🌹🌹DEEDAT🌹🌹 Wattpad Rashmarrka Writing by (maman khady) Page 6 Adai 2 lokaci

2.4K 144 3
                                    

🌹🌹DEEDAT🌹🌹
Wattpad
Rashmarrka
Writing by (maman khady)
Page 6
Adai 2 lokacin da suka karaso gidan hajiya karima  Horn driver yayi mai gadi yabude masu get masha Allah balaifi gidan yanada kyau gurin aje motoci yanufa yayi  parking fitowa sukayi SA IMAH sai kale kale takeyi wace tun lokacin da suka shigo kano take Kale kale ranta yayi matafari fes tashigo birni burin ta yaciki tashigo birni da take  mafarki part biyu ne agidan dayan bangaren suka nufa ba laifi babban falo ne da sallama suka shi babah mai aikin hajiya ce amsa masu tayi tare dayi masu sannu da zuwa bata jira amsawar suba ta koma ta nufi kichin ta hadomasu ruwa da drink ta ajiye takoma gurin aikin abicin rana datake hadawa hajiya ta kwallawa babah kira da sauri ta karaso tanacewa hajiya gani tace inah sauran masu aiki babah tace suna dakinsu hajiya tace je ki kiraminsu babah ta amsa da to tafice Sarah yar hajiya tafito daga ita sai kayan bacci iya kacinta sa ar SA IMAH dan itama bazata wuce 14 to 15 years ba gurin mamynta ta nufa dan bata lura da su SA IMAH ba hugging dinta tayi tanacewa mamy harkin dawo itama hjy karima da murna ta amsa mata tanacewa auta me yahana maki zuwa school yau yamutse fuska tayi tace mamy banda lfy ne hjy tace ayya auta Allah yabaki lfy tace amin mamy tace bakiga bakiba bazaki gaishesuba dasauri tajuya dan har ga Allah bata gansuba taduka harkasa ta gaida innah amsawa innah tayi tana murmushi dan wanan soyayyar tasu ta burgeta gurin SA IMAH ta nufa ta shafo fuskarta tanacewa wow mamy inah sonta murmushi SA IMAH tayi gefe kumatunta ya lotsa dasauri Sarah tasa hannuta gurin dan ramin sai murna takeyi tasamu kawar fira masu aikine suka shigo kusan su 4 gaisheda hajiya sukayi sanamata ya hanya ta amsa da lfy tabasu umarni  kuje Ku gyaramin dayan sashen can atare suka amsa da to hajiya kallon Sarah tayi tace kutafi dakinki tayi wanka jan SA IMAH tayi suka nufi dankita sunatafiya hajiya takalli innah wuro tace mata muje nawa kiyi wanka kafin sugama gyara inda zakuzauna tashi hajiya karima tayi ta nufi saman bene innah nabayanta aranta cewa takeyi yan gayu sun huta adai 2 lokacin da suka karaso cikin dakin aibaki innah tayi tana kallon tsaruwar dakin aranta tace masha Allah 
SARAH sai surutu takeyiwa SA IMAH dama ita batada yawan magana saidai akwai barna da rashin ji  amma ko a rugarsu bata da yawan magana tafiso takoma gefe tayita wakarta  Sarah tanunamata toilet shiga sukayi ta nuna mata yanda zatayi amfani dasu godiya tayi mata Sarah tafita itakuma SA IMAH yatsaya karema bandakin kallo saida tagama tabe 2 ta sanan tafito koda tafito Sarah tafitomata da wani riga da wando na Jens  SA IMAH tace tab wazaisa Riga da wando saikace yar iska Sarah dariya tayi tace dallah kisa kisha iska saida tamatsawa SA IMAH tasaka kayan  dan kwalin kayan da tacire tadauka zata daura Sarah tace wait wait mezakiyi SA IMAH ta bata amsa da daurawa zanyi batace mata komaiba ta dauko mata hula kalar kayan karba tayi tasaka fitowa sukayi falon koda suka fito sunsamu su innah har sunfito gurinsu suka karasa
****
suna isah gidan Horn saif yayi get man yabudemusu shiga da motar sukayi babban gida ne saikace wani gari  ababban falon gidan suka yada zango DEEDAT yace inah jinka saif yayi gyaran murya yace alhj bala yanada hannu a kidnapping din dake adabar kasar nan sanan company dinsa na magunguna ya hada kai shuwaga banin Australia Ana gurbataccin magunguna sanan suna sayarda maganin da kwanan watansu  suka kare sanan yana  deban yan mata dasunan basu aikin yi ya maidasu karuwai yaturasu kasashen waje  ajiyar zuciya DEEDAT yayi sanan ya furzar da iska mai zafi yace ahaka kuma yake Neman shugaban kasa yayi wani murmushin mugunta  yace zaka shigo hanuna very soon yace tunda kashiga gonata wlh sai nayi kaca kaca da harkalarka babu Wanda ya isa yataba min mahaifina ya kwana lfy yajuwu yakalli  saif yace masa inah binciken da nasaka kayi min abunda ya hadashi da papa har yake ikirarin sai yaga bayan papa ajiyar zuciya saif yayi sanan yace mun tatauna da P A dinsa yabani lbr abunda ya hadasu lumshe below eyes dinshi yayi da suka koma ja akan bacin rai yace inah jinka saif yanisa sanan yace yanemi papa ne domin yasa masa hannu   akan kwangilar da ya amsa ahannun shuwagabanin Australia  zai kwashe masu shrar asibiti kuma sharar tanada hadari sosai dan ta kunshi sasan jin dan Adam da magungunan da kwanan watasu suka kare shine yakecema papa idan suka kwaso sharar zasu cire magungunan arika sayar ma da