🌹🌹DEEDAT🌹🌹
Wattpa
Rashmarrka
Writing by (maman khady)
Page 5
Tasaka jakar a cikin Ghana musgo din da kayanta suke ciki
Washe gari tun kiran farko SA IMAH ta tashi dama batayi wani baccin kirkiba sbd zumudin zatabar bakar rugar su wacce tayi mata wuyar zama duk da gabadaya ahalinta suna ciki amma kwata2 batason ganin dangin mahaifinta kuma tadauki alwashi saita gasa masu aya ahannu misalin karfe 7 tabawa tayi sallama agidansu SA IMAH Inna ta amsa mata gaisawa sukayi tabawa tace kuyi sauri kufito kar rana tayi innah fitowa tayi dauke da kayanta ita kuma SA IMAH tana rike da magen ta fara tas tabawa tace badai da magenan zaki tafi da itaba tace da ita zan tafi dan banga Wanda zai hanani tafiya da ita tabawa tace nidai mutafi karki zageni innah wuro dai fitar da kayansu takeyi bata kula zancesuba suna fitowa kofar gidan suka samu mutanen garin cike da kofar gidan tsayawa innah tayi tana kallon ikon Allah batace dasu uffan ba takama hannun SA IMAH sukayi gaba baffa Aminu ne yabiyosu yanacewa Allah raka taki gona mudai mun yadda kwallon mangoro mun huta da kuda juyowa SA IMAH tayi tace ayya baffa Aminu ai ba acanzawa tuwo suna yanan atuwonsa haka zalika kanan amatsayin baffa na bakada wukar kan kare wanan matsayi karubuta ka ajiye ni SA IMAH sai nasa ka raina kanka tayi tsaki tayuce mamaki yatsaya yi wai wanan yar ficikar yarinya take gaya masa haka innah gurinsa tanufa tace hamma Aminu kaja girman ka meyi amfanin wanan abun kunce bakwa sonta to meye na kananun magan ganu gashi kaja yarinya ta gayama magana cikin bainar ja amma ba komai rayuwace tawuce tabarshi da bakinciki suna isa bakin titi dan daga rugarsu zuwa bakin titi 15 munit ne ba nisa tsayawa sukayi dan samun motar da zata kaisu kano basu dadeba suka samu mota sakace masa kano zasuje yace su shi
****
Yana fitowa daga sashen sa yaran sa naganin sa suka tashi tsaye hannu yadaga musu yace su barshi banisa zaiyiba komawa sukayi suka zauna saif yana hagosa yafito motar yanacewa man yane baice masa komaiba yashiga gurin mai zaman banza saif yadawo cikin motar yanacewa gurin my wife zamuje mudauketa zan kaita kamun kawarta tsuki DEEDAT yayi yace shine ka daukoni saif yace a a man akwai maganar da zamuyi but bazaiyu muyi maganar acikin mutane ba juyar dakan sa yayi yana kallon gefen hanya 20 mnt yakaisu gadansu budurwa saif wayar sa yadauka yace kifito dasauri gani bakin get bata wani dadeba tafito ba laifi kyakyawace amma ba fara bace sosai sallama tayi tabude bayan motar tashiga tana ganin DEEDAT ta kama kanta dantasan halinsa gaisheshi tayi bai amsaba dan tasan bazai amsaba din firar su ta masoya sukeyi bakaramin haushi sukaba DEEDAT ba jiyake kamar ya shakesu dan haushi sai tsuke yakeja akai 2 saif juyuwa yayi yace ya akayine man bace masa komaiba ya dan zamo daga kujerar da yake zaune ya lumshe idanunsa saif maida hankalinshi yayi akan tukinsa basu dau wani lokaci ba suka iso gidan su kawar nabila tace thanks sweet Hart murmushi yayi yace karfe nawa zaki koma tace 6 pm yace OK sai nazo daukarki tace to tashiga gidan saida yaga shigarta sanan yaja motar suka tafi DEEDAT yace kai wlh nagaji kayi sauri mugama inah jin bacci saif yace kai maganar dazamuyi akan Alhj bala ne Wanda kace in bincikama kafin katafi India DEEDAT bashiri yatashi zaune yace mutafi gidana muyi maganar OK saif yace
****
Sunfara tafiya tabawa tace nikam Aisha ( innah wuro) kinsan inda zaku nufa kuwa dan bazaku tareman agidaba SA IMAH tajuyo tace bama gidanki zamu saukaba bata bari ta karasaba tace to inah zuku nufa idan kunada kudi kukawo nabaku hayar daki daya wata mata dake jinsu tace baiwar Allah ya yan uwanki bane tabawa tace inah ruwanki ko iyayenane idan zaki basu gidane kibasu nidai bazasu zauna min agidaba matar tace zan basu kuwa innah wuro dai batace uffan ba dan ita mace ce wacce batason hayaniya ko kadan adaidai lokacin da suka shigo kano matar driver dinta tayima magana tace yasamu guri ya ajiye matar nana arazane tabawa ta juyo ta kalli matar tace hajiya dama motar kice a cikin ran tabawa bataso hakaba taso su innah wuro su wulakanta tace dama nasan wanan ba motar haya bace driver yasamu gefen hanya yafaka tabawa tafita tace Alhmdllh mun huta tayi gaba innah kuwa aranta tace kai ashe tabawa batada mutunci matar ta katse mata tunani dacewa baiwar Allah kiyi hakuri haka wasu mutanen suke
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...