Me zan yi da ita?
47
Mommah da sauri ta zubawa Hafsa ido cikin raunin murya ta ce "Me ya faru daren jiyan?" Hafsa ta ja ajiyar zuciya, cikin sanyin murya tace "Mafarki na yi da ban ji dad'insa ba shine nake son ki dubi Allah Mommah ki yi ha'kuri Shatu ta koma d'akin mijinta..." Gaba d'aya da Mommah da Ammar suka zuba mata wani kallo, murya a tunzire Mommah ta ce "Shi kuma Ammar d'in fa?" "Ya yi ha'kuri Addarmu ai dama ba matarsa bace, shiga hurumin da ba nasa ba ya ke son yi." Hafsa ta fad'a with confidence.
Mommah tsaki ta ja kafin ta ce "To Hafsa sai ki bari sai Hajiya Mama ta mayar da mu ciki tukun kin zama kece ya sannan ki ba ni umarni na bi, daga yau bana son sake jin maganar nan, Shatu Ammar zata aura fa'kat." Ta mi'ke a zafafe ta shige bedroom. Gaba d'aya wajen sakin ajiyar zuciya kawai su ke yi, suna mamakin kafiya da taurin kai irin na Addarsu. Hajiya Mama ta ja numfashi kafin tace "Allah ya yi mana mai kyau, ku tunda bata son maganar kada wanda ya sake mata kun san dai ciwon zuciyar da take fama dashi, da 'kalau ta ke nima da ba zan lamarin ya kai haka ba, idan ban da rigimar Dijah ina aka ta'ba yin haka fisabilillahi, 'ya'yanki biyu jal da Allah ya ba ki kiyi 'ko'karin had'a gaba tsakaninsu." Alhaji Baba ma shiru ya yi yana tunanin wannan abin da ko a mafarki bai ta'ba tunanin wanzuwarsa a zuri'arsa ba, sai dai tabbas ya san hukumullahi la ajabun.
Shatu sai a lokacin wani abu ya fad'a mata farinciki ya mamaye zuciyarta, tana sake martaba da daraja Hafsa a zuciyarta.
Imran kuwa jiki a sanyaye ya juya ya fice daga gidan.
Hafsa takaici ne ya gumeta na rashin kar'bar uziri irin na Mommah da ba su san dalilin canjawarta ba, da dai macece mai ha'kuri da saurin yafiya, amma yanzu duk ta canja. Jikinta a sanyaye ta mi'ke ta wuce d'akinsu.
Shatu na ganinta ta fad'a jikinta cikin tsananin farin ciki tace "Nagode Aunty Hafsa." "Ki godewa Allah da ya kimtsa min tunanin na rufa muku asiri a lokacin da na yi nufin tona muku, a karo na 'karshe ina sake jan hankalinki a kowane hali zaki kasance ki guji kad'aicewa ke kad'ai da namijin da ba muharraminki ba a d'aki d'aya,
Ke ko muharraminnaki ne ya kamata a matsayin ki na mace ki ri'ke martaba da 'kimar jikinki ko bakomai shine abin tun'kahonki, ina amfanin abinda ki ka aikata? Da ban shigo ba mai kike tunanin zai faru? Kina tunanin zai kyaleki ne a lokacin da yake neman farautarki ta kowane hali, sharrin zuciya kina tunanin ba zai iya saka masa tunanin ta hai'ke miki baa idan yaso ko da tsiya ko da tsiya-tsiya dole a mayar masa dake, mai zaki ce da Mommah da take 'ko'karin kare martabarki da kimarki?" Hawaye ne ya 'ballewa Shatu kamar famfo da sauri ta fad'a jikin Hafsan ta rungumeta tsaf, cikin kukan ta ke fad'in "Nagode, amma ina neman shawara ki gaya min yarda zan cire sonsa in maye gurbinsa da Ammar, wallahi na kasa Aunty Hafsa kullum sonsa sabunta ya ke a zuciyata." "Ki yi 'ko'karin tursasa zuciyarki wajen tunano duk wani rashin arziki da yake miki zaki ji kin daina son sa, ko na ce zai ragu a ranki, tun farko dai da Mommah ta yi shawara damu da wani ta barki kika aura ba Ammar ba, wallahi ina tsoron fitinar da zata iya kunno kai anan gaba." Ita kanta jida take kamar ta yi kuka, sosai ta ke tausaya musu.Shigowar Nahna da sanar da su mai gyaran jiki ta zo ne ya saka su yin shiru da zancen, suka fara shirin gyaran jikin.
Matar ta goge sosai komanta kuma da na zamani ta ke aiki,
Nan da nan kan kace me ta fara aikinta cikin 'kwarewa da sanin makamar aiki.——————————-
A zafafe Hajja ta d'auki invitation cards d'in tana dubawa, da hanzari ta mi'ke tana sakin hucin 'bacin rai, ta watsawa Manga cards d'in.
"Lallai Manga al'amarinka azimin rashin mutauncin da rashin darajani har ya kai haka? Auren Ammar d'inne sai yanzu za'a gaya min da ya rage saura sati biyu, wato nima naina tafi a 'yar gayya kenan? To ma uban wa ka nad'a da ya kai ma su lefe mu aka saka mu a gefe?" Manga ya sunkuyar da kansa yana jan duk addu'ar da tazo bakinsa kafin yace "Ai abin na gida ne, zancen gaba d'aya bai ja wani lokaci ba, kuma yarinyar da zai aura ba wata bace wacce Imran ya saki ce Shatu." Wannan karan wani zafaffen zagi Hajja ta 'kunduma masa "Wannan masifa har ina? Shin dole ne sai sun aureta? Da Dijah ta bi ta ishishshire, ban ga dalilinta na son wannan had'in ba idan ba wata manufa a ranta mai zai saka ta kafe ta nace, gobe zan dira a Abujar in ji hujjarta na aikata haka? Kai kuma da yake ka zama sallamamme sai ka 'kyaleta tana maka walagigi da yara saboda ta had'a gabar da ba zata mutu ba. Wannan masifa har a ina? Ni ko yarinyar nan bata da asali ne shi da yasa ba ta son ta bawa na waje gudun tonuwar silili." Manga da sauri ya ce "Subhanallah Hajja ki daina wannan zancen" "Na 'ki na daina nace na 'ki na daina ubana Manga, koma menene gobe zan je naji dahir ai." Manga ya mi'ke a hankali ya ce "Allah ya kaimu, sai mu tafi tare nima goben can na nufa." "Ina kuma ka baro Zainab?" Gaba d'aya annurin fuskarsa ya 'bace 'bat kafin murya a cunkushe ya ce suna hanya ba mamaki jibi, daga nan sai kunan wuce bikin." Tsaki ta ja ta ce "Wani bikin? Bikin gaibu bikin da babu shi?" Shi dai bai yi magana ba ya wuce sashensa yana raya "Kawu sa'idu kad'ai ya isheki Hajjarmu, ban da bana son tona asirin zainab a tsukun lokacin nan yau da na nuna miki vedion Zainab da zaki kwana kina tsine mata, amma akwai lokaci."