14

183 8 0
                                    

*🤍ME  ZAN YI DA ITA?*🤍

        NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-14

Tun da ta ganshi a parlourn hakan yasa ta zama don taga ko zaici abincin,shi kuwa yana dinning a zaune ya had'a tea ba tare da ya dubeta ba da alama sauri yake don haka da azama ya d'aga cup d'in tea d'in ya kur'ba ya kuma bud'e bowl d'in peppe soup d'in ta zuba a plate ya kai baki yana kur'ba dad'in peppe soup d'in ya ratsa har kwanyarsa ya lumshe ido yana sake zu'ka. Dariyar da shatu ta saka ce yasa shi saurin bud'e idonsa sai kuma ya had'e ransa yana dubanta tana ta she'ka dariya har da tuntsirawa,jikinsa ne ya bashi tabbas akwai dalilin dariyar tata don haka da sauri ya ture plate yace"ke zo nan" tana 'kunshe baki ta fara shirin guduwa "wallahi kika d'aga 'kafa daga wajennan ko da one step ne zaki ga abinda zan miki zo nan nace." Hantar cikinta ne ya d'uri ruwa har ta juya zata wuce ba tare da taje d'in ba taji ya dam'keta ta baya gashinta yaja taji zafi sosai don haka ta runtse ido."Don Allah ka sakar min gashi akwai zafi fa to wai mai ma nayi maka?" Tayi maganar cikin muryar shagwaba bai mata magana ba ya jata zuwa part d'insu a parlour ya wurgata saman kujera"gaya min uban me kike wa dariya ko na baki wahala nan dai ba mai cetonki balle kice wallahi idan baki gaya min ba ko school d'in da kike zumud'in zuwa ba inda zaki"Jin yace ba zata school ba ne hankalinta ya tashi duk d'okinta da takeyi zai ruguza mata shiri ta fara rawar baki"kada ki sake kiyi min 'karya ina da abinda zan saka a jikinki in gano gaskiya don fad'a min gaskiya kafin na gano da gaskiya." Ya fad'a cikin'kara tsare gira. Hakan ne ya sake razana ta tayi saurin cewa "idan na gaya maka gaskiyar zaka barni in wuce school?" "Fad'i ina jinki" ya fad'a yana tsareta da ido. Ajiyar zuciya ta saki sannan tace "Don Allah kayi ha'kuri a cikin peppe soup ne na zuba yawu na a tea kuma na zuba maka ruwan hamma....." da sauri taga yayi toilet yana kakarin amai hakan yasa ta suri school bag d'inta tayi waje a guje. Ya dad'e yana amai kamar ya amayar da kayan cikinsa 'karshe ya fito har wani jiri yake ji kamar ya kifa haka ya kwanta akan gado yana maida numfashi har ga Allah yarinyar nan ta cuceshi cuta bata wasa ji yake kamar ya fito da kayan cikinsa ya sauyasu ha'koransa kuwa da harshensa ya dirje su yafi sau nawa har rad'ad'i suke masa zazzafi mai zafi ya kamashi haka ya 'kudunduna a gado duk da yana da important issue haka ya ha'kura da fitar.

A school an kar'beta ko da suka gwadata suka ga gwara kawai su kaita primary five tunda tana da sharp brain idan yaso a gida a samar mata lesson teacher.

Da ta dawo kuwa samu tayi duk gidan suna part d'insu Imran wai bashi da lafiya ta'be baki tayi ta samu abinci kawai ta fara ci ita ina ruwanta da ciwonsa mutum sai shegiyar tsaftar tsiya har da wani amai da ciwo. Taci ta 'koshi sannan tayi wanka ta zira da wando tana fitowa ta tarar da mommah ta shigo. Mommah ta bud'e mata hannu tana welcoming d'inta tare da furta"oyoyo autar mommah ya school d'in" ta d'aga kai "
Ba laifi mommah amma fa sai an jawa 'yan class d'in kunne bana son rashin kunya don naji suna ce min wai ra'kumi a cikin 'yan tsaki to yau dai nayi musu na ba'kunta gobe kuwa wallahi na jaki zasu ci" Mommah murmushi tayi ta dafa ta "ba'a fad'a a makaranta baby na kada ki kula kowa kin ji'yar albarka kiyi karatunki kawai ki koma gida shine abinda ya kaiki kinji?" Murmushi tayi ta d'aga kai shigowar nahna ce yasa mommah ta tuna ruwan tea zata dafawa Imran kuma ya ro'keta don Allah da kansa zata kawo masa don yanzu tsoron ta'ba komai na gidan yake da zai iya ma da kansa zai shiga kitchen d'in ya dafa to jiri yake ji saboda tun safe ba abinda ya shiga cikinsa.Momma ta girgiza kai "kinga kuwa nahna shaf na manta abinda nazo yi bari in tashi" Nahna tana dariya tace "ya kuwa ce da kanki yakeso ki dafa masa kuma kina juyewa in kawo masa ni ban san me ya sameshi ba" mommah tace "mhmn rabu da Imran haka yake idan yana cuta sangarta ce dashi zan ga yarda matarsa zata yi da 'kyan'kyaminsa wallahi abin yana damuna sai kace wani mai cutar tsafta." Da kanta ta dafa tea d'in ta bawa Nahna ta kai masa.

