3

207 10 0
                                    

*🤍ME  ZAN YI DA ITA?*🤍

        NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-
3

"Waye nan" jatau ya sake fad'a da sauri shatu ta juya tayi kamar zata shiga bayan gida, murya can 'kasa tace "nice zan zaga ne " tsaki yayi ya shige yana bambamin fad'an "iskancin banza da wofi kawai ki nemi frigita ni cikin tsohon dare zan yi maganinki mai kama da ifritan aljannu" shatu dai bata ce komai ba tabi bayansa da harara tana sakin  'kananan tsaki " aradu Allah zai kaimu lokacin da zanyi maganinku " yana shigewa sad'af- sad'af Ta shige bayan gidan ta kuma haure'karamar katangar ta bar gidan a guje.

Shatu duk da kasancewarta yarinya da ba zata gaza shekara sha biyu tana da wayo da kaifin basira, hakan yasa bata sha wuyar kai kanta tasha ba, ta hau motar da zata kaita har cikin gari sannan aka saka ta a motar garin bauchi.

*************

Tafiyar awowi ce ta kaisu bauchi ko daga nan ta tambayi motar katagum, yaran tasha yasa ta a motar da zata kaita tafawa balewa daga can ne zata samu motar katagum.

Suna isa kuwa kasancewar gidan babban gidane bata sha wuyar nemansa ba a kasadata da family house din nasu. Duk inda ta wuce sai an bita da kallo kasancewar tayi kama da mutanennan da ake kira bararoji, jikinta dukun-dukun hakanan kanta she looks very dirty.
Sam bata damu da rufe gashin kanta ba haka take tafe wurjanjan da silifas wari da wari a 'kafarta.

Gidane babba irin ginin mutanen da , mai dauke da d'akuna birjik a kowacce shiyya, kasancewar nan ne ainahin gidan sarauta na garin, yasha gyara sosai da paint kana gani dai kasan ba wahala a tattare da ahalin gidan. Fili ne fetal ga manyan bishiyu ko ta ina. Rashin sanin inda zata yasa ta nufar wasu yara da taga suna wasan'kwallo a harabar gidan, ganinta a gurin yasa suka arce da gudu don su tabbas zatonsu aljannahce. Tsaki shatu taja had'e da komawa can gefe da 'kullin kayanta ta zauna.

Iface-Ifacen yaranne ya fito da ahalin gidan a rud'e suna duban yaran da suke fad'in "Aljannah Aljannah " shatu ta girgiza kai tana juyosu daga waje a zuciyarta tace "ai kuwa sai kunci  'kwal uwarku akan iyayenku zan huce a aljannar zan zo musu kafin na bayyana kaina " da sauri ta hargitse sumar kanta tsaf ta mi'ke ta hau zare ido ta shagid'e hannu d'aya, Ta dumfari babbar shiyyar da taga yaran sun nufa.

Ba zato ba tsammani suka ganta a tsakiyar filin kan kace meye iyayen yara sunyi hanyar neman tsira sai tsohuwa dada da aka bari jikinta yana'bari tana fad'in innahu min sulaimanu kuyi min aikin gafara wallahi ba laifina " shatu ta cusgune fuska  ta dumfari dada ai kafin kace mai dada ta saki gudawa da fitsari a wando ganin tana shirin fad'uwa shatu ta tintsire da dariya " ke tsohuwa dakata kada ki sume min ni ba aljannah bace kamar yarda kuka d'auka mutum ce ni d'iyar maryama 'ya wajen d'anki Lamid'o ". Dada ta zaro ido tana kallonta kafin tace "ki rantse da Allah " shatu taja tsaki " kwarankwatsa ni ba aljannah bace ko kinga kofato a 'kafata " sai sannan dada taja dogon numfashi tana zamewa a jikin bango zata zauna. Shatu ta kalli gudawar tace tana toshe hanci. Sai sannan dada ta lura ta saka salati da sauri ta rarrafa tashiga bayan gida shatu kuwa sai tuntsira dariya take.

Sai dada ta kimtsa ta dubeta bayan ta kaita rumfarta taje ta kira matan gidan " to duk ku fito ku ji min bayani wai wannan d'iyar maryama ce maryaman da tuni lamid'o ya sallamata ga d'iyarta mai kama da jinnu ta bayyana " shatu ta girgiza kai a hankali ta furta "zaki bayanin wannan ma ".

Sai sannan kowa ya fito cikin tsananin ta'ajjibi ana kallon shatu wai wannan jinin lamid'o ce yarinya kamar fulanin daji ita kuwa maryama mai yayi mata zafi ta za'bi rayuwar daji akan rayuwarta cikin gata da mutuncinta ". 'Daya daga cikin matan ta fad'a shatu ta watsa mata wani kallo had'e da cewa " yo haka 'kaddarar Allah ta za'ba mata kuma kada a sake a zagi uwata don kuwa bata raye aradu raine zai 'baci " Ta fad'a cikin karyayyiyar hausarta ta fulanin usli. Gaba d'aya suka zaro ido dada ta saka kuka "yanzu'yar nan kika ce maryama ta mutu? Innalillahi yau ya lamid'o da liman zasuji da wannan ba'kin labarin kullum zancen su na maryama ne "
Ta fad'a tana jan majina hawaye sha'be-sha'be, kafin ta share hawayenta tsaf ta mayar da kallonta kan shatu tana mata kallon  'kurilla " wace shaida zaki bamu mu yarda ke d'in jininmu ce d'iyar maryama daso?" Shatu ta mata wani kallon she'ke'ke aradun Allah babu shaidar da zan baku sai na cika cikina tunda ku kam baku san zuru ba kun san wahalar da na hya kafin nazo nan amma ba wanda yace min ga ko ruwa Na hya " dada tace "kwarai da gaskiyarki ke harira kawo mata abinci ke kuma furera ki kira matar lamid'o kice ko mai suke su biyo jirgi daga habuja suzo hukuncin ubangiji ya tabbata."

Ana kawo mata abincin ta fara ci hannu baka hannu kwarya dad'in abincin har tsakar kanta ga nama zu'ku-zuku wanda rabonta da cin nama tun sallahr layya ta bara idan har bata manta ba.  Taci tayi nak ta sha zo'bo sai sannan ta fara washe baki tana dariya ta kalli dada "to ko ki yarda ko kada ki yarda ni d'in diyar maryama ce ga hotunan da ta bani kafin rai yayi halinsa" ta fad'a tana zaro hotunan daga bujen da yake jikinta. Wanda suka san maryama da wanda sai a hoto suka santa duk suka zaro ido dada girgiza kai " ba shakka hukumullahi la ajabun innalillahi wa inna ilaihirrajiuna wato maryama daso sallama tayi damu " hawaye shabe shabe dada ta saki tana sake rushewa da kuka , sai kuma ta dubi shatu tana fyace majina " ikon Allah wato shi ubannaki bararo ne?" Shatu ta zaro ido " kan bala'i inji uban wa?" Ta fad'a tana cizon yatsa

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now