🌹🌹 DEEDAT🌹🌹
Writing by RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
PAGE 55
A yau Deedat da insfe ta Habib da wasu yaran suka kai hari a dajin nan da Deedat ya je da dare shida Saif, sunyi nasarar kama wasu daga cikin su wasu kuma sun gudu kuma sun kama manya su su ukku, duk a buge suke alamar sun sha giya sunyi tatul, har ƴan matan su duk saida suka kama su.
Insfe ta Habib ba ƙaramin mamaki yakeyi ba ta yanda akayi Deedat yasan da wanan gidan ko faɗa ma akayi mutum na rayuwa acikin wanan dajin zaka ƙaryata.Washe garin ranar da sukaje sukayi kame Deedat yayi shirin tafiya Abuja domin ya haɗama insfe ta Habib wasu baya nai da ya kamata ya sani, daga nan kuma ya duba bisa su Innah dayasa ayi masa.
Sallama yaje ma su Innah account number sa ta buƙata ta bashi kuɗin da zaiyi masu biza ɗin amma fafur yaƙi karɓa saida tayi masa jan ido sanan yace shi baisan ko nawa abin zai ci ba idan yaga ko nawa yaci zaiyi mata magana sai ta bada, yayi mata haka ne dan ta bar maganar koda ya bar gidan Sa'imah bata dawo daga makaranta ba kuma ba halin jiran ta dan time ɗin da jirgin su zai tashi ya kusa cika, saidai yakirata a waya.
Su Abdul ne suka raka shi airport sai wasu yaran sa guda biyu, saida suka ga tashinsa sanan suka dawo gida suna masa addu'ar sauka lafiya.
Da misalin biyu da rabi ya sauka, koda fito inda ake paka motoci yaran sa ya gani suna jiran sa, sara masa suke amma hannu kawai yake ɗaga masu buɗe masa suka yi, ya shiga suma suka shiga driver yaja kamar kullum gudu sukeyi sosai, muddin suna tare da ogan nasu, cikin ƙanƙanin lokaci suka kawo gida part ɗin sa ya nufa ya watsa ruwa ya bi lafiyar gado, saida aka fara kiran la'asar sanan ya tashi yaje ya ƙara watsa ruwa masu ɗumi dan jikin sa ya saki sanan yayi shirya cikin manya kaya, sunyi matuƙar karɓar sa.
Masallaci ya je dashi akayi sallah sanan ya fito, ya koma gida mota ya ɗauka ya ransa na masa magana amma ba wanda ya kula cikin su binsa suma sukayi a baya yana ganin haka ya fara sharara gudu ya shiga nan ya fita nan har saida ya ɓace masu, sanan ya fara tafiya ahankali, dan yanzu idan zai wani abu na sirri baya tafiya dasu dan zasu iya ɓata masa shiri.
Gidan da ya kai uncle Mubarak ya nufa, horn yayi mai gadi ya buɗe masa, ya shiga saida suka gaisa da mai gadi sanan ya wuce ciki, ɗakin uncle ɗin ya shiga a kwance ya same shi ya takure, wata mahaukaciyar dariya Deedat ya kwashe da ita, sanan yace ya dai uncle ka gaji da zama guri ɗaya ne hala?
Tashi yayi ya zauna duk ya rame yayi baƙi duk da ba dukan sa akeyi ba kuma ana kawo masa abinci mai kyau amma duk ya fita hayacin sa, wai me kake so danine?
Haba uncle ai lokaci bai yi ba so nake sai nagama da manya ka sanan nadawo kanka domin bazan barka katafi a bulus ba.
To meye dalilin kawo ni nan?
Zama yayi sanan yace abu mai sauƙi ka gaya mani shirin ku sai na sassauta maka hukunci.
Shiru yayi ya soke kansa ƙasa yana tunani, sanan ya ɗago yace ni bansan komai ba.
Wani murmushin mugunta yayi sanan yace kayiwa kanka, idan baka manta ba a kwai wata yarinya da kayima fyɗe cikin tsakiyar dare a hanyar ka ta shigowa Kano........
Tunani ya fara to a cikin matan da yama fyaɗe yacce yake nufi, kasa tunawa yayi, yace wacce daga cikin su dan sunada yawa.
To idan ka tuna ko wacece ka ne meni tunda kwaɗayinka bai tsaya akan mutane ba har ya kai ga aljanu kajama mutane.......
Kai dakata wai me kake nufi ne?Kuma ina matsayin ƙanin ubanka kake gaya mani magana haka.
