*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-27Elegant Online Writers.......
Cikin rashin sa'a bayan ya murd'a 'kofar d'akin ya tarar da ita a rufe. Nocking ya shiga yi tun yana yi a hankali har ya koma yi da 'karfi amma Shaheedah bata bud'e ba. Cikin tashin hankali ya koma part d'insa ya samo spare key na part d'in nata sai dai ya tarar da d'akin ya 'ki bud'uwa alamar da key a cikinsa ta baya. Jikinsa a sanyaye ya koma bedroom d'insa. Cikin yanayin da shi kansa ba zai iya misaltawa ba, yanayin da ko yana saurayi bai ta'ba shiga irinsa ba.
Kwanciya yayi ruf da ciki a kan gadon sa yana runtse ido da addu'ar Allah ya lafar masa da
Abinda yake damunsa, amma abin ka da yanayi na sihiri abin 'kara gaba yake masa. Ganin yana neman hallaka yasa ya mi'ke yana tunanin samun fita, ji yake kamar yaje waje ko karuwa ya nema duk da bai ta'ba aikata zina ba. Sai dai take zuciyarsa ta hasasho masa halalinsa Shatu, tsoron Allah ya shige shi yaga gwara yaje ya kusanci Shatun domin ita halaliyarsa ce, da yaje yana bin matan banza a titi. Da sauri ya mi'ke bayan zuciyarsa ta gama hasasho masa Shatu ce mafitarsa.Ya dad'e a tsaye a 'kofar d'akin yana sa'kawa da warwara tsawon mintuna talatin yana shawarar shiga ko ya koma, amma jin lamarin yake kamar zai iya rasa ransa matu'kar bai kusanci mace ba. Ransa a 'bace yana jawa Shaheedah Allah ya isa ya bud'e d'akin Shatu ya shiga.
Kwance ya sameta tana barcinta peacefully alamar lafiya ta samu,
Ya dad'e yana 'karewa kyakykyawar surarta da kyan fuskar ta kallo, zuciyarsa tana ayyana masa tabbas idan ya kusancetan zai ajiye komai ya rungumi matarsa su zauna lafiya, ya kuma nuna mata soyayya sosai zahiran wa bad'inan ko da hakan yana nufin abokannasa za su tara mutane suyi masa dariya. Yanzu kam ya amince yana son Shatu So kuwa ba na wasa ba, yanzu ne ya fahimci yana da abinda zai yi da ita, ya 'kalubalanci furucinsa na Me Zan yi da ita? Ashe wannan lokacin zai zo da zai ji son Shatu? Ya runtse idanunsa yana switching light d'in d'akin, zuciyarsa na harba masa da 'karfi wai yau shine yazo Gadon Shatu da niyyar sauke bu'katarsa ta aure, tabbas Allah Alhakamu mai juya lamari yarda ya so ya kuma tsara shi a lokacin da yaga dama.Kyakykyawar rungumar da yayi mata da 'kamshin turarensa da ya ziyarci hancinta shi ya farkar da ita daga barcin wahalar da ya d'auketa,cike da tunani da tsananin 'kaunarsa a ranta, don bata sam ma ta yi barcin ba, saboda yanayi tunanin da ta lula.
Gaba d'aya ta ji ya lula ta wata duniya, duniyar da bata ta'ba mafarkin shiga nan kusa ba.yanayi mai wuyar fassaruwa, yanayin da zata so ta dawwama a cikinsa dimun da'iman, ko da ace mafarki ne ba zata so ta farka ko a tashe ta ba, balle ta tabbatar zahiran ne abinda yake aiwatarwa a jikinta. Imran mutum ne na daban da ya iya nunawa mace zallar soyayya tattali da shagaltar da gangar jikinta a wani al'amari can daban da ya zama sirrinsu ne. Sirri ne mai wuyar fallasuwa ga ma'aurata masi koyi da sunnar manzon Allah da yace a 'boye hakan kada a fallasashi. Mai fallasa shi kuwa ya zama daga cikin mutane mafiya shashanci a duniya.
Shi kansa Imran ya lula wata duniyar, duniyar da bai ta'ba tsintar kansa a cikinta ba a lokacin da yake mu'amalantar Shaheedah, akwai banbanci mai tarin tazarar gaske, banbancin yana yin taushin fata santsinta da laushinta, da wani kuma al'amari daban da bai ta'ba jin sa a baki da sassan jikin Shaheedah ba. Tabbas yanzu ya yarda mata ma suna suka tara ya yarda ko wace mace da baiwarta. Ya samu Shatu a yanayin da yake so matarsa ta kasance kuma ko a aljannah aka bashi za'bi akan Shatu da hurulaini zai yi fatan kasancewa da Shatunsa. A kunnenta yake ta jera Alhamdulillah ala ni'imatihi, sai wasu zantuttuka da ya dinga fad'a mata tun kafin ya kai ga sanin ta d'iya mace, wanda zantuttukan kad'ai sun isa sanya ta 'kololuwar alfahari idan kuwa ta tuna dasu ko da nan gaba ne sun isa su saka ta nishad'i ta kuma san tabbas Imran ya kai 'kololuwa a cikin. 'Kaunarta.
Komai ya kammala cikin hukuncin ubangiji ya kuma samu Shatun sa fiye da tsammaninsa ciki da waje sai dai yace Alhamdulillah.