al ummah shine papa yaki amicewa  yace Sam baiyardaba dan duk Abunda zai shigo Nigeria saida sa hanun papa  to shine kaji yanacewa babu Wanda zaiji sirrinshi ya kwana duniya shine yakecewa sai yaga bayan papa DEEDAT yajinjiana kansa yace baisan dawa yake kokarin karawa dashiba dan mai ganin bayan papa sai Allah saif yamika masa wani memory card yace duk bayanan suna cikin nan karba yayi yace muje kakaini office din mahaukacin kare nan murmushi saif yayi yanacewa zakina kenan nasan indai case yashigo hanunka baka yimasa da wasa balle antabo papa DEEDAT baice masa komaiba Yakama hanyar fita saif yana bayansa motar suka shiga basu tsaya tsaya ko inah ba sai office din Alhj bala iso sakatariyar sa tayi musu DEEDAT kadai yashi danshi saif yace yashiga shikadai dan karyagane akwai wani Abu  yana shiga saida gaban Alhj bala yafadi yatsorata da ganinshi amma tuni ya wayance dacewa my son kaine yau office dina acikin ranshi kuwa cewa yake mai yakawo wanan dan iskan yaron gurina dan nasan zuwansa ba alkhairi bane  muryar DEEDAT ce takatse masa tunani da yake cewa ko baka ji dadin ziyara ta bane inkoma kasa magana Alhj bala yayi murmushi DEEDAT yayi aransa kuwa cewa yake ashekai karamin kwaro ne daga ganina har ka tsorata hmm nibada kai zanyi takon sakaba da manya ka zanyi  Alhj bala yace akwai wani abune murmushin mugunta yayi sanan yace a a nazone nagaidaka yatashi yace nizan tafi Alhj bala yace to sai mun sake haduwa juyuwa DEEDAT yayi yacemasa karkayi fatan haduwar mu domin bazatayi ma kyauba yace inbanda abinka Alhj bala ai bakin rijiya bagurin wasan makaho bane haka zalika sama tayiwa yaro nisa sadai yatada kai yayikallo yajuya yacigaba da tafiyarsa ta kasaita saida yakai bakin kofa ya juwu yayi murmushi yana shafa sajensa sanan yace abokina sai mun sake haduwa yafita ya banko kofar dafe kai Alhj bala yayi yace lalai yaro nan ya rainani wainine abokinshi zan daki mataki tunkafin lokaci yakure min dole ma oga yasan abunda ake ciki
****
Hajiya tace kutashi muci abinci yunwa nakeji gaba daya tashi sukayi suka nufi darning Aeria Sarah ce ta tashi tafara saven dinsu kowanne yafara cin abinci aran innah kuwa mamaki takeyi wai cin abincima harda guri gareshi batajin dadin cin abinci asama amma hakanan tafara ci wani irin dadi taji tace kai yan birni sunji dadin su  SA IMAH kuwa har wani lumshe idanu takeyi suna  gama cin abinci hajiya tace sutaso tanuna masu inda zasu zauna tashi sukayi sukabi bayan ta bangaren babban dantane yayan ta ukku namiji daya mace biyu Aliyu ne babba sai habiba sai saratu auta amma sunacemata Sarah Aliyu yanada mata matar batada mutunci ko kadan ta mallakeshi ta rabashi da mahaifiyarshi da yan uwansa sai abunda tace yakeyi ita kuma habiba tana auren wani dan kasuwa yanada kudi sosai amma uwar mijin bata bari aci kullum sune cin fara da mai da yaji ko kuma dan wake bata bari adafa abinci kirki wanan kenan
Babban falone sai dakuna biyu da kichin kowane daki da toilet dinshi duk akwai kaya aciki innah wuro tashiga yima hajiya godiya hajiya karima tace babu komai tace kushiga kuhuta driver zai kawo maku kayanku godiya suka kara yaimata fita tayi dan sarah tuni tafice dan batayi wanka ba  SA IMAH tace innah idan mun huta zamu nemi gidan da zamu kama haya dan naji tabawa tace akwai gidajen haya innah tace tunani na kenan zuwa gobe sai muyiwa hajiya magana daki daya suka shiga dan surage gajiya bacin wahala yayi gaba dasu dan basu saba irin wanan tafiyaba
****
Yana fitowa yasamu saif zaune abayan mota dirowa yayi yashiga motar yaja saif yace inah muka nufa batare da yakalle shiba yace mukoma inda muka fito gidanshi suka nufa a bakin get ya ajiyeshi yace idan nagama zankiraka bai jira saif ya amsa ba yashiga gidan yashiga wani daki yashi ga kafet dindake kasa ya yaye sanan wani dan karamin Gila's yabayana wasu numbobi ya daddana saiga gurin ya bude mattakala yahau yashiga daikin yaja amarfin kofar ya rufe wutar dakin yakunnah bakomai adakin wani Abu yataba   gabadaya bangon dakin yadauki hasake hmmm aiki yafara da computer din cike da kwarewa gabadaya dakin na urorine duk ya hada zufa yana bincike abunda ya shafi Alhj bala da wada ke tare dashi daker da temakon memory card dinda saif yabashi yasha mamaki ganin kanin mahaifinshi wato baban jiddah da turawa biyu sai minister man fetur dariya yayi yace haba biri yayi kama da mutum shiyasa ya turo ma haukaciyar yarsa gidan mu  ajiyar zuciya yayi yace kuafara kuka tun yanzu kafin nakarso rufi komai yayi yafito yanufi falo yadaga wayar sa yakira yace zoka mayardani gida

More comment

DEEDATWhere stories live. Discover now