ƙaddarar mace 40 by nimcy luv

293 11 2
                                    

*🤦‍♀KADDARAR MACE🤦‍♀*

           ~by~
    ~nimcy luv~

            
            4⃣0⃣


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

@wattapad
    Nimcyl
08119237616

  

       *do the best and be the best✌*

✨✨✨✨✨✨✨

Cigaba yayi da kallonsu, yayinda zuciyyarsa taci gaba da bugawa, yasan cewa madiha na Singapore, amma baiyi tunanin zasuyi kusa da juna ita da bebynsa ba, nutsuwarsa ya saita kana yayi murmushi yace dasu.

   " 'yan kauye kawai kunzu kun zubamun ido daka zuwana an rasa Wanda zaiyimin oyoyo a cikinku kamar baku sanni ba ya fada yana dallah masu harara"

Madiha ce tayi murmushi dan tunaninta wajan yazo, tunda baisan Jannat ba,  da sauri ta karasu wajansa shima bai nuna wata alama ba,amma yasu Jannat ce ya farajin dumin jikinta, tana karasuwa ta fada jikinsa tasaki kuka hannunsa yasa yana bubbuga bayanta amma bai rungumeta ba, itama Jannat kukan ta farayi kasa-kasa dan hakan ya tuna mata da farin cikinta kuma jigwan rayuwarta ganin Abdallah na shirin kamata tana kuka yasa ta joya baya ta gyara fuskarta ta kakaro murmushi ta kalleso inda haryau madiha tana makale jikinsa taki sakinsa gyara murya tayi sannan tace "barka da zuwa bakwanmu, ya hanya ta tambayeshi inda take kallon wani wajan daban"

  Basarwa yayi dan kar madiha ta gane komai ya kalli Jannat yace "lpa Allahamdulliah enmata"

  Bata kara magana ta huce bedroom dinta ta barso anan dan tagaji sosai ga kuma yadda zuciyyarta keyi mata kunci da ciwo ga bata da magani tana shiga ta samu ruwa faro mai sanyi ta bude tasha kusan fin rabi sannan ta ajiyye, kayan jikinta ta cire ta shiga toilet tayi wanka a gurgoje, sannan ta nemi riga mara nauyi ta saka iya gwiwwa ta gyara gashin kanta ta daure da ribbon ta feshe jikinta da turare da yake ta riga tayi sallarta yasa ta haye saman bed dinta taja baleket ta rufe jikinta sai bacci dan tana bukatar nutsuwa a zuciyyarta.

  Janyeta yayi daka jikinsa ya samu waje saman sofa ya zauna yana lumshe idanu shikadai yasan abinda da yakeji gameda Jannat yasani a wannan lokacin tana bukatar tai makwansa dan yaga sanda take kuka ga kuma madiha wacce bama dan ita yazo Singapore ba ya salam what should i do now, let me make her busy kallon madiha yayi yace .

  "Zonan sister"

  Babu musu tazo ta zauna kusa dashi ta zuba masa idanu sannan tace.

   "Gani nurul hayat"

Yauwa sister pls inajin yunwane inason kiyimin fatan duya da hadin fruits idan babu damuwa"

  "La ai yazamemin dole koda duniyyar kace na daukoma zan iya daukoma bare kuma abinci ta mike tayi mai light kiss sannan tayi kichin dan sama mai abinda ya bukata murmushi kawai yayi ya kwanta saman sofa kafin ta fara aikin 5minutes yasan tashi ga busy sosai dan haka ya tashi a hankali yayi bedroom din Jannat yana zuwa ya murda kofar yajita alamar a rufe ansa mata key juyowa yayi dan karya buga madiha taji kwaciyayi sosai a kan carpet yana kallon sama yayi da yakeji babu dadi cikin zuciyyar sa Abdallah kenan.

A dayan bangaran waya take tayi amma anki picking gaba daya ta fita haiyyacinta dan masifar ta taso mata kara kira tayi harta kusa tsinkewa sai taji andaga ko gaisawa basuyi ba ta fara mgn.

   " haba muhuseen tun dazo ina kira but you didn't pick my call why? "

Dry yayi kadan kamar bayaso sannan yace.

  "Dunda kikajini shuru aikinsan ba lafia ba, wlh 2days banajin dadi zazzabi na damuna, amma ki bari zuwa jibi zamu hado".

  Dan karamin tsaki taja dan ta fara gazawa tace.

  " Malam banason dugwan bayani, kawai kana ina yanzo zanzo".