Ita kuwa duk da tsananin azaba da taje ji bata saki baki tayi masa kuka ba, kamar yarda Shaheedah tayi shi kansa ya san Shatu akwai dauriya kamar yarda yake son matarsa ta kasance.A cikin daren ya had'a mata ruwa mai zafi, ta gasa jikinta sosai tana yi tana daurewa don ba 'karamar azaba ta sha ba. A gefen Gado ta zauna shi kuma ya fita da sauri cikin azama ya had'o mata tea mai zafi ya kawo mata sannan ya bata pain reliever ta sha, yana yi yana kallon fuskarta yana sakar mata murmushi alamar lamarin yafi gaban furtawa a baki. Ita kuwa tsananin kunyarsace take d'awainiya da ita don haka ta mi'ke da sauri ta zira hijab. "Muyi Sallah" ta fad'a a hankali murmushi ya sakar mata "zaki iya" ta d'aga kai kawai tana wasa da yatsunta. Saboda Shatu akwai Ibada kuma malamanta na Islamiyya sun gaya mata kada tayi wasa da 'kiyamallaili itace makamin 'kare dangi.
Sun yi salloli duk da ita a zaune tayi don ba zata iya yi a tsaye ba ya kama kanta ya dinga zubo addu'oi har abin ya bata mamaki ashe yana da ilimin addini haka, sam a haka sai ka zata bai damu da ibada ba. Yana shafawa ita ma ta shafa, tana shirin mi'kewa ya kama hannunta "Gwara da kika tuna min dama na shigo a wani yanayi shi yasa ba muyi sallahr ba amma yanzu ma da mukayi lokaci bai 'kure mana ba." Ya ja ajiyar numfashi sannan ya mi'ke yana kama ta ta mi'ke tsaye a kunne ya rad'a mata "ubangiji Allah yayi miki abarka ya bani ikon kyautata miki sannan kuma don Allah ki manta abinda ya faru." Ta d'aga kai tana murmushi, da kansa ya zare mata hijab d'in ya d'auketa cak sai kan Gado, su kayi kwanciyarsu cikin yanayi na matu'kar jin dad'i, ya kuma rungumeta tsaf a jikinsa kamar wani zai 'kwace masa ita."
——————-
Shaheedah kasa runtsawa tayi cikin daren, kuka kuwa ita kanta ba zata iya irga adadin da tayi shi ba, kukan take ba 'ka'k'kautawa tana dana sanin bata zuba masa maganin ba. Bayan ya gama buga 'kofar tana le'kensa ta ga kuma san da ya fito daga bedroon d'insa ya shiga d'akin Shatu. Hankalinta tashe ta shiga buga kanta a jikin wardrobe tana kuka, ga numberr Antynta ta 'ki shiga. A zuciyarta ta dinga ayyana shikkenan yau Imran ya d'and'ana wata macen duk da dai ta san i gobe aure ya mutu murus. Tunaninta ne ya tsaya cak lokacin da ta tuna iya zallar maganin na zubawa a shayi ta bashi ya sha bata bashi na naman ba. Ta zaro ido da sauri tana mi'kewa bata son a samu matsala, zuciyarta ta shiga harbawa ya akayi ta manta? Bayan mutumin ya ja kunnenta akan kada tayi kuskure yanzu tsoronta d'aya akan mai zai faru? Bata son lamarin ya juye kanta. Da sauri ta sake buga wayar Antynta cikin sa'a a lokacin ta shiga. Hankali tashe ba tare da gaisuwa ba tace "Na shiga uku Anty." Da sauri Antyn tace "Da aka yi me? Kin kuwa duba time Shaheedah past 3:00am fa." Cikin kuka ta shiga bata labari. Antyn ta zabga salati "lallai kuwa Shaheedah dole kice kin shiga uku ba ke kad'ai ba ma har ni. Wace irin wauta ce wannan? Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna sai fa da na ja kunnenki akan kada ki bada maganin ba tare da mahad'insa ba saboda shiriritarki yasa nace duk sanda zaki bayar ki nemi shawarata saboda in tuna miki yanzu ga shi kinje kin ji'ka mana aiki. Sai ki jira zuwa wayewar gari muga abinda zai faru. Yanzu na san ko na kira Shuwa wayarta ba shiga zata yi ba tana can tana yawon banza." Kuka Shaheedah ta saka kalmar Na shiga uku kuwa ba ta bar bakinta ba.Ai kuwa Shaheedah yarda ta ga rana haka ta ga dare gashi taje ta ga Imran bai dawo d'akinsa ba. Ta tabbatar har a lokacin yana tare da Shatu, hakan ya dad'a d'imauta zuciyarta, ta tabbatar da maganin yayi aiki da yanzu wani zancen ake ba da ba wannan ba.
Har Asuba tana jiran wayar Antynta. Sai da aka idar da sallah sannan Antyn ta kira, duk da ita Shaheedahn ko sallahr ta gagara yi. Da azama ta d'aga wayar cikin murmushi Antyn tace "ki kwantar da hankalinki boka yace wa Shuwa bakomai tunda har ya sha na shayin, sakin zai yiwu 'kiyayyar ce nan gaba zata iya gushewa amma kafin lokacin za'a san abin yi in dai sakin ya yiyu za'a yi musu farra'ku. Yace na tsananin tsanar a cikin naman yake." Shaheedah da sauri ta saki dariya cikin zakwad'i tace "Har naji dad'i da wallahi hankalina a tashe yake. Ina godiya Anty na samun kamarki sai an tona really proud of you yanzu shegiya yau zata je musu da black news." Ta she'ke da dariya Allah dai ya bar mana Anty shuwa" Anty tace ameen ai ta cika aminiyar 'kwarai."
(Masoya na kuyi ha'kuri da jinkirin da aka samu yau biki muke wallahi shi yasa ma zaku ga typing d'in kad'an ba haka na so ba. Sannan gobe insha Allah ba typing ina da babban uzurin da zai ri'keni zuwa jibi dai insha Allah zaku ga typing mai yawa. Wallahi ina sonku sosai kamar yarda kuke son books d'ina domin da bazarku nake taka rawa💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿)