👨✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨✈️
Written by *Zeeneert*💕
*Zeeneert* @ wattpad
*Page Seventy Two*
Ranar Tuesday Hajiya Asma'u mai dakin Chief of Army ta kira Ummi take sanar da ita the following day Wednesday zasu turo adawo da Lefen da suka kaima Iman sekuma Allah yayi Muzammil din ba mijinta baneba. Ummi sam idea din be mataba,aganinta ai su Chief of Army sunwuce haka agurinsu,kaya da sunan Iman akayi regardless of Muzammil ta aura koba shiba anma kuma bataso tayi karambanin yanke hukunci batareda tayi consulting su Daddy ba danhaka taceda Hajiya Asma'un sudan saurara zata sanar da maigidanta and they'll get back to them. Aikuwa Ummi nasanar da Daddy bejira jin nata ra'ayin bama yahau fadan miyasa zasu dawo da kaya aida sunan Iman akayisu. Yadaga waya yakira Chief of Army yana korafin sunfi karfin haka agurinsu,yace aceda familyn Abba mijin Iman din anhutashe su yin lefe anriga anyi mata. Inkuma sunyi insisting zasuyi duk bai baciba tahada dawannan din duka tayi amfani dasu and she should take it as gudumawa daga Uban dakinta Muzammil da familynshi. Chief of Army yarasa mezece da mutanennan da dimbin alherin su agareshi da ahalinsa. Yace Iman na godiya kuma shima bayaso yaji zancen Muzammil yace zaidawo mai da makullin gidan danba Iman ya aura ba! Regardless of waya aura gudumawar dayayi niyar bashi kenan. ALLAH yayiwa yaran duka albarka yabasu zaman lafiya agidajensu. Abba yace "Amin ya hayyu ya qaiyum"
Yana ajiye wayar yaceda Ummi tafada mai adadin kudin da aka kashe wurin hada lefen,Ummi tace batasani ba sede akira Mummy da su Mummyn Lagos atambayesu. Sune suka hada kayan. Daddy yace "Kirawo min su yanzu kice ina nemansu" tako daga waya takirasu tasanar dasu sakon Daddy,ba'ayi mintuna goma ba segasu a sashin nasu dayake duka suna can tare a sashin Mummy. Daddy ya tambayesu total din kudin da suka kashe inda Mummyn lagos tasanar dashi. Take yayi transfern thesame amount a account dinta yace aje ahada ma Mamansa exact lefen da akama Iman akawo. Mummy seta hau korafi,wai wani lefene za'asai ma Mami bayan uban kayayyakin da Amira ta nuna masu tace Muzammil ne yasaya mata a Abuja? Ga kayan biki dana hana gori da aka sai mata readymade da take da tabbacin zata iya jera watanni uku tana sasu batareda tayi maimaici ba? Tace da Daddy dan Allah amayar masa da kudin sa abar zancen lefennan aidama can ba wajibi bane al'adace. Inma kayan da akasaima Mamin basu mata bane tana iyace da mijinta suje tare tasai wasu amma Daddy sam yaki! Yace yanda akema kowace diya haka za'ama Mami ! Sukayima bare ma bare ita datake yar cikinsu da gatanta da komai? Dan Allah Mummy tabar zancennan tun kafin ranshi yabaci! Harshi zatayima fulaku ? Adole Mummy tahakura akabar zancen ganin kamar Daddyn yanaso yamaidashi wani lane da ita sam bahakane arantaba. Gani kawai tayi ba amfanin yin lefen tunda Auren gidane moreover sutura kowace irice in Mami batasai ma kanta ba tabbas Muzammil zai iya cika mata gida dasu batareda yaji ko dar ba! Ayi lefe azo ana nunawa duniya ana irga kaya dinnan ita sam ba burgeta yakeba anma tunda Daddy yadage yata iya? Sesuyi yanda suke so ai Yarsu ce sunkuma fi kusa.
Kwanaki biyar su Mummyn Lagos sukayi suna hada lefen Mami,sunkuma yi kokarin sayan kaya irin na Iman wadanda basu samu irinsu ba kuwa sesuyi replacing da wani da kudinsu daya koma yafi. Wannan karan ba atafi da Mummy ba instead Maman Khady da Aunty Khadija ne suka tafi tareda Mummyn Lagos din. Suna dawowa ba ahada wani gayya ba yasu yasu family members dinda basukai ga watsewa ba suka kaiwa Mami kayanta gidanta inda suka hada da Ubansun garan da Abba yayiwa Mami tuntuni. Komai dai son barka gwanin ban sha'awa, kana gani dai kasan kayane akayiwa yar so kuma yar gata!
Mami da Muzammil ba abunda suke se barzar amarcinsu! Kowannensu nan nan yake da dan uwansa tareda nuna masa soda kauna! Wai danma yan shige da fice irinsu Sa'adah da Nanaaa na taka musu birki dankuwa Yan Matan dake da wayonsu kuma kai awaye yake sukanyi skipping kwana daya basu leko ba inko sunzo baswa wani jimawa barinma insun tarar da Muzammil din a gida. Yara kananan ne dai ba'a da yanda za'ayi dasu,ko an hanasu sesun sulali jiki sunje. Kunsandai gidan amarya da farin jini agurin yara. Ko abinci wannan Mami bata fara girkawa ba,daga cikin gida ake kawo musu breakfast,lunch and dinner kullum hakanan kullum Muzammil inzai shigo dadare baya dawowa hannu rabbana,baroo da kayan makulashennan seya kawo mata and Mami couldn't be more than happier! Ayanzu jitake bawanda yakaita sa'a a duniya!
![](https://img.wattpad.com/cover/302177252-288-k647401.jpg)