*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-
2Sumul suka farka innaji ranar ta d'an ji sau'ki, har yamma shatu na tare da ita Ta kasa motsawa ko nan da can ranar kam jikinta a sanyaye yake duk tsiwar da masifat ta zubar tana gefen innaji a zaune kan tabarmar karauni. Innajin Ta tsefe mata kanta Ta wanke tas da kanwa da karkashi sai 'kyalli gashin yake yasha man kwakwa kasancewar shatu mai gashi na ban mamaki tamkar mutanen 'kasar hindu don ma bata son gyarashi da 'kyar take barin innajin ta ta'ba mata kai shima sai tayi mata jan ido.
Har aka gama tana kwance lamo ba mai magana tsakaninsu ita innaji tana karatun suratu maryama ita kuwa shatu ta lula duniyar tunani gaba d'aya ta rasa sukuni.har la'asar tayi kafin ta mi'ke tayi alwala ta kuma zubawa innajin ruwan alwala innaji ta kar'ba tana murmushi " Allah yayi miki albarka shatu yasa ki cimma duk burin da nake miki fata a rayuwarki ". "Ameen " shatu ta fad'a murya a sha'ke. Suna idarwa innajin ta aiketa gidan modibbo kar'bo rubutu.Duk tsokanar da yara suke mata a hanya ranar banza tayi dasu burinta taje ta dawo ta iske innaji lafiya sumul, don haka take ta sauri kamar zata tashi sama.
Ko mintuna biyu bata yi ba a gidan moddibon ta juyo a sukwane ko saurarar gwaggoji ( salame) da take 'kwala mata kira ba tayi ba.
Kamar an cillota haka ta afka tsakargidan da sauri ta saki ajiyar zuciya had'e da cewa Alhamdulillah Allah innaji na d'auka kafin na dawo kin mutu" murmushi innaji tayi kafin ta furta "mutuwa ai sai lokaci yayi ayshatu" da sauri ta dubeta jin sunan da ta kira ta dashi innaji ta waro ido tace "lafiya " ta hau girgiza kai " ji nayi kin kira ni da sunan da baki Ta'ba kira na ba " dariya kawai tayi tana shan rubutun ta had'e da kallon shatu kallo mai nuna tsananin 'kaunar da take mata.
Cikin dare innaji ta fara jin ciwon na'kuda tun tana daurewa har abin yaci 'karfinta ta mi'ke da 'kyar ta bud'e wata adaka ta zaro wasu hotuna da biro ta rubuta address din family house d'insu ta nad'e a takarda ko bakomai bata san ya ta Allah zata kasance ba.
Da 'karfi ciwon yazo mata har bata san lokacin data fara tashin shatu ba a razane shatu ta tashi saboda wani mummunan mafarki da take a wannan lokacin, ganin innaji cikin wani mawuyacin hali bata san sanda ta zunduma ihu ba tana ru'kun'kumeta " bana so innaaji bana son mafarkin da nayi ya tabbata ". Da kyar innaji ta'ka'kalo wani murmushi tana mi'ka mata takarda " ayshatu ban san ya ta Allah zata kasance ba amma koma dai yayane bayan raina ki nemi dangi na idan mahaifana suna raye ki basu wannan takardar da wannan hoton suna gani sun san ke jini nace Ayshatu idan babanki ya dawo kice masa ya yafe ni Allah ya yanke ganawarmu ". Hawaye take yi sosai na tsananin azabar na'kuda. Ayshatu kuwa ta zama kamar mutum mutumi ta rasa ma mai zatayi abinka da'kan'kantar shekaru. Sai jijjiga innaji take ba bakin magana har zuwa sanda taji innajin ta saki kalmar shahada jikinta gaba d'aya ya saki ji kake d'if lamarin Alhakamu ya tabbata. Ita kuwa a nata tunanin barci innaji tayi bata san mutuwa ba bata san ya ake mutuwa ba gashi ana fad'a musu zafin fitar rai a yanda kuwa ake kwatantawa tabbas wannan ba mutuwa bace barcine ta ayyana hakan a ranta, don haka hankalinta kwance ita ma ta kwanta a gefen innajin barci ya kwasheta barcin da shine ya kaita har'karfe goma na safe.
Tana farkawa ta tashi a razane tana kallon hasken d'akin tare da tunanin me yasa innaji yau bata tashesu sallahr asuba ba. dubanta ta kai inda innajin take da sauri ta zare ido ganin idonta a kakkafe ya kalli sama ai bata san sanda ta hau jijjigata ba jin bata motsi yasa ta runtuma waje a guje tana Kiran jama'a "kuzo ku duba min innata tayi barcin zomo na tasheta ta'ki tashi " ma'kota suka shiga gidan sai gani tayi suna fitowa jiki a salu'be ga kallon tausayi suna mata . Kalmar da taji wata ta fad'a ne Allah yaji'kanki maryamu halinki na gari ya biki yasa ta farka daga tunanin da take na cewa innaji barci take.aiko zuba hannu aka ta 'kwalla'kara sai ganinta a kayi a zube ba numfashi.
Allahu akbar kabeeran Ubangiji kenan mai yin yarda yaso a lokacin da yaga dama Allah yaji'kan iyayenmu.