page 46&47

1.7K 113 0
                                    

🌹🌹 DEEDAT🌹🌹

writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah))🤜🤛

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

PAGE  46&47

Murmushi malam yayi da yaga yanda takeyi, ruwan zam_zam ya ɗauko ya buƙaci abashi kofi, har Deedat zai fita momy tace ga kofin nan zoka miƙa masa karɓa yayi ya zuba ruwan a ciki  addu'o'i ya a ciki sanan ya tashi ya nufi gurin ta ruwan ya watsa mata a jikin ta,  gaba ɗayan ta aka ɗagata a ta rabu da gadon bata ƙasa bata sama sanan aka sakota jikake tim sanan ta saki wata razananiyar  ƙara.

Kallon Deedat yayi sanan yace inason gaushi da ruwan zafi.

Ammah ce tace to bari a kawo  da sauri ta fita bata daɗe ba sai gata ta dawo ɗauke da filas ɗin ruwan zafi da kasko wuta da gaushe amma irin na kwalin nan ne, miƙa masa tayi ruwan zafi ya zuba sanan ya saka ruwan zam_zam ɗin acikin ruwan wata addu'a yayi sanan ya sake zuba mata su, wata irin shiɗewa tayi sanan tasaki ƙara, ta koma lafewa kamar wacce ta mutu.

Gaba ɗaya ɗakin idan ka cire mazan ciki duk kuka sukeyi, Abdulsamad ma idanun sa duk sun cika da hawaye, Deedat kuwa gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi.

Habbatus sauda malam ya saka gaba ɗaya ɗakin ya tur nuƙe da hayaƙi ihu ta fara yi bai kulata ba ya sake saka garin wani magani a ciki, bashiri Jiddah ta miƙe tsaye, zata gudu malam yace kar ku bari ta fita........

Kafin ya rufe baki Deedat ya kamota ya dawo da ita, magana ta fara tana faɗin sai na kashe ka dama inada haushin ka.
Du yanda yake ciki damuwa saida yayi murmushi yace dan Allah karki barni da rai ki kasheni yanzu_yanzu.
Wani irin juyi tayi dashi, da sauri ya ƙara damƙo ta daban yayi saurin dake wa ba da ta kadashi.

Malam ya sake zuba mata ruwan zafi da zam_zam, wani irin juyi tayi ta kwalla ƙara kaɗan Deedat ya faɗi, bashiri yama su Abdul magana suzo su kama masa, Abdulsamad kam tuni fuskar sa ta wanke da hawaye.

Qur'ani malam ya ɗauko ya fara karanta wa ihu take amma taƙi tayi magana, shi kuma malam abinda yake so kenan tayi magana, amma taƙi tayi.

Saida taga haza sanan tafara bashi hakuri, tsayar da karatun yayi sanan yace inajin ki zaki faɗi dalilin ki na cutar da wanan baiwar Allah.

Mtswwwwww taja tsaki, sanan tace anƙi a faɗa ɗin.
Murmushi yayi sanan ya buɗe jakarsa ya ɗauko wani garin magani ya zuba cikin ruwan zafi nan masu zam_zam da addu'a, ya miƙa ma Deedat yace ku bata tasha..........

Wallahi duk wanda yayi gangaci bani su saina kashe shi har lahira.
Karɓa Deedat yayi yace ai nagaya maki ki kashe ni, bakinta ya matse ya ɗura mata ruwan yana gama bata ta riƙe wuya tana kakari idanunta duk sun fito, karatu malam ya ci gaba dayi, kayi hakuri wallahi zan faɗa maka yanzu da ƙyar take magana.

Bai tsaya ba ya cigaba da karatu saida yaga ta gala baita sanan yace inajin ki kuma kika sake kika yimani ƙarya ƙonaki zanyi.

Saida ya harari Deedat sanan tace bama zanma ƙarya ba. To inajin ki.
Fara basu labari tayi abinda ya haɗa su da Mubarak zuwa rabuwar su da saurayin ta Amar.

Malam yace to meye laifin wanan yarinya ai saiki je gurin wanda ya maki laifi ki ɗauki fansa.

Abinda yasa nafara takan ta lokacin da nazo gidan sa domin na ɗau fansa abinda yayi mani sai naci karo da Jiddah tana ma maman ta rashin kunya duk da ni ba musulma bace amma ina mutunta mamana to da naga rashin mutun cin da take mata yasa ni shiga jikin ta, nasata yin abubuwa da dama sanan nazo mata a matsayin ƙawa nace mata sunan jamcy na dinga zuga ta tariƙa yin abubuwa har sata inasa ta a lokacin da ta gaya mani cewa tanason wanan, ta nuna Deedat, nikuma bana son shi ko kaɗan bansan dalili ba, ni nake kawo mata labarin wacce kake so na dinga zuga ta akan ta kashe ta nima da kaina nasha zuwa na kashe ta amma sai na sameta tanada wani tsari ajikin ta sanan babban abinda ke hanani zuwa kusa da ita tana addu'a kafin ta kwanta sanan tana alwallah sanan tana karanta addu'o'in safiya da marece waɗannan su ke hanani zuwa kusa da ita, danaga haka saina koma kan Jiddah na dinga zuga ta har ta dinga aika mutane su kashe ta duk dan na ƙuntata ma amma ban samun nasara, ranar da muka aika na ƙarshe ne ka kama wanda yaje shine mukayi faɗa da ita Jiddah to shine na bayyana mata ko wacece ni  shine na ɗaure mata jiki gaba ɗaya  da baki duk lokacin da taso magana saina shaƙe mata wuya sai ta kusan mutuwa sanan na sake ta.

DEEDATWhere stories live. Discover now