ƙaddarar mace 42 by my nimcy luv

314 14 8
                                    

*🤦‍♀KADDARAR MACE🤦‍♀*

       *NA'EEMERH SULAIMAN*

     NIMCY LUV

           4⃣2⃣

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*@wattpad*
    Nimcyl


~ameena firstlady wannan page din nakine✋✊ mungode da amsa gayyatar mu zuwa program dinmu na musamman~



✨✨✨✨✨✨✨

Wani farin cikine ya saukarwa Daddy da Abba dama dukkan wanda yake wajan, fuska daddy ya haɗe yayi kamar baiji abinda anwar yace ba, ganin daddy bazai magana ba yasa anwar kallan abban jannat yace.

"Abba ina beby? An gama ɗaurin auranne? Meya kawoni asibiti kuma? Haka yayita jero tambaya, yana jiran Abba ya bashi amsa.

Murmushi Abba yayi kana ya jinjina kai yace.

"Son wanne aure kake magana ne, koka manta yanzo wajan 2years da auran ka"

Zabura anwar yayi daka kangadon da yake yana kokarin cire karin ruwan da aka samai bakinsa yana rawa yace.

"Abba ban gane makakeson cewa ba, nawa auran ko nasu yaya Faisal kake magana"

Numfasawa Abba yayi kana ya girgiza kai daman yasan dole akwai wannan ranar gashi yazo koya za'a ƙare dashi ohhho, kallonsa yayi kana yace "a'a kai idan akace shekararsu Faisal 2 da aure ka yarda, ina mgnar auran kane da matarka maimuna ina fatan yanzo ka gane"

Ai bai jira Abba ya karasa maganar da yakeson yiba ya ƙunduma wata ashar yana hantsiluwa akan gadon ya zare allurar hannunsa jikinsa na rawa ga rashin karfin jiki idonsa yayi ja hawayene ya fara zubuwa bakinsa na shaking yace wa .

"No! Abba how can i marriaed her, pls abba think about this, i don't like her at all, she can't be my wife ever Abba ya fada yana jijjiga kafaɗar Abba"

Wani wawan mari daddyn Anwar ya sakarwa anwar a fuska har sau biyu, kana ya nuna shi da ɗan yatsa yace.

"Kai banason shirman banza dana hofi, lokacin daka wulaƙanta beby agaban ƴan daurin auran kace baka sonta ka tsaneta kai maimu kakeso, ubanwa yayi maka magana uban ya takura maka, ina gargaɗinka da babu ruwan ka da jannat karka ƙara shiga rayuwarta bare ka ƙara War gatsa mata farin cikinta, kaje can ka ƙarata da mara ƙunyar matarka amma beby tafi karfinka kaji ko yana kaiwa nan ya fice ya bar ɗakin"

Jirine yake ɗibansa waishin yaya zaiyi da rayuwarsa, taya zai iya samu farin cikinsa a wannan lokacin, mafarkinsa ya wargatse, tunaninsa ya gushe shin ina zaisamu mafita, ji yake duniyya tayi mai zafi kallon key din hannun Abba yayi babu wanda ya kula ya fisgi key ɗin ya fice a guje.

*Singapore* da gyar ya samu ya shawo kan Jannat ta daina kuka, yayi mata dukkan tai makon da zai mata tarin da takeyi ya tsaya, yayi nasarar shawo kanta harya bata abinci taci ya bata magani tasha, yana shafa kanta yana bubbuga bayanta har bacci ya ɗauketa, tunanin mafita ya farayi amma ya gaza yin komai dukkan abinda ya saƙa sai yaji baya yimai dai-dai daka karshe ya yanke shawarar zai jira su gama exam idan yaso Saidu tafi Nigeria gaba ɗayansu dukkan abinda za'ai saidai ayi No matter how he can't life without her, madiha kowa dunda ta shiga ɗaki bata fito ba, tayi kaca-kaca da ɗakin nata tazama kamar mahaukaciyya, tayaya Abdallah saiso kawarta wacce take matukar jin kunyarta, kin yaudareni jannat kinso abinda nafi kauna aduniyya mai yasa baki gayamin dunda kuna tare ba, meyasa kinsan ina sonsa zakici amanata meyasa aminiyyata, what am did to you, tunda muka haɗo komai nawa ke nake tambaya hatta shawara idan inaso kenake tambaya why beby meyasa hakan ta faɗa tana cilli da Laptop ɗin gabatan ta.

*Bayan sati ɗaya a Singapore* sun gama exam lafiya sai jiran saka makon, shirye shiryen kumawa gida suke, idan kaga beby da madiha bazakace wani abu ya faru ba son koma dai-dai saidai ta ciki na ciki Abdallah yana basu kulawa sosai haka zai ce su shiga kichen gaba ɗaya amma madiha hakuri kawai take dan gaba ɗaya hankalin Abdallah na kan beby, abu kaɗan zai mata ta hau kuka harda dukansa, daman beby badai kukan kissa ba.
 

Tayiwa madiha da Abdallah sallama sbd dare yayi bacci takeji, ta gama shirinta na kwanciyya bacci, azkar take karantawa a wayarta ta gama kenan zata kwanta bacci message yana shigowa wayarta..........





*Gsky idan banga comments yadda nakeso va😡😎yasin yajin aiki zani ahhha✋🙅*

Comments and shere

KADDARAR MACEWhere stories live. Discover now