42

287 7 0
                                    

Me Zan yi da ita?

Wannan ne complete wancan mistake ne

42

Hafsa da Nahna dariya ta so ku'buce musu sai dai suka gimtse kawai. Yayin da Ammar gabansa ya shiga dukan uku-uku, yaji ganinsa na neman 'daukewa, tashin hankalinsa 'daya kada dai ace Imran kome ya zo yayi da Shatu, tabbas kuwa da zuciyarsa ta buga. Da kuma ya sanya hakan a mizani na rashin halarci matu'kar iyayensu za su sake yarda da Auren Imran da Shatu shi kuma ya tashi a tutar babu da ba'a yi masa adalci ba.

Mommah ta'be baki tayi a fusace tace "Sai ka 'daura himma." Ta mi'ke ma ta bar table 'din gaba 'daya tana 'ko'karin yakice 'bacin ran da ya taso mata, na abubuwan da duk suka faru a lokutan baya. Imran kuwa wucewa yayi da Akram aka fa'darsa zuciyarsa fes da samun mafita don ko ba'a yi DNA ba ya tabbatar wannan 'dan nasa ne ko makaho ya shafa zai yarda da hakan.

A ranar su Hajja su kazo gaisuwa bisa tilastawar Kawu Sa'idu. Har da Zainab aka taho. Lokacin da su Mommah suka zo suka tarar dasu. Zuciyarsu gaba 'daya sai da ta kusan bugawa da suka ga yarda Shatu da twins 'dinta suka Koma. Yara kamar 'diyoyin larabawa jajur dasu ga suma ba'ka si'dik kwantacciya a kansu ga shi jikinsu dumimi a murje gwanin sha'awa. Idanuwan kowa a kansu yake don ma Mommah tana tofe su da addu'oi kafin su shiga taro.

Gaba 'dayansu da kyar suke amsa gaisuwar Shatu ita kuwa ba abinda ya dame ta bayan ta gaishe su mi'kewa tayi ta fice daga sashen gaba 'daya tana mamakin yarda Shaheedah ta koma kamar mai cutar 'kanjamau." A gefe can daga tsakar gida suka zauna ita da Hafsa da Nahna sai suka zamo tamkar wasu fitulu masu haskawa.

Suna zaune su Imran suka shigo, Idanunsa suka fa'da cikin na Shatu tayi saurin 'dauke nata ta mayar kan nasu Akram da suka mi'ke da guru, suka nufesu direct Akram wajen Babansa ya nufa ita kuwa Ikram wajen Uncle Ammar ta nufa. Har sun wuce yaron yace "Uncle caya na amco ciweet a wajen Mimi na." Imran yace okey bari na kai ka, har gurinsu ya 'karasa dashi yaron ya mi'ka mata hannu "Mimi na ciweet." Harara ta zabga masa tace "Ka sauka daga gurinsa ko sai na makeka, ka san shi ne?" Da sauri Imran ya watsa mata idanu yana kallon 'dan 'karamin bakinta da yaji tamkar ya kai mata sumbata a zuciyarsa yace "Sai tsiwar tsiya." Shi kuwa Akram kuka ya saka jin fa'dan da Miminnasa take masa. Cikin zafin rai Imran yace mata "Zaki ba shi ko sai na 'bata miki rai? Ni kike cewa kuma bai sanni ba ko? Daga ke har mijinnaki ku saurari sammaci zan ji dalilin da yasa kika yi aure da cikina a jikin ki." Murgu'da masa baki tayi har da 'dan guntun tsakin ta. Imran ya wara ido kafin yace "Ni kike yiwa tsaki?" Ta sake zuba masa harara ta 'dauke Kai. A zafafe ya juya da yaran a hannunsa ya ma fasa shiga gidan mutuwar sai yaje asibiti anyi DNA test 'dinnan. Idan kuwa ya tabbatar da yaron nan 'dan sa ne wallahi sai yaci uban mijinta, sai kuma yayi shari'a da wanda ya 'daura mata aure da cikinsa a jikinta. Tunanin da ya dinga yi kenan yana driving a motar da ya kar'bi key 'dinta wajen drivern Alhaji Baba.

Sun da'de a asibitin kafin result ya Fito, a hakan ma don ya sakar musu ku'dine kuma private hospital ne. Sakamako dai ya nuna yaro nasa ne. Likitan cikin tsokana yace "Ai ba sai kayi DNA ba kamanninka da yaron kamar kayi kaki ka zubar ya isa a shaida 'dannan naka ne ko tantama babu." Imran murmushi yayi yana kar'bar takardar as evidence zuciyarsa a dugunzume da 'bacin ran da wani banza can ya aurar masa mata, ya raya a ransa wallahi sai ya 'daureshi kuma shari'a zasu zuma da shi har kotun 'Koli.

A zafafe ya koma gidan mutuwar, ya tarar su Hajja har sun fito zasu tafi, don haka antsaitsaye suka gaishe shi har zai wuce Hajja tace cikin 'bacin rai "Imrana idan ka sami lokaci ka zo ina son ganinka in ji dalilin wannan rama ta tashin hankali da Shaheeda tayi." Wani kallo ya jefi Shaheedan dashi kafin yace "Ai bani zaki tambaya ba ita zaki tambaya dalili tunda ni dai ina bata ci da sha, ina kuma sauke mata duk wani hakkinta na aure." Daga haka yasa kai ya shige gidan a ransa yake fa'din "Ke ce wannan yake a gabanki ni ba shi bane a gabana." Gaba 'daya sak su kayi suna kallonsa tare da tsananin mamakin sauyawarsa kamar ba Imran ba da suke juyawa son ran su. Hawayen takaici ya zubowa Shaheeda tace "Hajja kun ga abinda nake gaya muku ko?" Hajja ta girgiza kai "Na gani ba shakka wannan karan Dijah da 'karfinta take, to wallahi gidan ta tarar mu zuba ni da ita shege ka fasa jar uba! Ban ga ta zama ba. Zainab ma da falmata da ran su ya gama dugunzuma ya 'baci suka dinga sakin maganganu da alwashi iri-iri na son rai da ba'kin hali a zuciyarsu.

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now