57

1.7K 104 1
                                    

*🌹🌹 DEEDAT🌹🌹*

*Writing by RASHIDA USMAN*

*Wattpad*

*rashmarrka*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

page 57

Dayake ita kaɗai take da wanan sunan ko?
Ba'ita kaɗai keda sunan ba amma  bayanin da tayi yayi kama da family mu sosai.

Koma dai menene idan munje zamu gani, bara naje na kwanta gobe tun safe zamu fita.

Kilama kafin ku dawo su Abu sunzo. Cewar Abdulsamad,  ummi tace aiko dai kafin kudawo sunzo dan ɗazu munyi waya dashi yace tunda munƙi dawowa tarkato maku matan ku zaiyi ya kawo maku.

Ammah tace kinga kenan zamana da yarana ya tabbata. Taɓe baki ummi tayi tace kanku dai akeji ni baku gabana. Ita dai Innah bata saka baki ba sai murmushi takeyi.

Miƙewa Deedat yayi ya musu saida safe, har yakai bakin ƙofa yaji Gwaggo nacewa jan ƙosai zo kasiyon rama nayi masu tsaraba na manta ban siyaba.

Baki buɗe ya waigo yana kallon ta yace "waike meyasa bakiso a zauna ƙalau an gaya maki nan Kano ne dazakice na siyo maki rama ina zan samu..." Bama wanan ba ban hanaki ceman jan ƙosai ba?

Ance maka jan ƙosai kayi ƙuli_ƙulin Rakkiyya dani.
Aiko zaki gani bara nakira Captain Sagir yamin waj......... Bai ƙarasa ba yaji saukar filo ƙirjin sa, kallon Ammah yayi yace haba Ammah taron dangi zakuyi man ina cewa nafasa. Yoooo kafasa mana angayama bamusan hanya ba...

Kallon Gwaggo yayi yace bari ganin an tare maki duk mukaje sai na ɓatar dake. Ɗan kwali ta turo gaba tace koda aka haifeka nasan Dubai bare ka ɓatar dani.

Jinjina kai yayi sanan yasa kai ya fita batare da ya sake cewa ko ƙala ba, yana shiga part ɗinsa ya janyo wayar sa ya kira Sa'imah dake ɗaki kwance tana chatting da Sarah, murmushi tayi sanan ta ɗaga, sun jima suna fira sanan sukayi sallama.

Washe gari da misalin  tara na safe (9am) driver da security ɗinsa suka kai su Airport, sit ɗaya ya zauna da Sa'imah, AbdulMajid yana ta hararar sa amma yaƙi kulashi.

Har ya gaji ya koma gurin su Gwaggo ya zauna sukayi ta fira har suka gaji  kowa yayi shiru barinma Gwaggo da Innah.

Sa'imah kuwa dauriya kawai takeyi.

Koda suka sauka motocin gidan su AbdulMajid sunzo suna jiran ƙaraso warsu, shiga sukayi suka nufi family House ɗin su, dama tunda zasu taso ya kira aka gyara masu part ɗin da suke sauka idan suka zo Dubai, Sa'imah na shiga ɗakin da aka nuna mata ta zube kan gado ko takalmi bata cire ba, ta lumshe ido duk jitake jikin ta na mata ciwo, ƙofar da aka turo ne yasata buɗe idanun ta domin ganin waye yashigo, wata matashiyar budurwa ce tashigo hanun ta ɗauke da tire an ɗora ruwa da lemu sai dabino a gefe cikin wani ɗan kwano.

Gaishe ta tayi da larabci,  amsawa Sa'imah tayi da ɗan guntun larabci da take ji, ajiye kayan hanunta tayi sanan ta juya ta fita.
Ta daɗe kwance sanan ta tashi ta nufi ban ɗaki ta watsa ruwa sanan ta fito tasaka doguwar riga marar nauyi, gyalen rigar ta yafa ta rufe kan ta zuwa kafaɗu, fitowa tayi batare da tasha kayan da aka kawo mata ba, tana fitowa falon taga Deedat zaune yana danna lap top  ɗin shi yana aiki ɗagowa yayi ya ƙare mata kallo sanan ya mata murmushi yace bakiyi bacci ba kenan?

Kanta na ƙasa ta gyaɗa masa kai, murmushin yasakeyi sanan ya nuna mata ɗakin da su Gwaggo suke dan, Gwaggo ƙin yarda tayi a raba masu ɗaki da Innah tayi.

Ba musu ta nufi ɗakin tana tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashe ma, da kallo ya bita har saida ta shige sanan ya lumshe blue eyes  ɗinsa da suka fara canza kala akan gajiya, cigaba yayi da aikin sa.

