59

207 8 0
                                    

Nazeefah Nashe

Shikkenan Shatu tayi shiru da zancen, kafin ta janye jikinta ta mi'ke direct kitchen ta shige Imran murmushi yayi a zuciyrsa ya ce sai kace iya girkin ta yi, saboda tun ranar da tayi 'kwa'ba ya hanata yin girkin ya zata da gasken bata iya ba.

Nutsuwa tayi sosai ta fara shirin girkin da zata yi Mandi Rice sai patoosh salad da steam bread tayi sai kuma ta had'a shredded chicken, tuni gidan ya bad'e da wani daddad'an 'kamshi da ya farkar da Imran daga barcin da yake akan three sitter a parlour d'in.

Mamaki ya kamashi jin yanayin 'kamshin tamkar a restaurant wato da gaske dai Shatun girki take, shi tsoron shiga kirchen d'in yake shi yasa bai shiga ya hanata ba ko kuma ta saka masa rigima.

Yana zaune ta fito ta fara arranging abincin a dinning ta gama komai sannan ta shiga wanka.

Tsaf ta fito cikin wani sassau'kan lace mara nauyi ta kashe d'aurin ta kana ganinta kaga cikakkiyar bahaushiya don yau kam har da sar'ka da d'ankunne aka saka ga bakin nan ya ji red lipstick duk da shi kad'ai ta saka a fuskarta ba 'karamin kyau ta yi ba.

Tunda ta fito Imran ya kasa janye idonta daga kansa ba 'karamin kyau tayi masa ba na fitar hankali, ya dinga godiya ga rabbil izzati da ya bashi kyakkyawar mata. Tana zuwa ta bushe fuskar sa da iskar bakinta, da sauri ya lumshe ido yana sha'kar hucin daddad'an mouthwash d'inta. Ri'ko hannunta ya yi da sauri ta zame "Please 'kalbeey kada ka 'bata min makeup after all ma ni yunwa nake ji." "Mai zaki ci?" Ta guntse dariya tace "Jagwalgwalon abincina mana na gaji da cin abincin garinnan ni baya min test, kai kuma kace ban iya girki ba, amma kuma yau dole kaci abincina." Gabansa ya fad'i sosai yake tsoron cin abincin saboda bai san mai zai tarar ba. Yana kallonta tana zuba masa abincin a ido dai tamkar zai yi dad'i bai san a bakin ba.

Ta saka spoon d'aya a plate idanunta cikin nasa ta bud'e abincin a spoon tace "Ha" ya runtse idanunsa kafin ya bud'e bakin saboda bai san mai zai tarar ba tsami ko gishiri ko yaji? Sai dai ga mamakinsa wani daddad'an test ne ya gauraye bakinsa har bai san sanda ya bud'e ido ba yana tauna abincin ya had'iye cikin tsananin mamaki ya ce "Dama kin iya girki har haka?" Dariya ce taso ku'buce mata tace "Dama gwada ka nayi naga zaka iya zama dani ban iya abinci ba? Alhamdulillah kaci jarabawa, dole nagode wa Mommah da Maman tayseer da ta koya min abincin 'kasashen waje." Hannunta ya kamo ya 'kwace spoon d'in ya dambazo abincin ya fara ci cikin nishad'in don ya dad'e bai ci abinci mai dad'insa ba. Ya cika abincin a bakinsa yace "wacece Maman tayseer d'in?" Tana murmushi tace mai eatery d'in MHD fa? Wato Mara Hamisu Dankaka ba abinda ba tayi har abincin gidan biki, snacks da cakes Na birthday ta 'kware a kowane fanni." Imran ya girgiza kai yace "Tabbas ni shaida ne tunda ga matata ta 'kware ita ma." Shatu ta dubeshi yarda yake cin abincin ba wasa abin har mamaki ya bata. Ta ce "Yanzu ace na yi maka abinda nayi maka kwanakin baya ina yarinya zaka cigaba da cin abincin?" "Menene abinda kika yi min kwanakin baya?" Dariya tayi sosai ta ce "Lokacin da ka tsaneni na ji haushi na zuba maka yawu da ruwan hammata a tea." Yana murmushi ya kamo hannunta "Ban da tona abinda ya wuce Hayateey ai yanzu ko hammatar ina lashe ta tas yawu kuwa nawa nasha? Ko mai na jikinki yanzu bana 'kyamarsa ji nake kamar daga jikina suka fito." Shatu murmushi kawai tayi ba don ta yarda ba ta zuba ruwan tatacciyar pineapple da ta had'a masa sannan ta tara yawu a bakinta ta zuba sosai a ciki ta mi'ka masa. Yana murmushi ya had'a da hannunta ya shanye abinsa tas cikin dad'in rai ya kai mata peck a lips d'inta "Yanzu kin tabbatar?" Shatu cikin farin ciki ta fad'a jikinsa kawai tana tsananin murna. Sai da suka nutsu da kansa ya zuba abincin ya dinga bata har sai da tace ta 'koshi, sosai yake mamakin yawan cin abincinta gashi ta 'kara murjewa duka wasu halittun jikinta sun sake cika sun tumbatsa kamar ana hura musu iska.



———————————

Hameedah ta dur'kushe gaban Mommah tana hawaye sosai ta ce "Please Anty Dijah ki yafe min wallahi ina jin ha'k'kinki ne yake d'awainiya da ni, gaba d'aya Habib ya juya min baya tunda na dawo gida bai nemeni ba ko a waya Shuwa ta riga tada gama dashi da asirinta."
Mommah tana murmushi ta kamata tausayinta sosai ya ratsa zuciyarta, dama ita bata ri'kesu da komai ba tuni ta yafe mata, kuma kullum ta yi sallah sai ta ro'ki ubangiji ya daidaita tsakanin Hameedah da mijinta, idan ma asirin ne a jikinsa Allah ya ruguza kaidinsu saboda ko bakomai 'kanwar mijinta masoyinta ce, wanda in dai Hameedah na cikin rashin nutsuwar zuciya ta tabbatar itama na ta mijin zuciyar tasa ba zata nutsu ba ko da kuwa ya nuna mata bakomai, ta san zance kawai ya ke. Musamman Hajja da shekarun girma suka kamata yau lafiya gobe cuta, wannan nema dalilin da yasa tasa Manga yada dawo da Hajjan kusa da ita, ita ke kula da Hajja da abincinta da magungunanta na hawan jini da ciwon sugar. Sosai ta d'au Hajja matsayin uwa ba suruka ba, yarda zata kula da babarta ba tantama haka zata kula da mahaifiyar mijinta domin itama uwa ce.

Me Zan Yi Da Ita?Where stories live. Discover now