanadauka john yace DEEDAT yana inah Alhj bala yace yana kano bikin dan uwansa john yace to bayacan yana nan Australia saida gaban Alhj bala yafadi aransa yanacewa tome yakaishi Australia batare da john yasake maganaba ya katse wayar wani yaronsa dake kefensa yamikama wayar yace kira kace yashigo   yakira akacemasa ai yatafi  john yace akirashi kiran DEEDAT sukayi dagawa yayi yace ya akayi mutumin yace ya kuma katafi DEEDAT  yace kabawa jakin shugabanku waya mikamasa wayar yayi yakara akunne DEEDAT yace nasan kanajina kakira awaya kanayiman banzar barazanarka shine nikuma nazo gabanka inga kalar iskanci ka to naga kai bakakai matsayin da zanyi fada dakaiba Abu nakarshe dazan gayamaka sunan mahaifina yafita bakinka
Koda yatsansa bazaka iya tabawaba bare kuma kace zaka kasheshi daganan yatsinke wayar John yace inah abincika min wanene AHMAD DEEDAT HASHIM wani daga cikin yaransa yanajin sunan sa saida zufa takaryomasa yace ranka yade nasanshi sojane sanan bakasarsa kadai yakeyima aikiba har kasarnan yanayiwa aiki nidai shawarata kar kayi takon saka dashi dan wlh bazaka iya dashiba idan kace zaka jadashi to wlh bazaka kai lbr ba john yace aikuwa idan yana taba wasu yakai lbr to ni bazan barshiba har kasarshi zanje na wulakantashi duba min awane guri suke yanzu yace OK sr cikin mintuna 15 yagano inda suke yace ranka yadade suna airport yace ok inah so narigashi saukau kakira jirgi yace OK sr 

Saura minti 10 jirginsu yatashi ya iso airport din dasauri yanufi gurinda yahango saif yace muje saura 10 minute saif yace muje wayar DEEDAT CE tadauki kara yana dubawa yaga Anwar dagawa yayi yace anace yakayine Anwar yace ninema anace DEEDAT yace kwantar da hankalinka ganinan zuwa yanzu haka inah airport Anwar yace Allah yakawoku lfy have amin Anwar yace baby ka tace kayimata tsaraba yace DEEDAT yace to

DEEDATWhere stories live. Discover now