KADDARAR MACE PART 14

340 12 0
                                    

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*🤦‍♀KADDARRA MACE🤦‍♀*

           *NA*

*NA'EEMER SULAIMAN*



           Page 1⃣4⃣


Wattpad
Nimcyl
Face book
Nimcy luv page
07051284590
Sulaimannieemerh@gmail.com

   _This page i  dedicated it to my lovely sisters ikilima and lawiyysat and my special friend bride to be ummey ameenu❤💃💃💃much luv to you_

*📲typing*



      Zaro ido waje tayi jin abinda yake mata ta dago kai ta kafeshi da idonta murmushi yayi yasa tafin hannunsa ya rife mata ido shima ya lumshe idonsa yaci gaba da abinda yake...

       Sunkai 10 minute ahaka kana ya saketa ya cigaba da kallonta sannan yace "wannan shine cikar kauna my heartbeat ya karasa fada yana kanne mata ido daya😉"

     Murmushi tayi tadan daki kirjinsa tace "ni Allah banso"

      Yayi dariya sosai kana ya kwaikwayi voice nata yace "to ni koma inaso sai yaya"  

Nan fa ta shagwabe fuska zatayi kuka😢

    Ah oh ni 'yarsu kekam kuka bayayi maki woya tom shikenan ban karawa ya fada yana rike kunnansa"

   Dariya tayi tace "babu komai an yafema tun kafin kayi laifin"

   Tnx alot rabin raina au namanta ban gaya maki ba

   Tayi saurin cewa
mefa

    Uhm meye na saurin tambaya kuma daman gobe zan koma Singapore ne shiyasa naxo muyi sallama nabar komai wajan Daddy kafin na dawo za'asa ranar auranmu ina dawowa sai ayi biki.....
   
      Dan bata rai tayi tace "wai wannan komawar dolene wallahi bansan rabuwa dakai jinake idan katafi kamar bazamu kara samun farin cikiba pls rabin raina karka tafi ta fada tana dora kanta a cinyarsa"

      Shuru yayi dan yasan daman dole sai tayi wannan rigimar kallanta yayi yace "ah haba dai mekike cewa haka koma pls kidaina banso kuma banda abinki meye amfanin wayar dana siya maki zamuyi waya sannan zan bude maki WhatsApp zamuna magana karkisa damuwa aranki babu mai rabamu sai wani ikon allah.....
   
     Murmushi tayi dan taji dadin maganarsa kana tace " allah ubangiji ya kaika lafiya cikin yarda da aminci yabaka ikon yin abinda katafi yi"

   ameen ya allah nagode sosai allah yayi maki albarka ya kareminke daka idon makiyya......"

      Ameen tace kana tace "karife idonka da ganin matan Singapore banson ko wacce mace ta kalleminkai"

     Habawa ina dake wazan kallah yanxo dai tashi kije ki kwanta kinga dare yayi nima 7:30 zabar gida kinji ko

    Mikewa tsaye tayi tace "good night ta karasa fada tana kissing kumatunsa"

  Owk night rabin raina i luv you
 
  I know tace tana shigewa bedroom dinta

  Dariya yayi yana fice daka part din......

      Wanka tayi ta shafa lotion kana ta fesa turare ta shin fida abin sallah ta fara sallah ta dade tana addu'oi sannan ta tashi tasaka kayan bacci ta kwanta..

    Awani jeji suke suna kallon juna ta kalleshi tace "wai meke farowa dakai naga dukka canzamin "

     Bakomai kawai yace yana karayin gaba

    Cigaba tayi da biyoshi amma abin mamakin idan ta taho sai taga yayi mata nisa kiransa ta farayi tana kuka amma ina sam bayajinta haka taita kiransa har yabace da ganinta...

      Farkawa tayi tana salati hade dayin duk addu'ar datazo bakinta tana tunanin mafarkin da tayi sannu ahankali taji jikinta ya fara sanyi kirjinta yana dagawa zochiyarta na bugawa ahankali idonta ya fara rifewa ..

  Tun asuba ya tashi haka kawai yaji gabansa na fadowa harya gama shirinsa tsaf yana ta addu'a a zociyyarsa har 7:00 tayi sannan ya tashi ya Shiga bangaran mummynsa yayi mata sallama sannan ya koma wajan daddy shima yayi masa sallama.....

     tura kofar dakin yayi ahankali ya rife kofar ruf kana ya joyo ya kalleta yana tunani a zochiyarsa yana cewa "wannan wacce irin kwanciyya tayi da alama batai sallah ba ya fada yana karasawa gadon dan bubbaga gadon yayi amma mata farkaba ya kara hura mata iska a fuska still shiri nanfa gabansa ya fadi sosai dan yasan bata da nauyin bacci hannunta ya daga yaga yakoma nanfa ya fara jijjigata yana kiran sunanta nanma shuru ahankali yasa hannunshi ya taba saitin zochiyarta yaji bata bugawa innalillahi wainna ilaihir raji'un...





     _Ya salam i have nothing to say 👌just waiting my next page✍_





       *tako har kullum*
              _nimcy luv_
          ❤❤❤❤❤

KADDARAR MACEWhere stories live. Discover now