Alhamdulillah da kace ƙanin uba ba uban nawa bane.
Kwaɗayin da ya kaika danne yaran mutane shi zai kaika ya baro dan Zalja tace ta yafe inan zan gayyato ta tazo ta ɗauki fansa abinda ka aikata mata.Wacece Zalja kuma?
Me na maka kake ƙoƙarin haɗani da aljana?
To idan kana so nama hukunci da kaina ko kuma na kaika kotu, kafaɗa mani shirin ku da masu ruwa da tsaki aciki.Kai asuwa da zan gaya ma su ne, kayi kaɗan ko ubanka bai isa yaja dani bare kai...
Murmushi Deedat yayi ya tashi ya nufi wata durowa ya ciro ɗan ƙaramin akwati, ya dawo gurin zaman sa, ya buɗe wuƙaƙe ne masu kama da al'makashi wani ƙarami ya ɗauka sai ƙyali yake, akwatin ya rufe ya maida gefe, sanan ya kamo ɗan ƙaramin yatsan uncle Mubarak, bai ankara ba sai ji yayi gits ya yanka masa farce.
Wata razananiyar ƙara ya saki bandeji yasa ma yatsan sanan ya ɗora masa bindiga aka yace kayi mani shiru ko na tarwatsa kanka.
Shiru yayi yana haɗiyar yawu.
Shin zaka gaya mani ko muje yatsa na gaba......
A'a Zan gaya ma amma kafin nan ya ƴata take?
Karka sake tambaya ta inda take ko ka manta inda ka barta ne?
Ka amsa Mani tambayar da nama idan ba haka ba muje yatsa nagaba, al'makashin sa ya gyara ya saita ga yatsan sa na kusa da ƙarami.......
Dakata karka yanka zan gaya ma. Tom inajin ka wanene ogan naku gaba ɗaya?
Alhaji Hassan shine ogan mu. Wane Alhaji Hassan kenan?
Wanda dai kasani shugaban mai bada tsaro na Nigeria. Jinjina kai yayi, sanan yace to amma da wa kuke waya a wata ƙasar?
Wanan malamin mu ne shike duba mana lokacin sa'ar mu. Hmmmm badai malam ba sai dai boka.Saif fa ba cikin ku yake ba?
A'a ba cikin mu yake ba, yaron Abdulkarim ne. Sashi dole yayi ko kuma akan son ransa da abun duniya yasa shi yimasa aiki? Gaskiya dole yasaka shi dan saida yasa aka kamo mahaifiyar sa sanan ya yarda da aikin amma kullum yana roƙon mu, mudaina saka shi cikin al'amarin mu, amma muka ƙi.
To me kukeyi da jira_jiran da ake ɗauko maku a cikin cikin uwayen su?
Wanan malam ne ke bamu umarnin aikata haka, da fyaɗen da mukeyi, sanan kuma da sa mata maɗigo maza kuma luwaɗi, ko wanen mu an bashi abinda zaiyi ni fyaɗe aka bani, nadaga yima mata, wasun mu kuma luwaɗi, wasu kuma ya tara mata a gaban sa suna maɗigo, duk dai an raba mana abinda zamuyi sanan bama sallah la'asar, idan muna gudun a gane sai muyi alwallah muna gamawa sai musa hannu mu shafi gaban mu to alwallah mu ta karye sai mubi mutane muyi sallah kaga kenan babu sallah mu tunda bamuda alwallah.Ɗagowa Deedat yayi idanunsa sunyi jajir akan baƙin ciki da takaici, ace musulmai, suna aikata haka duk akan duniya, tashi yayi yana haɗa hanya........
Tun da dai nagaya ma duk abinda kake so kafitar dani daga nan. Bai tanka masa ba ya rufe ɗakin yayi ficewar sa daƙyar ya kai kan sa gida saboda yanda kansa ke sara masa kwanciya yayi a rigingine, ya daɗe kwance a gurin yana saƙawa da kwance wa yama rasa wane tunani ne zai, wayar sa da tun ɗazu take faman ringin ya share da ita, itace tasake ɗaukan sabon ƙara da ƙyar ya lalubo ta ya duba wani abokin aikin sa ne, ɗagawa yayi ya kara a kunne batare da yayi magana ba.
Taɗayan ɓangaren akace hello blue eyes kana jina kuwa? Eh ina jin ka ya akayi?
Kuyi maneji Please
Don't forget to:
Comment
Share
Vote
Follow
Follow
FollowIt's Rashma
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...