Page Sixty Six

1.4K 89 55
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@ wattpad

*Page Sixty Six*

Badai soyayyar sa na zuciya,jiki da bargonta ba not based on the personality Ameera portrayed? Badai tun asali tana yimasa soyayyar auratayya apart from na danganta ba?inko hakane yazatayi? Ina zatasa kanta da wadannan mugayen kaddarorin dake yawan jifanta akai akai? Wama zata tunkara da wannan maganar bayan cin kwan makauniya da diban albarkar datama daga familynta harshi Muzammil din?toh tama ce musu me? Tagano tana son Muzammil ayi hakuri amaida aurensu ajanye batun aurensa da Yar Chief of Army kome!?

Aikuwa data cika babbar mara hankali kuma Uwar rashin sanin darajar kai! Granpa kuwa ta tabbata wannan karan shida kanshi zai koreta yayi disowning dinta a family din gabadaya! Ga barakar datayi abaya data samu ta dinke within two months tsakaninta da sauran family din dazai iya sake rugujewa akoma gidan jiya! And how can she even be soo selfish? Shi Muzammil din tanada tabbacin yana sonta ne dukda tasha ji yana fada kuma actions dinsa sun nuna but what if yana fadan hakane sabida karyayi breaking heart dinta? What if yasha fadane sabida ya boye laifuffukan da Ameera tayi? What if the care and everything he showed towards her was only because she's his favourite cousin soyayyar dangantaka ce kawai? What if tun asali Yar Chief of Army yakeso sunjima tare he was only sacrificing to marry and make their marriage work sabida barakar da Ameera tayi? Inbahaka ba just two months da faruwar komai ace harya samu Mata angama maganar komai aure nan da wata daya!? Kai da walakin goro a miya!

Tasa hannu tatare hawayen data ji suna kokarin zubowa kan kuncinta!

Ita kanta ayanzu tasan Muzammil yayi mata nisan da bazata iya taroshi ba(he came right through her hands asaukake but she let him slip away)! Inkuma ita mai hankalice ya kamata tasamawa kanta sauki tasawa zuciyarta salama Muzammil ya haramta a gareta ta but then seta tuna ita zuciyar bata da kashi hakanan ita soyayya babu ruwanta da kudi,kyau,asali bare wani abu waishi "Sanin yakamata" You can control everything you feel within you but not when the heart is in love! Barinma irin tata zuciyar data taso da SON Muzammil,ta girma da SON Muzammil,ta wahala a SON Muzammil take kuma rayuwa da SON Muzammil!

Yakice shi a zuciyarta ba abune mai sauki ba bakuma tasan ta Inama zata fara ba! Da Allah yataimaketa seta shiga tuna kalaman Aunty Ilham alokacin datake cewa

"kizama mai fawallawa Allah lamuranki akoda yaushe dakuma kowane irin hali kika shiga and see how he brings solutions to you in a way you've never imagined....!" Takuma tabbatar da hakan cikin watanni biyu dasuka wuce(tasted and trusted)! Dawannan taji tadan samu kwarin gwiwa damuwarta taragu! She'll pray and pray! Zata roki Allah yacire mata son Muzammil yabarsu da soyayyar yan uwan taka dasuke ma juna! Zata roki Allah yabata ikon tayashi farin cikin sabuwar rayuwar dazai shiga yabasu zaman lafiya da matarsa har gaban abada tareda zuri'a dayyiba!

________

Ranar Monday da Sojojin Muzammil sukazo yin lunch Mami harta tashi zataje ta hada musu abincinsa wata zuciyar ta haneta dayin hakan,tace

"Keee raba kanki da wannan aikin iyayin tun yanzu! Inyayi aure keke da hakkin bashi abinci ko Matarsa?what if kika sabar masa bayan Auren yacigaba da requesting hakan yajanyo sabani tsakaninsa da matarsa?"

Dawannan tunanin tayiwa kanta fada takoma tacigaba da harkokin gabansa. Shiko Ogan yanacan yanajira ya kwashi gara anma harlocking lunch yawuce shiru,the following day ma haka. Arana ta ukun ne yakasa hakuri. Lokacin lunch nayi ya tattari yan komatsen sa se M.M. TUMBIDO RESTAURANT. Baikuma zarce ko'inaba se ofishin Mami. Ta idar da sallar azahar kenan tana ninke sallaya yashigo. tayi mamakin ganinshi amma ta boye mamakin nata. Tayi kokari ta saita bugun da zuciyarta keyi aduk lokacin dayake guri tashiga murmushin dole
"A'aaaa Hammah yau kaine a M.M TUMBIDO RESTAURANT?" Muzammil yace "Ba M.M TUMBIDO RESTAURANT ba har M.A. Tumbido all kinds of cuisines and delicacies(sunan restaurant din Mami dake Sweden kenan) kya ganni indai kika cigabada min irin wannan horon" harga Allah Mami bata gane Inda ya dosa ba,ta wara idanu da mamakin sa tace "Nikuma? Wani horo namaka?" Muzammil yakarkada kai in disbelief yace "Eh bazaki saniba dayake ba'a bakin ki kika lasa zumar kikajiba" ya rike kugu cikeda tuhuma yacigaba "Yarinyar nan narai narai kika fara aikamin abinci kullum ina kwasar gara ina saka miki albarka kwatsam seki daina babu kuma wani kwakkwaran bayani? Inma wani laifin nayi aise afadamin ingyara anma horon yayimin tsauri......" Mami dukda halin datake ciki ba karamin dariya Muzammil yabata ba. Yanzu dama dukwannan korafi da tuhumen tuhumen akan tadaina aika mai abincine? Yo ita inama tagane? Tayi kokari ta gimtse dariyar dake cinta aciki. Shiko ogan ya kasa ya tsare yanaso yaji laifin dayayi.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now