🌹🌹 DEEDAT🌹🌹
Writing by RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah))🤜🤛BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
PAGE 41&42
Gaskiya nidai Indo gidan ki yana neman ga garata zama.
Kumin bayani mana taya Fa'iza mai aiki ta kasace soja?
Innah Sa'imah zatayi maki bayani nidai gidan zan tafi dare yanayi.To maman Afnan mungode gashi kibama ƙawata, wata leda ta miƙa mata.
To mungode Innah, sai anjima.
Daga haka ta fita Sa'imah ta bita a baya, koda suka isa harabar gidan driver ɗin da ya kawo ta yana tsaye yana jiranta.To nagode sosai maman Afnan da ziyara.
Ba komai matar mu.
Hararar ta tayi, sanan tace "kinga banason haka fa."
Murmushi tayi tace yanzu ma nafara.Kinsan baki shiga gidan su Sarah ba............
Ohhh God dan Allah kar ki gaya mata nashigo unguwar nan.
Tab aiko sai nagaya mata kinshigo, nayita roƙonki kishiga gidan su kiƙi.Lah matar bro wanan sharri haka nidai nayi nan, idan kuma kika yi mani sharri keda Allah.
To Allah ya kiyaye hanya ya saukeki lafiya.Tace "Amin" daga haka tashiga motar suka bar gidan.
Ita kuma Sa'imah tana ɗaga mata hannu, har saida ta daina ganin su sanan ta koma cikin gida.Yau takama assabar a yau ne kuma su Innah zasuje ganin gida, mota biyu sukayi har ta sojojin,da Deedat yabama umarnin duk inda Sa'imah zataje to su tafi tare.
Innah da mamy da gwaggo suna baya Sa'imah ke driving, Dan mamy tace bata yarda Sarah ta ja motar ba.
tunda suka shigo unguwar Innah kecewa "ai wanan unguwar ta manya ce ba irinmu talakawa ba."
Mamy tace "ai sai kiyi kuma dawo wa kam ai kun gama dan sai an karɓi wanan kyautar."Sarah ta waigo tace nidai daga Innah ta dawo nan nima zan tattaro inawa_inawa indawo nan.
Mamy tace "ko mukoma ki kwaso kayanki kafin su dawo kinga ke kin tsufa anan."
Gwaggo tace sha kuruminki ta hanun dama na ai babu wanda ya isa ya hana miki dawowa nan, dadai wanan nunar ranar ce da bazan damuba yanzu ma inah neman wanda zan bawa sadakar ta.
Sa'imah tasan da ita take, kamar bazatayi magana ba sai can tace wallahi idan kika sake magana idan ba ina juye motar nan ta kife ba yau minake.
Ja'ira ni ban tashi mutuwa ba ki tsaya na sauka sai ki juye uwar ki..............
Bata ƙarasa ba Sa'imah ta figi motar da gudun bala'i, ihu gwaggo tafara tanacewa wai dagaske kashe mu zakiyi ki tsaya nace.
Me mamy da Innah zasuyi inba dariya ba duk da suma sun tsorata da irin gudun da Sa'imah keyi.
Jin mota ta tsaya yasaka gwaggo buɗe idanu, taci gaba da faɗa Innah na bata hakuri amma kamar cewa akeyi ta ci gaba saida taga sojojin dake binsu sun nufo su yasaka ta yin gum da bakin ta.Sarah tace Innah kinga dai_dai wanan kwanar aka tashi sace Sa'imah.
Allah sarki Sa'imah na dayanzu ina nan inata kuka, cewar gwaggo, dariya sukayi gaba ɗaya, sanan suka shiga cikin gidan.
Innah sai mita takeyi gida yayi girma daya, bazata iya zama cikin sa ba.
Mamy kam bata kulata ba sai murna takeyi tana yaba kyan gidan.**************
Ammah me kika fahimta dan gane da ciwon Jiddah?
To papa nidai gaskiya gani nakeyi kamar ba ciwon asibiti bane tunda kaji sunce basuga komai ba.
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...