  Uhm aa kiyi hkr zuwa jibin, ina mijinki? meye amfaninsa kije gunsa mana"

  Niba dugwan zance nace kayimin ba kaga sai anjima da kashe wayar gaba daya tana juyi saman bed dinta tashi tayi ta nufi 6angaran anwar tana shiga ta ganshi ya fito cikin shiga ta alfarma  tsayawa tayi tana kallonsa dan bakaramin kwarjini yayi mata ba bakin buyal ne ajikinsa yasaka hula fara mai zanan baki sai a gogu da takalmi duk farare zai zuba kamshi yake sumar kannan tasha gyara sai kyalli take kallonta tayi kamar zai mgna sai kuma ya basar dan anwar badai shariya ba matsuwa tayi ta fada jikinsa tana kuka bai cemata komai ba kawaidai ya zuba mata idanu saida tagaji sannan tace"

  "Pls hubby ka taimakeni ina cikin wani hali, dan Allah karkasa rayuwata tayimin ba daidai ba, karka manta ni matarka ce ta sunna"

Janyeta yayi ajikinsa ya kalleta sosai still baice komai ba kuma bashi da alamun mgana, hannu yasa ya goge mata hawayen, sannan ya daga 'yan ya tsunsa guda biyar alamun ta jirashi zuwa 5minutes murmushi tayi sannan ta kara rungomeshi uhm hajiya maimuna kenan.

  Ta gama jera komai akan carpet dan Abdallah bayacin abinci a darning saida anisha wanka tayi ta sauya kayan jikinta ta dawo parlour Jannat inda taga Abdallah shima ya sauya kaya jikinsa alamun yayi wanka kenan  da murmushi a fuskarta ta karasu wajansa tace.

  "Barka da zaman jira nurul hayat, bisimillah ga abinci?"

Uhm daman haka ake kin bar 'yar mutane tun dazo a daki a kulle har kina shirin cin abinci babu ita sauri tayi ta tashi tana cewa"

  "Kai beby bakya rabu da damuwa wallahi, mutum yaje daki ya zauna shi daya na hanaki bakiji ba, gaban Abdallah ne ya fadi jin abinda madiha ta fada wato kullum cikin damuwa take gsky rayuwar Jannat abar dubawace gashi haryau family su babu Wanda yasan tana da ciwon zuciya gashi yana tsoran gaya masu ya salam ya fada yana runtsa idonsa motsi yaji a bayansa yana dubawa ya gansu sun fito tare haryau shirgar dazone ajikinta kanta ko dan kwali babu zame hannunta tayi taje da hado milk mai sanyi ta shanye tas duk gaban Abdallah kana ta dawo saman sofa ta kwanta tana maida numfashi dan wani irin ciwo takeji a zuciyarta nantake girjinta ya fara dagawa ahankali hannu tasa ta danne saitin zuciyarta madiha ce ta kalleta tace.

  " beby taso muci abinci, tun dazo ke muke jira nida nurul hayat pls"

Still idonta a rufe yake,tayi murmushin karfin hali tace.

   "No! Madiha kuci kawai banci ngd"

  Girgiza kansa yayi kana ya dau spoon din zaikai bakinsa kenan sai yaga Jannat ta fara mikewa jikinta gaba daya ya dauki rawa nan take ta fara tari sosai saiga jini ya fara zuba ta cikin bakinta har lokacin tana rike da saitin zuciyarta da gudu Abdallah yayi kanta gaba daya yama manta da wata madiha a rikice yake cewa.

  "Pls ruhina Karkiyimin haka Idan kika muto nima mutuwa xanyi kece rayuwata kece komai nawa ya fada yayin daya kankameta ajikinsa gaba daya duk karfin rokwan da yayi mata mai hana jikinta karkarwa ba tana wata irin fisga da gyar ta bude baki tace.

  " Abdallah rayuwa bata da amfani a wajena tabbas mutuwa itace hutu a gareni farin ciki jin dadi abokin rayuwa duk sunyimi nisa Wanda nake tunanin zai bani farin cikin a yanzo wani dalili yasa bazan sameshi ba kaga dole na bukaci mutuwa wata irin shakuwa tayi hade da kankame Abdallah sai kuma bugun numfashinta ya tsaya ya salam Jannat kenan.

  Da sassarfa ya shigo part din su abban Jannat a parlour ya samesu da Abba sai mama sai kanwarsa meera da yayan Jannat faisal mijin meera ne tun kafin ya karasu suka zubamai idanu yayin da shikuma ya tsaya cak yana kallon wani wajan kallon wajan sukayi Ashe picture din Jannat yake kallo Wanda yake manne a parlour tana dry dukkan dimples dinta sun luma wani jiri ya faraji yana dibansa ji sukayi ya ambaci sunan jannat da karfi sai kuma ya sulale a wajan a sume babu numfashi.........






   💃💃💃💃💃ahhyeee wata tafi wata a hankali wata tafi wata a comments wata tafi wata💃💃💃💃











NA,EEMERH SULAIMAN🤕

KADDARAR MACEWhere stories live. Discover now