*🤦♀KADDARAR MACE🤦♀*
*NA*
*NA'EEMERH SULAIMAN*~nimcy luv~
Face book
~nimcy luv page~
Wattpad
~nimcyl~
Kaddarar mace group chat2⃣1⃣
*~Bani da burin bata muku rai my fans amma gsky zamu fara batawa daku akan comments din da baifi 2minute ka rubutashi ba kusani comments shine yake bamu karfin gwiwwa kuma wlh daka yau duk group din da basuyimin comments ba bazan kara turo mus novel dinava~*
✨✨✨✨✨✨✨
Dr Abdallah yayi saurin runtse idonsa yana tasbihi ga Allah yakasa ko motsi sbd rikon da tayimai ya bude idonsa ahankali ya zubawa jannat idonsa da ya koma ja soyyayar yarinyar kullum kara yawa take a zochiyyar kullum addu'a yake akan Allah ya cire masa sonta amma ina kullum karowa yake....Asalin dr Abdallah haifaffan garin makkane shi dayane tilo wajan iyyansa anisha itace mahaifiyyarsa sai kuma mahaifinsa ibraham Abdallah tun yana dan shekara biyar cim ya haddace alkur,ani mai girma ana alfahari da abdallah sbd kwazonsa idan yana mgn da turanci saika rantse rainon England ne hakama labarafci karatune ya kawo Abdallah Nigeria yasamu yabu da kuma nasarori da dama wajan mutane iyyansa sunyi sunyi ya dawo makka ya cigaba da aikinsa anan sannan a aura masa madiha wacce take bala'in sonsa amma yaki yace Nigeria tafimai zaina zuwa yana dubasu yanzo haka yana Aminu Kano teaching hospital da aiki abdallah farine sosai mai cikar zati dugune yana da dan kauri ga kasunba a gefen fuskarsa abdallah Sam baya son yawan mgn koda yaushe akwai murmushi akan fuskarsa wannan shine Abdallah ibraham Makkah....
Kokawa aka shigayi tsakanin jannat da anwar da tabbatar saiyayi mata allurar ta dage ta fasa uwar kara tare da kankame Abdallah hawaye majina suka taro waje daya fuskarta tayi jajawur duk ta fita haiyyacinta duk abinda take bai fasa yimata allurar ba yana yimata allurar ta zube akasa sumammiyya sbd sabar ranaza....
Ohh ni anwar wannan wacce irin mata Allah ya bani mai shegen tsuran allurar nan ya dauketa cak yasaka a kan bed din joyowa yayi yaga babu kowa a dakin saishi da jannat murmushi kawai yayi ya dauko ruwa mai sanyi ya shafa mata a fuska...
Tana zaune ita kadai a palour tayi ta gomi tana tunanin makomar rayuwarta tabbas idan tara sashi kamar ta rasa rayuwar tane wajan wa zata ta fadamai damuwarta wata zochiyar tata tace "ki fadawa mumy bakida kamarta itace mai sonki batason bakin cikinki dole zataso abinda kikeso tayi murmushin jin dadi ahankali ta tashi ta nufi bedroom din mumy...
Tura kofar dakin tayi tasamu mumy akwance akan bed tayi sallama ta shiga dakin ta zauna kusa da mumyn tata..
Ta kalleta tace daughter lpa dai?.
Kasa daurewa tayi tasaki kuka mai cin rai kuka take sosai hade da cewa " mumy na shiga uku xochiyata ta kusa fashewa akan son anwar mumy kin kusa rasani idan har narasa yaya anwar ta kara fada tana kankame mumy nan take kuma maimu ta fara tari har jini yana fitowa...
Ajjiyar xochiya tasaki jin ruwa mai sanyi a jikinta kana ta bude idonta ahankali anwar ta gani zaune kusa da ita yana tayi mata dry nanfa ta sauya fuska ta daman mai jiran kadan ganin yadda tayi da fuska yasan zata iyya kukan nata dan haka yace "beby ayimin afuwa nasan nayi laifi amma kinsan rayuwarki da lafiyyarki da kwanciyyar hankalinki yafimin komai nima da san raina nayi maki ba ayi hakuri gimbiyya ya fada yana rike gunne"..