Yana ganinta ya mi'ke zaune da kyar yana ri'ke kansa ya jingina da bangon gadon a hankali ya motsa bakinsa muryarsa ta fito "please mommah ce ta dafa kuma kina tsaye a wajen? Ibilishiyar yarinyar nan kuma bata wajen ko?" Nahna ta girgiza kai tana dariya ta tabbatar masa mommah ce ta dafa da kanta. Ta zuba ta mi'ka masa yana sipping a hankali. Lokacin shaheeda ta murd'a 'kofa ta shigo kallo d'aya tayiwa nahna ta d'auke kai hannunta d'auke da cooler ta nufi gefen gadon ta zauna cike da kwainane sai zabga 'kamshi take ta zauna a gefensa tana jan yatsun  'kafarsa "am sorry Habibi ya jikin?" Nahna ta kai idonta kan hannun sai kuma ta ta'be bakinta da sauri ta fice tana mamakin rashin kunya irinta 'yan matan yanzu sam basa iya tsare mutuncin kansu shi yasa ko auren aka yi mazan basa ganin mutunci su.shaheeda ta sake kallonsa tana murmushi " Habibi in zuba maka abincin?" Da sauri ya girgiza kai, ta kuwa had'e rai a hankali tace "kai habibi I cooked it with my own hand fa please kaci kaji?" Cikin muryar shagwa'ba take gaya masa hakan ya sake narkar da zuciyarsa yana jifanta da wani kallo ya matsu ya matsu sosai ya auri shaheeda shi kad'ai irin son ta da yake dan'kare a zuciyarsa yana jiran lokacin da Zai amayar dashi.ta zuba a plate ta zauna tana bashi a hankali cikin sigar jan hankali.

Mommah ce ta tilasta shatu sai taje dubashi, ta mi'ke tana zun'bura baki a zuciyarta take tunanin ita mommah bata san itace silar ciwon bane ta tabbata yanzu idan taje sai ya huce haushin abinda tayi masa. Hafsa ce cikin fad'a tace "Ba zaki tashi kije ba sai na 'bata miki rai baki san d'an uwanki bane shi duk duniya baki da kamarsa fa shi da Ammar." Mi'kewa tayi ta fita niyyarta idan ta fita ta la'be ta dawo tace taje, sai dai a rashin sa'arta Nahna ta mi'ke tace "Bari muje na san halinta yanzu ta 'buya tace taje." Ta tura 'kofar bed room d'in a hankali bayan ta shiga parlourn hakan yasa Nahna saurin juyawa ta koma. Ita kuwa shatu mummunan gamo tayi shaheeda ce a gefen Imran tana ta shafa masa fuska wai tausa take masa ta shige jikinsa sosai kamar me. Da sauri shatu ta runtse ido tayi saurin juyawa shi kuwa Imran motsin da yaji ne yasa shi saurin mi'kewa sai yaga fitar shatu da sauri ya janye jikinsa yana wa shaheeda wani irin kallo "sau nawa zan gaya miki bana son irin wad'annan abubuwan bafa wayewa bace yanzu kinsa yarinya 'karama ta gammu a haku me kikeso tace mai kike so tayi zargi a zuciyarta?" Shaheeda marairaice masa fuska tayi "Haba habibi meye a cikin hakan kawai fa tausa ne amma tunda baka so insha Allah na daina Allah ya kaimu lokacin da zaka zama halal d'ina in nuna maka pure love da ba surki amma waccen yarinyar mai take zuwa yi har bed room d'inka?" Runtse ido yayi yana tunanin lamarin yarinyar baya ko son ganin fuskarta tsoronta lamarinsa yake bashi don haka dole ya samarwa kansa lafiya ya fita sabgarta kafin tayi abinda zai kaishi lahira burinsa ma lokacin bikinsa yayi ya tattara ya bar gidan ba sai ta ganshi bama balle ta hukunta shi da 'kazantarta.

A ranar Dahda ya dawo amarya aka shiga giringid'ishin kama miji mommah dai ko gurinsa bata jeba balle taga abinda zai 'bata mata rai, sai da ya gaji da kansa ya shiga part d'inta tana zaune da kwalliyarta ta tsadaddiyar atamfa ta kashe d'auri parlorn nan sai 'kamshin turaren wuta yake yi. Murmushi ya sakar mata "uwargida ran gida barka da hutawa ni nazo gaisheki tunda ba'a nemansa" murmushin ta saki itama bayan ta gama saurararsa tace "hakan da kayi shine abinda ya kamata ka bi cikakkiyar sunnar manzon Allah ya hanya?" "Alhamdulillah" ya furta yana sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya ya tabbata da itace da girki da tuni ta kai masa ruwan wanka ta kuma taimaka masa da tausa da lafiyayyen girkinta tana zuba masa tana murmushi ba dole dijah ta sace zuciyarsa shi kad'ai ya san wacece dijah ya kuma tabbatar ba zai samu kofa kwafinta bane balle wacce ta kaita. "Na biya wajen hajja wai me ya faru ne ta tabbatar min da aljannu a cikin gidannan wai ba zata sake zuwa ba" yana murmushi ya fad'a mommah ma dariyar tayi tace"Ba mamaki da aljannun a d'akin da take sauka amma mu dai bamu ta'ba gani ba" "Ni na sani na san rigimar hajja ce yanzu ba ma wannanba ta rigime min sai anyi bikin Imran nan da wata d'aya da Rabi" mommah ta saki murmushi kafin tace "Masha Allah Allah ya nuna mana me yayi saura ai ya gama gininsa Allah yasa albarka yasa abokiyar arzikinsa ce yana d'akima ba lafiya" Dahda ya mi'ke "ai naje na duba shi ina shigowa zainabu ta fad'a min Allah ya bashi lafiya yace min stress ne yayi masa yawa Imran ne akwai son kud'i baya son hutawa" mommah tana dariya tace "kyan d'a ya gaji ubansa"

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now