Page Sixty Three

1.1K 92 61
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert@wattpad

*Page Sixty Three*

Mami jin ya ambaci komawa gida batasan ina tasamo karfin data fizge jikinta daga nashi tanamai wani mugun kallo ba tace "Semuga tayanda zaka daukeni mukoma gidan ai inkai kakawoni!" Daganan tayi ficewarta a parlourn kamar zata tashi samaaa!

Binta yayi da rinannun idanunsa dahar sun canza launi yana shafa suman kanshi trying to regain his self from the moment anma harta bace mai da gani beji ya koma daidai ba,dakyar ya iya komawa ciki yazube kan daya daga cikin sofas dinda ke parlourn ya lumshe idanu. He could still perceive her scent through his nostrils

Ummin Sadiq dake Kitchen tareda Stella suna aiki dayake kofar Kitchen din a bude yake kawai se ganin Mami tayi tashigo tawuce daki,daga yanayinta kuma tagane basu wanye lafiya da Muzammil din ba. Tsame hannunta daga kwabin gurasar larabawa da takeyi tayi,taje sink ta kunna tap tawanke sannan tafice a kitchen din tanufi dakin da Mamin take. Abakin kofa suka kusa cin karo ita zata shiga Mami na kokarin fitowa sanye da hijabi yar karamar handbag rataye a kafada.

Ummin Sadiq daga sama har kasa take kallonta tace "Ina zakije?" Mami tace "Shine kika fada musu inda nake Ummi.....?" Sekuma tafashe da sabon kuka,Ummin Sadiq takama hannunta suka koma cikin dakin tazaunar da ita abakin gado tace "Kewai bakya gajiya da Kuka ne Dear?" itadai Mami kukanta tacigaba dayi batareda taceda ita komaiba,bata taba tsanmanin Ummin Sadiq zata shammaceta hakaba?tadauka she's siding her tana kuma sonta tareda danta shiyasa taketa nan nan da'ita tunda tazo gidan ashe abun bahaka yakeba.

Ummin Sadiq ganin Mami batada niyar daina kukan tace "Amma ai dama banmiki alkawarin bazan fadama su Mummyn ki kinanan ba ko ranar Dear. You're like a Daughter to me,yanda nadauki Sadiq haka nadaukeki sabida kedin wata abace mafi soyuwa agareshi. Ga uwa uba zumuncin dake tsakanina da Mummynki. Bazan iya ganin kina abunda baidace ba ingoya miki baya just because at the end it'll be in my Son's favour. Nida shi we are not selfish! our love for you is not about leading you to a destruction just because we want to have you to ourselves. A ajiye batun nida Sadiq ne a gefe shi saurayi ba'ayi masa haka Dear. You shouldn't ever chose a guy over your Family. Koshi bai goranta mikiba toh tabbas wataran familynshi sesun goranta miki that's if anyi sa'a sunyarda ya aurekinma kenan dankuwa bakowane iyaye bane zasu yarda su aura ma dansu yarinyar data bijirewa zabin iyayenta tagudu gidansu Saurayi! Duk soyayyar da Namiji zai miki bazai taba kaiwa kwatankwacin wanda Familyn ki kemikiba and no one want and knows what's best for you better than your Family. Guduwa from one place to the other bashine mafita ba Dear but instead face your reality! Kiyi hakuri kikarbi zabin iyayenki! Give your husband a chance and I assure you you'll get to know you're just having wrong perception about him due to his past mistakes! Inkuma danni da Sadiq kike wadannan abubuwan toh kisani baki burgemu ba dankuwa bazamu taba so muzama silar yiwa iyayenki rashin biyayya ba" anma sede maganganun Ummi ko kadan basuyi tasiri akan Mami ba. Ta kunnen nan suka shiga suka fita ta dayan,tadaukeshi amatsayin kara ne kawai Ummin ke kokarin yi bawai don batason tazama surukarta in the future ba and so she's still on her words! Muzammil seya saketa anyarda a gida za'a aura mata Sadiq zata koma gida.

Ummin Sadiq tashiga sharema Mami hawayenta trying to cheer her up tace "Ansan amare da kuka amma bantaba ganin meyin harda na banza irin nakiba Maryam" tatashi tadauko powder da wet lips dinda tasaya mata jiya dasuka je shopping agaban mirror tace "jiyan da fuskar ki ta kumbura tayi fusu fusu kamar ba amaryarda mijinta yazo gariba?" Dakanta ta shafa mata powder da wet lips din kuma ba laifi se fuskartata tadanyi wasai. Ummin Sadiq taciro mata wani maroon abaya daga cikin kayayyakin data saya mata tace tasauya dan na jikin nata normal shirt and skirt ne kawai. Haka Mami tasauya kayan badan ranta yasoba.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now