page 54

1.9K 122 1
                                    

🌹🌹 DEEDAT🌹🌹

Writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

My Mariya umar musa wanan shafin nakine kyauta kiyi yanda kike so dashi my best friend I really love you, Allah ya raya mana yaran mu.

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

PAGE 54

Anas kaine.......
Bata ƙarasa ba ta tafi luuuuu zata faɗi da zafin nama Deedat ya riƙo ta ta faɗo jikin sa a sume.

Da gudu  ya ƙara so gurin yana kiran sunan ta yana jijiga ta, umma kitashi mana umma.

AbdulMajid ne yayi saurin nufar firij ya ɗauko ruwa ya shafa mata a fuska, ajiyar zuciya ta sauke ta fara bin mutanen dake gurin da kallo, akan fuskar Anas ta sauke idanun ta ƙure tayi da kallo sanan ta kai hannu ta shafi fuskar sa, auta na kaine ko mafarkin da nasaba ne?

Murmushi mai haɗe da kuka yayi yace umma nine ba mafarki kike ba nine Anas ɗinki autan ki.

Rungume sa tayi tana sakin kukan farin ciki, ayya yarona na ɗauka sun kashe mani kai.
Hawaye yake share mata yace a'a ban mutu ba amma ai naga sun harbe ki.

Eh dogon suma nayi, daga nan tabashi labarin yanda akayi tasamu lafiya.
Shima labari ya bata yanda ya kasance.

Duk cikin su Deedat ba wanda ya katse su saida sukayi mai isarsu sanan sukayi shiru, ba abinda Iya keyi sai sharar hawaye ba ƙaramin tausayi suka bata ba.

Deedat yayi gyaran murya sanan yace zaka gane gidan da ka zauna a yola?

Eh ranka ya daɗe kodaga bacci na tashi zan gane gidan.
To badamuwa zan saka lokaci sai muje.

Cikin jin daɗin ya dinga yi masa godiya.
Hannu kawai ya ɗaga masa ya tashi ya nufi ɗakin sa duk ransa a jagule, yana kuma mai jin idan har bai hukunta waɗannan mutanen ba to bazai taɓa samun nutsuwa a rayuwar  sa ba, ace duk waɗannan zunuban da suke aikatawa duk dan neman duniya ne, iska ya fitar mai zafi sanan ya tashi ya shiga banɗaki ya sakar ma kansa shawa tana jiƙa shi, idon sa a rufe duk ransa a dagule.

Sai gurin biyar su Innah suka dawo abakin get ɗin su Deedat tace Ibrahim ya sauke ta ita kuma Sa'imah cewa tayi bazata shiga ba, tabi Ibrahim suka wuce gida.

A falo ta samesu har Deedat ya fito suna ta zuba fira Gwaggo da ka kalle ta kasan tana cikin farin ciki, gaishe ta sukayi ta amsa da fara'a, sanan ta gaida Iya, yarona inah su Ammah?

Sunje gidan Mamy daga nan suka ce zasuje gidan su umma.

Ok banko haɗu dasu ba koda yake ni ana kai lefen natafi wani guri, to Hajiya Gwaggo mai maza larabawa da hausawa harda fulani, kitashi mutafi ko.

Ɗankwali ta turo gaba ta cewa kin manta da jan ƙosai.

Kai Deedat ya dafa yace nidai na shiga tara wai me zan maki kidaina cemani jan ƙosai......

Bata kula shiba ta kalli Iya tace ƙawata sai gobe idan nadawo.
To Allah ya kaimu.
Autana ga Adda A'isha baka gane taba ko?

Innah tace ban gane ba naji kince autan ki.
Zaki gane muje gida na miki bayani.
To muje, sallama sukayi ma su Iya, har Anas binsu yayi, Deedat yace yadai kabi Gwaggo bamuyi abinda ya kawo ka ba.

Sorry oga amin afuwa zuwa anjima idan muyi sallah magariba sai muyi magana.

To shikenan ba damuwa.

Koda sukaje gida Sa'imah na baje a kujera tana nishi wai ta gaji, Gwaggo na ganinta tace ragguwar banza me kike ma nishi ɗaya bayan ɗaya kamar mai na ƙuda.
Baki ta murguɗa mata haɗe da fari da ido.
Iyye ni hali dubu ni kikema haka. Innah tace nidai Gwaggo gaya mani waye wanan kafin kuci gaba daga inda kuka tsaya.

DEEDATWhere stories live. Discover now