Me ya zan yi da ita?
A razane Shatu take kallonsa ta ce "Kamar ya ta mutu?" Da sauri ya yi parking a gefen gidansu ya ce "Haka suka ce min, ki shiga gida bari naje na yi confirming." Shatu ta yi shiru tana nazarin abin tabbas a matsayin karatunta yaci ace ta fahimci shiri ne, don haka ta ri'ke hannunsa "Ba zaka je ba, idan kuma zaka je ba dai kai kad'ai ba, muje tare a nemi police su shiga lamarin, idan yaso ni da police d'in mu tsaya daga waje sai kai ka shiga ciki." Shiru ya yi yana nazarin maganarta kafin ya girgiza kai "Hakan ya yi muje." Kafin suje kuwa sun kira yafi sau nawa. Basu yi wuyar samun police ba bayan sun yi musu bayanin issue d'in,
Aka basu police uku ciki har da mace suka kuma tafi da motar police d'in.A harabar fundu'k d'in suka yi packing ya ciro waya ya yi dialling numberr da aka kira shi, ba 'bata lokaci aka d'aga Shuwa a gigice kamar gaske ta sanar da shi numberr d'akin da suke. Imran ya shige ciki ya bar su Shatu a reception bayan ya sanar da su room number d'in da yarjejeniyar idan suka ji shiru after just like ten minutes kawai su biyoshi.
Shatu tana kallo ya shige lifter d'in kawai sai hankalinta ya kasa kwanciya zuciyarta ta dinga bugu.
A bud'e ya tarar da room d'in kasancewar apartment ne suka kama mai room and parlour. Shuwa da zainab suna zaune a parlourn da alamun tashin hankali a fuskokinsu, suna ganinsa suka mi'ke a kid'ime Shuwa tana sake matsar hawayen 'karya ta ce "Shiga tana ciki Imran Shaheedah tazo sa'i da ambaton sunanka ta cika." Imran gaba d'aya ya gigice ko bakomai akwai dangantaka da ya zama dole ya damu da mutuwarta, da sauri ya danna kansa cikin d'akin dai-dai lokacin da ya su'bale ji kake tim ya fad'i a 'kasa cikin azama Shaheedah da ta riga ta gama shirinta ta yo kansa da ruwan maganin a cup ta saka masa a bakinsa azaba ta saka shi kur'be ruwan da aka zuba maganin bugarwar a ciki, yana ware ido alamar mamakin ganin Shaheedah da ranta, mintuna biyu sunyi yawa maganin ya fara aiki take idonsa ya rufe, Shuwa ce ta taimakawa Shaheedah da uwarta suka d'ora Imran akan gado, ta mi'kawa Shaheedah camera kafin ta jinjina mata alamar ta yi aiki mai kyau suka ja mata 'kofar bedroom d'in suka zauna a parlour.
Dai-dai lokacin da Shatu da police suka bayyana a parlourn. A razane Shuwa da Zainab suka mi'ke hannayensu a bakunansu tamkar su zunduma ihu. Shatu cikin tashin hankali ta ce "Ina ku kai min mijina ba?" Ba tayi wani tunani ba ta afka cikin bedroom d'in cikin tashin hankali ta 'kwallara 'kara ganin Shaheedah daga ita sai underwear's tana 'ko'karin hayewa ruwan cikin Imran da ta'ballewa kaf ma'ballen rigarsa da gashi sai boxers na maza, da sauri police d'in suka fad'a bedroom d'in. Ba abinda ya damesu da yanayin da Shaheedah take ciki don su sabonsu ne ganin mata a haka, Shatu ta angaje ta tana dudduba Imran ta ke ta tabbatar da baya cikin hayyacinsa ai kuwa ta sake saka kuka ta nayiwa police d'in bayani, Shaheedah kuwa jikinta tamkar mazari sai rawa take saboda razana da tsorata, musamman ganin police d'in sun zaro handcuffed sun ma'kala a hannunta bayan ta zura doguwar riga a jikinta, haka nan su Shuwa ma ba a barsu ba aka datse hannayensu da handcuffs. Shatu kuwa 'kokari kawai take Imran ya farfad'o ganin yarda ya sandare tamkar gawa. Police d'in ne ya kira doctor ya ce yazo ya duba wani patient suna pera palace hotel. Ya gaya masa room number d'in shi ya tsaya da Shatu, su kuma sauran suka wuce da criminals d'in station d'insu.
Mintuna kad'an Doctor d'in ya d'auka sai ga shi ya bayyana a hotel d'in sabida su sun san kan aikinsu.
Yana dubawa ya tabbatar musu da 'kwaya ce mai 'karfi aka bashi ya sha amma yanzu zai bashi allurar da zata saka 'kwayar ta sake shi in just a minutes.
Ba ayi taking wani time ba kuwa Imran ya farka, duk da yana jin jiri da matsanancin ciwon kai, Shatu ta kamashi ya mi'ke zaune tana shafa masa kansa da ta lura yana sara masa a hankali ya ce mata "muje gida." Police d'in ya taimaka mata suka kaishi mota da kansa ya kaisu gida sannan ya basu compliment card d'insa ya ce su nemeshi zuwa gobe Idan suna son ganin su Shaheedah. Imran ransa yayi masifar 'baci musamman da ya ji sunan Shaheedah ko sunan ba ya bu'katar sake ji balle mamallakin sunan.
