*🌹🌹 DEEDAT🌹🌹*
*Writing by RASHIDA USMAN*
*Wattpad*
*rashmarrka*________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comBISIMILLAHIR '''RAHMANIR''' _RAHIM_
______________________________________
_page_ 58
______________________________________AbdulMajid da Deedat sune a gaba sai su Gwaggo, Sa'imah kuwa ta koma bayansu tana tafiya a hankali da har sun wuce ta, saida taga zasu barta a baya sosai sanan ta ɗaga ƙafa, duk da haka sun rigata shiga bakowa a falo sai tv dayake aikin sa, AbdulMajid yace kuzauna bara nayi mata magana.
Zama sukayi Gwaggo na zama tace wai Aljannar duniya kenan wanan gida haka........
Innah tace Gwaggo meye haka don Allah kiyi shiru.
Anƙi ayi shiru da bakina wallahi sai na maganta. Hararar ta Sa'imah tayi, bansan mutum na harara taba sainaga idon sa sun faɗo.......Fitowar AbdulMajid da wata dattijuwa shiya katse mata maganar da takeyi, basa ganin fuskar dattijuwar Kasancewar tana bayan Abdul, miƙewa Deedat yayi yace my mata.
Karma ka matso dan nasakeka.
Oh ni Ahmad naga takaina to ni yanzu menayi da aka sakeni?Bata kula shiba ta zauna kujerar da ke kusa da ita, kallon su Innah tayi da suma sun kafeta da idanu suna kallon ta, itako Sa'imah ta kafe da kallo tana tunanin a ina tasan mai irin wanan fuskar.
Sa'imah tsarguwa tayi da irin kallon da matar takeyi mata, yasata ɗan zamowa ta gaishe ta, numfashi ta sauke sanan ta amsa sanan ta maida kallon ta ga su Gwaggo ta fara masu magana da larabci, shiru duka sukayi, saida AbdulMajid yace mata ai basa jin larabci amma suna jin filatanci.
Da filatanci suka gaisa shiru kowa yayi, sai can ta nisa tace Abdul dawa wannan takeyima kama ta nuna Sa'imah. Shima Sa'imah ya ƙurama ido sai can yace da Khaulat take kama. A'a duba dai da kyau nidai kama takeyiman da a
Shukhra ƙanwarka. Aikuwa Hajiya amma wlh tana kama da maman ku Khaulat..........Gwaggo ta katse masu zance da cewa wai me kuke cewa ne?
Murmushi Abdul yayi sanan ya mata bayanin abinda suke cewa.Oh ai Sa'imatu kamar su ɗaya da marigayi ya mamar mu dan babu abinda ya raba su........
Bata ƙarasa ba taga wani hoto miƙewa tayi tsaye hanunta na karkarwa tana nuna hoton dake jikin bango, kwallah ta cika mata ido ta ciro hoton ta riƙe ta ƙura masa ido, gaba ɗaya ɗakin kallonta sukeyi barin ma ƴar dattijuwar nan, ganin hawaye sun wanke mata fuska yasaka Deedat tashi ya ƙarasa gurinta yace Gwaggo meyafaru?
Fuska ta share ta ciro hoton ta nuna masa tace wanan hoton mu ne da muka ɗauka gaba ɗayan mu, kallon ta, tamaida ga dattijuwar tace dan Allah a ina kika sami wanan hoton?
Iyaye nane da yayena. Bakinta na rawa tace kardai kice man kece Sa'imah..........
Eh nice Sa'imah kin sanmu ne?
Ba shiri Gwaggo ta ƙaraso gurinta ta ɗaya ta rungume tace nice yayar ki Halima. Ai bashiri ta fito daga jikinta ta sake komawa ta ƙan ƙameta ta saki wani irin kuka, sun ɗauki lokaci a haka ba wanda ya katse su saida suka gaji sanan suka zauna rungume da juna saida suka nutsu sanan Deedat yayi gyaran murya, waigowa sukayi a tare suka kalle shi, yace wai kun manta damu ne?
Gwaggo ce tabashi amsa da cewa haba jan ƙosai mun isa mu manta dakai.
Bata bari yayi magana ba ta fara nunawa Hajiya Sa'imah su Innah tana mata bayanin su, sanan ta nuna mata Anas ɗanta.
YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...