Me Zan yi da ita
46.
Wata irin bugawa zuciya ce ta risketa, lokacin da ta ji ana buga 'kofar d'akin, shi kansa bai san sanda ya bud'e ido ba, da azama ya mi'ke yana neman wajen 'buya.
Shatu da sauri ta ja hannunsa jin ana sake buga 'kofar wannan karan da d'an 'karfi, toilet ta tura shi ta jawo 'kofar da sauri, zuwa lokacin har wani gumi ya yanko mata duk da sanyin a'cn da yake d'akin.
Tana bud'ewa taga Hafsa a tsaye ri'ke da kanta, Ta d'an matsar da ita gefe "Matsa Shatu barci nake ji kamar na kifa, waccan 'yar rainin hankalin ta hanani barci, wallahi Nahna akwai ba'kar muguwa." Cikin wata iriyar razana Shatu tace "Tashin hankali anan za ki kwana?" Da sauri Hafsa ta kalleta, tana nazarinta sai ta lura kamar tana 'boye wani abu saboda yanayin yarda fuskarta ta nuna, Hafsa ta ce "Anan zan kwana is there any thing wrong?" Da sauri Shatu ta girgiza kai cikin matu'kar firgita, ta bata hanya ta wuce.
Jikinta a sanyaye ita ma ta bi bayanta hantar cikinta na kad'awa da kuma fargaba da tsoron kada Hafsa tayi katari da shi bata san wace iriyar amsa za ta bata.
Allah-Allah ta ke barci ya kwashe Hafsa ta samu ta bud'eshi ya fito,
Sai dai har zuwa lokacin Hafsan ba tayi barci ba tana dai kwance kanta yana sara mata.Shi kansa da yake cikin toilet d'in hankalinsa a tashe ya ke, duk wani sound d'in maganarsu a kunnensa suka yi shi, it means kenan kwanan toilet ya kama shi, ya juya ya dubi toilet d'in duk da neat yake and clean ba ya jin zai iya kwana sur a cikinsa. Idanunsa ya kai kan windown toilet d'in ya ga 'karami ne sosai ba ta yarda za'ayi ya iya fita ta cikinsa. Tsaki ya ja sosai ya tabbatar da maganar hausawa da suka ce idan ba ka iya mugunta ba ba ka yiwa kanka ba yanzu ya zai yi ya ku'buta daga tarkon da ya tsunduma kansa. Tur'kashi! Ace Mommah ta wayi gari a ganshi a bedroom d'in Shatu ai shikkenan kashinsa ya bushe ya kad'e kuma har ganyen sa.
Hafsa na daga kwancen ta zaro waya ta duba lokaci past 2:00 am, ido ta zubawa Shatu kafin ta ce "Ke me ya hanaki barci?" Shatu da ta lula duniyar tunani bata ji me Hafsan ta ce ba har sai da ta ta'bo ta kuma ta sake maimaita mata, a murya a d'ashe ta ce "Dama ina samun sleepless ban san me yasa Ba." Hafsa ta ta'be baki kafin ta ce "Saboda kina tunanin Imran mana kin kuma kasa fitowa ki gayawa Mommah gaskiya, ke mijin ki kike so kin bari kuna wahala da soyayyar juna, ni wallahi ban ga dalilin wannan kwamacala da Mommah ta ke shirin had'awa ba na yi mata magana ta kasa fahinmta, na kuma lura Nahna ce ta ke zuga Ta." Shatu shiru ta yi mata kawai, saboda ita ba wannan zancen ta ke so ba, so ta ke Hafsan ta yi barci Imran ya samu ya fito daga toilet. "Ta shi ki yi light off bana iya barci da haske, kema kuma ki kwanta ki runtse idon ki kina karatu a zuciyarki za kiyi barci." Shatu ta bi yarda tace ta kwanta ta runtse idon ta tana saurarar karatun da Hafsan ta saka mata, cikin hukuncin ubangiji barcin mai nauyi ya d'auketa. Hafsa ta bita da kallo zuciyarta cike da tausayinta ta tabbatar soyayyyar Imran ce ta ke d'awainiya da ita. Har ta rufe ido za ta yi barcin sai ta ga kuma gwara ta yi alwala ta yi sallah ta ro'ka musu Allah sassauci a zuciyar Mommah.
Direct toilet d'in ta nufa, Ba tare da wani sound na tafiya ba, saboda kada ta tashi Shatu, shi yasa Imran bai ji tahowarta ba balle ya yi locking toilet d'in. Ta murd'a da sauri kawai ta afka kanta ciki.
A tare wata irin fad'uwar gaba ta riskesu, Hafsa da Imran, har Shatu da ta farka jin sound d'in bud'e toilet, da sauri ta d'ora hannu a kai, shi kuwa Imran runtse idanunsa ya yi cikin wani irin takaici da dana sanin biyewa son zuciyarsa. Yanzu mai zai cewa Hafsa ta fahimci ba abinda ta ke zargi suke aikatawa ba? Babu! Direct zuciyarsa ta bashi amsa.
Hafsa kuwa wani irin sanyin jikine ya rufeta da tashin hankali lokaci guda. Kafin ta ja jiki ta jingina da bango sabods jirin da ta ji yana neman kada ita, cikin wata iriyar murya tace "Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna! Imran mai zan gani haka?"