Suna zuwa gida ruwa kawai Shatu ta taimaka masa ya watsa sannan ya zube a gadon wani nauyayyan barci ya sake d'ibarsa.
A station kuwa a cell aka saka su Shuwa, hankalinsu a tashe yake sosai musamman sun san nan d'in ba Nigeria bace ba sa bu'katar bribe balle su basu su yi bailing Kansu, ko ina ma suka ga kud'in da zasu basun? Hawaye ya shiga kwarara daga Idanun Shuwa tana da Na sanin Zainab, da tunda suka had'u ba ta mori komai a tare da ita ba sai wahala a da tayi tunanin Idan komai ya kankama zata mallake Shaheedah da ita kanta uwar ta Ta, sai yarda tayi dasu, ta kuma mallake duk dukiyoyin mazajensu shi yasa bata jin shakkar kashe ko nawa ne akan matsalarsu don ita bata dangi a Nigeria daga 'kasar sudan ta gudo tsabar talaucin danginsu a sudan yasa ta barsu ta gudo Nigeria tashin farko ta had'u da Zainab shikkenan suka jone. Tayi tsaki a cell d'innan yafi shurin masa'ki har Zainab ta gaji ta ce "Wai Shuwa tsakin na menene?" A zafafe tace "Na komai ne ma Zainab, Na ba'kin ciki da takaicin had'uwa da ku ne? Duk wani tattalin arziki ne ya kwaranye akan matsalarki da ta 'yarki sam ba 'kashin arziki a tare da ku, don haka da zarar an fita cell d'in zan raba jiha da ku kowa ya kama gabansa don ban ga mamora tarayya ta daku ba." Zainab cikin 'bacin rai ta ce "Ni kai tarayya ta dake ta zame min masifa, kin d'ora ni a bigiren bin bokaye da malamai wanda hakan ne ya janyo min kwaranyewar tattalin arziki na sabida bawa malamai da bokaye kud'ina, ko da haka kika ganni ina ce da arziki na kika ganni shine Dalilin da yasa kika ma'kale min, sai yanzu saboda butulci kinga bani da komai shine zaki ce kowa ya kama gabansa." Shuwa a zafafe tace "Na fad'a d'in kowa ya kama gabansa ko ke d'in 'kanwar uwata ce da zan zauna dake dole daga nan ma da na taho da shiri wallahi 'kasar mu zan wuce.." nan da nan fad'a ya kacime a tsakaninsu kamar za'a bawa hammata iska. Shaheedah kuwa kuka ta ke sosai ji take kamar ta tashi ta rufe su da duka, tabbas yanzu tana da na sanin hawa turbar da suka d'orata da bata sauketa a ko ina ba sai tashar nadama, yanzu waya san irin hukuncin da hukumar 'kasar nan zata zartar musu?
—————-
Fuskarsa ta shiga shafawa a hankali, da kyar ya bud'e idonsa. Murmushi ta haske idanunsa da shi kafin ta sakar masa peck a gefen kumatu, a kunne ta rad'a masa "Please 'kalbeey ka tashi haka wuni fa kayi kana barci ka tashi mu ci Abinci." Da kyar ya mi'ke ta raka shi har toilet ya yi brush sannan ya watsa ruwa a fuskarsa, yanzu kam ya ji dad'in kansa don kuwa ya yi masa sau'ki Sosai.
Madadin saman dinning akan tattausan carpet ta jere musu kwanukan abincin, ya kuwa ci sosai kasancewar wuni yayi bakomai a cikinsa..
Suna gama ci ta kwashe kwanukan tas sannan ta dawo ta sanya 'kafafunsa akan cinyarta tana masa massage a 'kafarsa, dad'in massage d'inne yasa shi lumshe ido take abin ya fara dawo masa kamar a lokacin aka yi shi, bai Ta'ba ganin shashashar uwa irin uwar Shaheedah ba yau kam sun 'kureshi a malejin mamaki. Shatu da ta lura tunani ya afka ta ce "Gobe ya kamata muje station d'in ayi bailing su, su koma Nigeria na tabbatar dai ba za su sake basu lasisin sake shigo musu 'kasa ba." Imran ya bud'e idonsa da suka yi jajur kamar garwashi ya zube su akan Shatu "Ni Zan je nayi bailing su? Ashe kuwa za su tabbata a can, har abada ba zan sake shiga sabgarsu ba." Shatu shiru tayi masa ganin ya d'au zafi sosai.
—————————
A can kuwa station gwamnatin 'kasar ta tattara case d'in ta turo Nigeria, sannan aka tarkatasu aka watso jirgi da sharad'in ba zasu sake shigowa turkeyba. hakan ya faranta musu rai tun a airport kuma suka yi baran-baran kowa ya kama gabansa, shikkenan fa amintakar ta watse dama duk abotar da ba tsoron Allah cikinsa baya tasiri. Allah kasa mu fi 'karfin zu'katanmu.
Tun a airport gwamanatin Nigeria tasa aka yi ram dasu dole ne a
tuhumesu dalilin zuwa su aikata wannan aika-aikar a 'kasar da
ba tasu ba, ashe tsuguni
bata 'kareba, domin dai
kotu ta yanka musu tara ko zaman gidan yari na shekara biyu cif....Nazeefah Nashe
08033748387