chapter 9- fatima

48 5 0
                                    

Ina xaune aka shigo ana murna , Wai an daura aurena , tashi nayi nashige toilet , ruwa na kunnawa kaina Ina kuka nayi awa biyu , nanny ce ta shigo dakin, Fatima !!! Fatima fitowa nayi da toilet ido na duk sun kumbura , Fatima kuka kikeyi rungume ni tayi itama kukan ta fara , nasan kukan me nanny keyi , ta Saba Dani , ita ta raine ni tun Ina yar karama ta , ita take lallashina , she's just like a mother to me yau Kuma gashi xamu Rabu , ba Dadi idan xk Rabu da Wanda kuka Saba , ba Dadi idan na tuna baxan dinga ganin nanny ko yaushe ba , kuka na sake fashewa da shi , dago ni tayi tace Fatima Kar ki damu xan dinga xuwa gidan ki duk ranar asabar Ina duba ki , kallonta nayi nace nanny ngd sosae Amma ba hk naso ba , xan. So mukasance tare har abada , kallona tayi tashi tayi Sannan ta fara mgn Tana kokarin kokarin fiddo min kayan da xas saka ,. Less ne fari gyalena ma fari ne , waddannan sune kayan da pappy yace na saka , fatima Nima din ba hk naso ba. , Naso ace muna Tare Amma yanxu lkcn xaman aure ne , kayana na saka sannan ta kawo sarka da yankunne da xobe duka na xinari , gyalen ta dauko ta daura min saman Kai na , fatima kinyi. Kyau kiyi hkr da inda xaa kaiki kinga dai auren Hadi ne kiyi koKari ki fahimce mijinki , wannan dawainkyace kanki ki kula da hakkin mijinki , ki nemi aljannarki ta hanyar bin mijinki ,sbd yanxu aljannarki ta koma hannun mijinki , nasan kina da hankali baxaki bani kunya ba , Fatima. Kar kiyi Wasa da addininki , ki Kuma riqe addu'arki sannan ki yawaita yin axumin litinin da alhamis shima ya bada kariya da. Kuma yawan yin Kiya mul lail , karki min godiya yanxu watara xaki min , idan Kuma na mutu kimin addu'a , jawo min gyalena tayi ta rufe min fuska , kuka nakeyi sosai , ta shi na tayi muka sauka parlor gurin su mammy da pappy , suna xaune Akan kujera , kasa na xauna gaban su , pappy ne ya daura hannunshi kaina Wanda xan iya cewa tunda nake ban taba jin hannunshi akaina ba , Fatima ngd Allah ya Miki albarka , kiya Fe Mana duk Abunda muka Miki , mu Baki Mana komai ba Kuma duk Abunda nake Miki banta jin Koda digon sonki ya ragu araina ba saima karuwa da yakeyi , Fatima muna sonki , bamuyi tunanin hanyar da muka dauka ta tarbiyantar da ke ta hanyar hantara ki xai cuta Miki ba Amma sai gashi ba ke ba har mu Fatima ya cutar da mu , hawaye m ne suke xuba idona , fatima kiyi hkr da mijin da na aura Miki wannan ne kadai gatan da xan Miki sbd kisamu farinciki Nan gaba , sannu a hankali xaki Saba da yanayin , karki manta dai yanxu aljannarki ta koma karkashin mijinki , Dan hk karkiyi kasa da guiwa gurin nemanta , Ina Miki fatan Alkhairi Fatima ba cikin gari daya xamu xauna ba Dan hk kiyi hkr da Ina xaa kaiki ki kasan ce Mai biyayya kamar yadda nasanki abaya xaki ci riba pappy ya fada Yana koKari. Goge hawayen da suka xubo Mishi , aranshi Yana cin daci , mammy ce ta matso tace Fatima baban ki yafadi duk abunda nakeson fada sai dai Karin Bayani , a matsayina ma mahaifiyar ki na yafe Miki duka hakkin haihuwa ki sannan Kuma inaso ki you hkr ki