page 51

2.1K 125 1
                                    

🌹🌹 DEEDAT🌹🌹

Writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah))🤜🤛

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

PAGE 51


Washe gari sai gurin ƙarfe goma Deedat ya fito ɓangaren su Ammah ya nufa gaba ɗaya a falo ya same su gaida su yayi, Jiddah ta gaida shi. Ya amsa ba yabo ba fallasa.
Iya tace wai kai yaushe zakayi aure?

Murmushi yayi sanan yace my Iya aini da aure na. Yaushe kayi aure ban sani ba?

Sanan wacece matar taka da ban santa ba?

Kusa da ita ya dawo ya zauna sanan yace maida wuƙa mrs kishi kece  matar.

Iya tace Alhamdulillah har hawan gishiri na ya fara tashi ashe nice, duk da haka ya kamata kayi aure.
Kar ki damu zanyi insha Allah an kusa ma nan ba daɗe wa ba zakiga nayi.
Ammah ya kalla yace Ammah zan fita ku shirya gobe da ƙarfe 8am jirgin mu zai tashi.

To shikenan Allah ya kaimu goben. Amin ya amsa.
Tashi yayi zai fita, ummi  tace ina zaka je ne?

Dakata wa yayi ya waigo yace zanje office ne.
To kadawo da wuri zakayi mani rakiya nayi shopping.

Shagwaɓe fuska yayi yace ummi ba gasu ya Abdul nan ba.
Tsuki taja tace waɗannan ne zasu yimani rakiya ko tare ni akayi aka gagauramin mari babu mai iya kataɓus a cikin su.

Ammah tace bama zasu raka ki ba muma fita zamuyi kuma da kike cewa ragwaye ne sunfi ɗan ki ƙarfi da jarumta.
Naji dai jeka yaron albarka Allah ya dawo min kai lafiya ya tsare mani kai.

Amin ya amsa sanan yasa kai ya fita, yana fitowa yaran sa suka taso suka buɗe masa ƙofar mota ya shiga suka bar gidan kamar kullum yanda suke gudu da mota haka suke tafe saida suka fito daga layin sanan yace su shiga ɗayan layin dake kusa da nasu, shiga sukayi a ƙofar gidan suka faka motacin yace dasu su jira shi yana zuwa, shi kaɗai ya shiga ɗakin da ya kai Saif ya nufa koda ya shiga ya jigata gashi ba'a cire harsashin ba, gurin a kwatin magani ya nufa ya ɗauko ya buɗe allura ya fara yi masa sanan ya cire harsashin sanan ya gyara gurin ya ɗaure ƙafar da bandeji sanan ya tada shi yace "tambayar ka zanyi idan ka kuskura kaƙi gaya mani gaskiya to zanma mafi mumunan hukuci."

Meyasa kake cin amanar ƙasar ka?
Sanan kuma meyasa kaci amana ta?

Kuka Saif ya rushe da shi yace ka gafarce ni akan abubuwan da na riƙa yi maka wallahi sakani akayi ba yin kaina bane.

Naji ka gaya mani meye dalilin ka sanan waya saka ka?

"A lokacin da nafara aiki a ƙarƙashin ka ban jima da fara aiki da kai ba wani aiki ya taso mukaje Kano kasan ni mahaifiyata kaɗai ta rage mani, idan baka manta ba lokacin da mukaje Kano na ɓata na kwana biyu kayita nemana baku ganni ba saida ga baya kukaga nadawo, azahirin gaskiya banje ko ina ba hasali ma ina cikin gidan a wani ɓangare wanda babu wanda zai san da akwai gida a gurin Baban su Anwar ya saka a sace ni shine ya nuna mani mamana a ɗaure shine yace mani yana so na riƙa kawo masu bayanain duk abunda kakeyi sanan yasaka ni  kula masa da duk shige da ficen jami'an tsaro idan zasu shigo da kaya ta ɓarauniyar hanya,  a duk lokacin da naga suna aikata wani abu wanda yafi ƙarfin tunani na nakayi yunƙurin gaya ma nakan tuna gargaɗin su da sukayi Mani na cewa duk lokacin da na tona masu asiri zasu saka maza fiye da goma suyima mamana fyaɗe sai ta mutu wanan garhaɗi shi ke hanani faɗa maka."

To naji wanan waya saka ka sato uncle?

Kuma meyasa kasaka ayima Sa'imah fyaɗe?

Bansan ya akayi ba yasan kana soyayya da Sa'imah nidai kawai ya kira ni ya bani umarnin nayi ma Sa'imah fyaɗe agaban mutane, ganin bazan iya ba ya sashi cewa zai haɗani da wani sai nasaka shi yayi mata, to shine ya haɗani da Munnawar ɗan gwamna shine baya jin tsoro kowa.

DEEDATWhere stories live. Discover now