Dry ta saki dan bazata iyya fushi da yayan nataba babu zato yaji ta kwaramai ruwan sanyin akansa nanfa jannat ta fara dry hard rike ciki hannu yakai zan cafko ta zillah hakanan ya hkr ya zuba mata idanu shikadai yasan meya keji game da ita da kyar ya bude baki yace " beby zonan kiji wata mgna mai dadi"
Makale ka fada tayi alamar bazatazo ba..
Lumshe ido yayi ahankali kana ya budeso tar akanta yace "beby jannat zaki kasheni da sonki wlh"
Da sauri ta nufeshi tace rifamin asiri waceni da zanyi kisa"..
Hannunta ya damka yace "wana kama"
Zaro idanu tayi hade da dafa kirji tace "bani ba"
Yadda tayi mgnar yabashi dry Dan haka yasa hannu ya lakace hancinta yace "matsuraciyya kawai ya fada tare da zura hannunsa a aljihu ya Ciro wani farin zobe na gwal karamine mai dan karamin dutse a tsakiyya iyyakar kyau zoben yyi kudi kowa basai kayi mgnaba yace " beby ban hanunki mugani"
Babu musu ta miga masa hannun ta ya dauko zoben ya durkusa a gabanta tare da riko hanunta yace"will u marriage me jannat Abbakar rano ya fada yana lankwabe kai abin tausayi..
Kasa mgna tayi sbd
Farin ciki saita Shiga daga masa kanta hade dayin hawaye Wanda ta kasa gane na farin cikine ko bakin ciki haka ya zura mata zoben a hannunta sai shegi yakeyi...Sosai takeyin tarin jinin wanda yasa mumy rikece "no daughter pls kedaya nakeda ke kina tunanin zan zuba ido rayuwarki ta lalace nayimi miki alkwarin dole ki auri anwar dan haka ki kwantar da hankalinki..
Dry tashigayi tana rungunme mumy tace " u are the best mumy"
Dr Abdallah joyi kawai yake akan bed dinsa yarasa meke da munsa Ashe ya rinyar da yake matuwarsu itace wacce amininsa keso shikam yaga ta Kansa meke shirin faruwa da shine wannan wanne irin sone haka da yaga tunanin bazai kaimaiba ya tashi ya dauro alwala ya fara gabatar da lafila bbu adadi yana rogan Allah akan zabin ubangiji....
Zaune suke a palour su biyu "yaya ni aganina abar aurannan next week idan Allah ya kaimu"
Alhj Abbakar yace shikenan daddyn anwar Allah ya kaimu next week din amma bana son ka wahalar da kanka nizanyi komai na maganar auran sadaki shine kadai naka"
Daddyn anwar zaiyi mgna amma ya kasa sbd kwarjinin da Yayan nasa yayi masa shiyasa ake cewa anwar shiyayo shida ashman ya bude baki yace "to yaya Allah ya saka da alkairi su koma Allah ya tabbatar da farin ciki a cikin auransu"
Daddy yace ameen sai kaje ka fara shiri tundaka yanzo..
MAFARIN KADDARAR......
Tana kwance akan sofa ta dakin mumy dan yanzo bata kwana a dakinta sbd oga anwar cewar mumy a fara yi mata gyaran jiki mazai kara ganin taba saida biki..
Karasuwa tayi ta zaune hade da cewa amarya ba kya laifi ko kin kashe Dan masu gida..
Ashe!! bandai kashe dinba da kinga yadda ake kwallo da amarya cewar jannat"
Maimu tayi murmushi tace "af wayanki fa zaki aramun na kira friends dinmu na gaya masu bikin naki dan tawa babu kudi..
Wlh kamar kinsan dazo my man yasamin kudi a wayar ta fada tana miga mata wayar tace bari naje gun mummy yanzo zan dawo..Maimu ta bita da kallon banza a zochiyyarta tana cewa wani Abu sauri tayi ta dau wayar ta shiga xender ta turo picture din anwar wajan kala 10 saikuma ta turo na anwar da jannat subiyu daka nan tashiga contact ta dau number anwar din tana murmushin cin nasara...
~vote~
~comments~
~shere~
*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

YOU ARE READING
KADDARAR MACE
Short StoryJannat da maimuna kawayene tun suna yara anwar shine dan uwan Jannat kuma saurayinta haka maimuna tashiga wajan malamai dan raba tsakaninsu