yafe min duk Abunda na Miki , sannan Kuma ki riqe addininki ki Kuma yiwa mijinki biyayya Allah ya bada xaman lpia ki tashi ku tafi dangin mijinki na jiranki tun daxu xaku wuce , nanny ta kamani na tashi mota aka sakani sannan nanny tashiga left side Dina aunty hassana kanwar mammy ta xauna ta Right side , gaba Kuma uncle husain twin brother aunty hassana , sai Kuma driver , mota ashirin suka min rakiya xuwa Abuja , karfe 6:00 na marece muka Isa bawani , maitama aka nufa Dani Kai tsaye gaban wani katafaren gida Wanda ko Vila albarka Dan girma , inaji idan nace xan xagayeshi to sai na kwana kafin na gama, Shiga naxo yi nanny ta tsaidani , addu'ar shiga gidan miji ta bani Sannan nashiga da kafar dama, wow masu karatu xan so kuga gidan domin kowa ya hadu ba karya su mammy da pappy ma sunyi aiki sosae domin kuwa wasu mutane suka dauko daga Dubai suka sake funitures
Daki na suka kaini xaunawa nayi tsakan gado dangin amarya duka suka juya suka Kama hanyar kaduna , suka dangin ango , already baba ( mahaifin Bilal) ya Kama musu hotel su kwana sbd dasafe su duba ya amarya ta kwana, Ina xaune naduba agogo karfe 8:30 gashi kowa ya watse , alwala nashiga nayi na Rama duka sallar da ake Bina , xaunawa nayi Ina jiran ango yashigo , amma haryanxu shiru , karfe 12:00 dai dai nayi deciding naje na cire Kaya na kamar ance na leqa window Naga wasu maxa biyu sun fito daga cikin gida , dama , da ga gurin da nake bana Jin me suke cewa sbd nayi nisa dasu , Ina 3rd floor ne , dayan Naga Yana dariya Dana kalli bakinshi da kyau sai Naga kamar ango yake cewa shikuma dayan ya daure fuska kamar Bai taba dariya ba, mgn Naga wannan Mai dariya yayi ma dayan a kunne dariya Naga sun fara yi Sannan sai Naga Mai dariya ya Shiga mota Yana Mishi hannun , bude gate akayi yafita shikuma dayan Naga yayi mgn da sojojin gurin kusan sunfi 20 duk sun baxu a gidan Banda wadan da ke waje, Shiga yayi ciki, saurin sauke numfashi nayi Ina tunanin wannan ne mijina , toilet nashiga nayi wanka na dauro alwala shiryawa nayi cikin , rigar barci Sannan na na dauko kur'ani na da mammy ta bani lkcn da xaa sakani mota krtu nayi sannan nayi addu'a , nashafa a jikina , kwanciya nayi sbd Naga har one tayi ba ango ba lbrnshi .
Dasafe dangin ango suka dawo suka kawo lefe akwati hamsin suka kawo wani daki suka bude suka saka min su dakin ma yayi kyau wata katuwar closet ce , wadda bansan iya adadin kayan da take ci ba kasan ta suka jera kwatunan miqa min wani Karamin akwati sukayi karba nayi ba bude wata katuwar sallayace da kuma kur'ani sai Kuma sarkar xinari , wannan ki aje gurin ki rufe closet din sukayi wannan kaya lefen ki ne mukullin dakin suka bani Sannan suka ce duk dakin da ke hasan uku da Kuna kasa gabaya nakine da kuma komai sake gurin nakine , Hawa na biyu kafin naki na mijinki ne duka , mu xamu tafi ,abincin ku na dinning area ohk to ngd ki gaida gida , rakiya na musu har wajen gida sannan na dawo ciki , his family I very nice but I don't think he's nice lyk them
❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️

Mrs Bilal❣️Where stories live. Discover now