Page Sixty Two

580 62 29
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert@wattpad

*Page Sixty Two*

***

Koda Mami tafita wani hadadden restaurant dasuka kware a harkar girke girke including continental dishes datakejin labarinsu tunma kafin tazo garin sokkoto tace da mai Taxi yakaita. Koda ta isa restaurant din table dinda babu kowa tayi booking ita kadai ayayinda tadauki menu tana duba abubuwan dasuke dashi akasa daga karshedai tace tuwon sakwara da vegetable soup dayaji namomi kala kala takeso sukawo mata. Sosai taci tuwon bayan ankawo mata danba karamin yunwa takejiba,ga uwa uba dadin da abincin nasu yamata! tunda tashigo restaurant din kuma take lura da few people around dakeyi mata kallon daya wuce shari'a amma se bata kawo komai aranta ba,tayi tunanin ko kawai tsarguwa ne irin nata. Ahaka ta kammala cin tuwon,tasha chilled exotic mesanyi datasa suka kawo mata ta kora da ruwa sannan tatashi taje tayi settling bills dinta tayi ficewarta a restaurant din. Abun mamaki kuma still wasu daga cikin mutanen dataketa wucewa nayi mata irin kallon da akaita mata acikin restaurant din dazu,yanzukam tattabatar ba tsargi bane kuma ba lafiya ba! Toh anma meyake faruwa ne wai? Why are they looking at her that way? gabadaya setaji hankalinta yatashi zuciyar ta nata dukan uku uku different thoughts running over her mind. Gashi itaba android phone ba bare ta duba danta tabbata wannan kallon da ake mata has to do with something about her daya gama gari by now! Yar Nokiar data saya ma tabaro shi a hotel cikin akwatinta bare takira Ammi taji ko menene! Take kuma idanunta yasauka kan wani CAFE dakenan tsallaken titi. Dasauri tayi crossing road din bayan ta tabbatar ba motoci masu tahowa sannan tashiga CAFE din. Gaisawa tayi da masu CAFE din ignoring irin kallon da daya daga cikin Samarin CAFE din ketayi mata tace hayar computer su takeso subata na yan mintuna zatayi amfani dashi. Guiding dinta daya daga cikin Samarin CAFE din ogansu yasa yayi zuwa inda computers dinda suke bada haya ke ajiye,kujera Mami taja tazauna ayayinda ta kunna Computer. Hannunta har rawa yake tsabar kidima dason sanin meke faruwa. Ahakadai tasamu tayi login to her Instagram sanin cewa nanne zata fi samun relevant information dinda take nema easily.

Haka tashiga scrolling recent feeds daketa shigowa,aikuwa batajima tana hakan ba idanunta suka sauka kan wani post da daya daga cikin manyan bloggers datake bi tayi and here goes the content

"Our renowned Chef and Food book authoress datayi fice cikin chefa chefaiii,the first Daughter to the Tumbidos in person of MARYAM ALIYU TUMBIDO has went missing and the Family has promised dukwanda yasamota koya fadi inda take will be rewarded with a token of 30million naira"

Se akasaka layinda za'akira in akasameta plus other details daza'a iya reaching family din! Next slide Mami tatafi danjin abun take kamar a mafarki kamar kuma ba akanta ake magana ba! Hotonta ne gashi barau barau akan screen din computer! Wanene da wannan aikin kenan? Take wani barin na zuciyarta ya raya mata

"MUZAMMIL" as far as she could remember Ammi tace Daddy Babba ya gindaya sharadin kada kowa yayarda yanemeta inbashiba!

But does he has to go to this length? Seda ya yada ta a duniya cewa ta gudu tabar gida? Eh mana? Waye zai karanta content dinda yabayardin batareda yayi zargin hakan ba?Wani irin takaici da bakin cikinshine taji yasake turnuketa lokaci guda!ayanzukam intace bata jin tsanar Muzammil azuciyarta tayi karya!he's the reason behind every single unfortunate thing dake faruwa a rayuwarta anma bakomai! Inshi naci dason ganin ya cinma dukwani abu dayasaka agaba ne burinsa batareda yadamu da feelings din waninsa ba toh ita taurin kai da kafiya ne nata!yagama duk abunda zaiyi but she won't ever let him wim over her akuma kanta zaifara losing!ita ba kanwar lasa bace ba ankuma shata ta warke!Yau indai MUZAMMIL yazo yasamota acikin garin sokotto yaci galaba akanta toh bata cika sunanta Maryama ba! Tatashi daga gaban computer tature kujerar data tashi kai kace yaki ne hakanan ba tayi ko logout daga Instaaccount dinnata batayi ba tsabar bacin rai. biyan masu CAFE dinma mantawa tayi zatayi ficewarta sukayi calling attention dinta! Adole tadawo ta sallame su sannan tafice!

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now