Tana shiga itama ta jingina da ƙofar ta dafe ƙirji tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudu. Ke lafiyar ki kike wanan nishi haka sekace wacce tayi wasar tsere? "Cewar gwaggo dake kwance"

Baki Sa'imah ta turu tace "banason sa'ido."
Ba ido nasa mikiba  ƙafa ce keda ba'a maganar arziki dake. Bata kulata ba ta nufi doguwar kujerar da ke ɗakin ta kwan ta bata jima ba bacci yayi awon gaba da ita. Tafi awa biyu tana bacci sanan ta tashi koda ta tashi duk jikin ta ya mata nauyi, wage_wage tafara ko zata ga su Innah amma bata gansu ba bakowa a ɗakin sai ita kaɗai, da sauri ta sauko daga kan kujerar da take kwance, ta fito daga ɗakin ta a falo tagan su zaune  ga kulolin abinci a gaban su, gurin su ta ƙarasa kusa da Gwaggo ta zauna, ta ɗora kanta akan kafaɗar ta tace shine kika ƙi tashina ko.

Yoo natada ke ki hauni da masifa, nikuma yau banajin faɗa shi yasa nasaka maki nagani. Naji bara naje nayi wanka kuma saura kicinye duka.  Tunda kin maidani akuya dole kice na cinye. Dariya Sa'imah tayi ta miƙe tsaye  ta danufin shiga ɗaki.

Hajiya Sa'imah ina wuni. Cewar Innah.
Lah Innah yi hakuri wanan mai ran ƙarfen ce ta ɗauki hankalina ba gaida keba. Murmushi kawai Innah tayi tace jekiyi wanka ki fito kici abinci.

To my Innah harta fara tafiya Innah ta dakatar da ita tace jeki can ɗakin ki kira mani Anas shima yazo yaci abinci. Ta nuna mata wani ɗaki, ɗakin ta nufa ta ƙwanƙwasa, buɗewa yayi sanye yake da jalabiya baƙa tayimasa kyau sosai saida ta gaida shi sanan ta faɗa masa saƙon Innah, to kice ina zuwa. Juyawa tayi tafaɗa ma Innah sanan ta wuce.

Tana wuce wa saiga Deedat da AbdulMajid sun shigo, gaida Innah sukayi a tare sanan Deedat zauna kusa da Gwaggo  yace yadai matar naga duk kinyi wani iri.  Badole kaga nayi wani iri ba angama yawo dani a sararin samaniya.

To ya bakuci abinci ba?

Zamuci mana  muna jiran autana da Sa'imatu. Tsuke fuska yayi yace waike idan baki ɓatama mutum suna ba baki jin daɗi ne meye Sa'imatu ?

Haɓa ta riƙe sanan tace an ɓata duk abinda zakayi saidai kayi. Tashi yayi daga kusa da ita yace munma ɓata dake. To sai me idan mun ɓata ai tafi nono fari. Haka kikace karfa anjima kizo kina ƴar murya.

AbdulMajid yace wai kai ance an ɓata dakai bazaka haƙura ba kinga matar kuci abinci sai muje cikin gida ku gaisa da kakar mu. To mijin bara mugama sai muje.

Lalaima matar nan yanzu agabana kike cema wani mijin ki. Ɗankwali ta turo gaba,  sanan ta gutsiri goron ta tace yoooo bazan faɗi agaban ka ba me kataɓa bani ........

Lalaima matar nan yanzu bayan kin gama cimani kaji da goro shine yanzu kike yimani gori.  Gaskiya Gwaggo baki kyauta ba kin gama cinye ma yarona kuɗi kuma kice baki so shi. Eh nace banayi ko za'amin dole ne aiga Abdul nan idan ka daina siyaman shi zai siyo mani. Ah kice kin zama lashe moni kenan.

Shigowar Anas shiya ya katse masu firar da sukeyi kusa da Innah ya zauna, bai jima ba Sa'imah ma ta fito tana sanye da atamfa wanan karon, saida ta gaida su gaba ɗaya sanan tasamu guri ta rakuɓe. Miƙewa Deedat yayi yace Bara na watsa ruwa kafin ku gama sai mushiga cikin gida tare.  Ta afito lafiya.

Abinci suka fara ci har AbdulMajid  sun kusa gamawa ya fito yazauna shima yaci sanan suka nufi cikin gida.



Muje zuwa

Please don't forget to:

Comment
Share
Follow
Follow
Follow
Vote

It's Rashma

DEEDATWhere stories live. Discover now