Me Zan yi da ita?
Nazeefah Nashe
Wattpad
@Nazeefah38108033748387
—————————-
Bayan wata hud'u, zuwa lokacin tuni cikin Shatu ya girma ya zama 'kato masha Allah wata bakwai cif, amma da kyar take iya d'aga 'kafarta.
Suka fara shirin tafiya Nigeria, Imran tuni ya kammala musu duk wata siyayyarsu ta haihuwa duk da ba wanda ma ya san da cikin ko Mommah bata sani ba, kasancewar ya san matar Ammar ma tana da cikin tare ya siya musu komai domin ko edd d'insu 2 weeks ne kawai banbanci matar Ammar zata riga Shatu kenan.
Ranar wata friday jirginsu ya dirga a Nigeria, suma su Ammar cikin dare zasu sauka dama sun had'a bakin surprising za suyi wa Mommah.
Abokinsa Khalil ya kira ya d'aukesu. Sai ko tsiya yake masa Da yau mun ga abinda zaka yi da ita ko da yake tun akan twins muka san abinnaka cika baki ne dama wa Allah zai bawa wannan kyautar ya banzatar da ita?" Murmushi kawai Imran ya ke yana sosa 'keya d'aya hannunsa kuma cikin na Shatu yana mammatsa mata shi kasancewar ya kumbura suntum.
Nocking d'in da ake ne yaja hankalin Mommah da take kitchen, faten Accra take dafawa Hajja, da sauri ta fito duk da ta san Hajjan na parlourn ta san ba zata iya mi'kewa ba saboda ciwon 'kafa da yake damunta, su Akram kuwa suna Islamiyya, Basirah sun gama ayyukan da zasuyi mata sun shige 'bangarensu guda da Dahda ya ware musu a gidan yayi musu aure da direbobinsa, kowa tana da parlour da d'akuna biyu ga toilet da kitchen duk a parlourn, saboda Mommah tace ba ta son rabuwa dasu, ta riga ta saba dasu tun suna yara.
Turus Mommah tayi da ta bud'e 'kofar taga ba'kin bazata. Ga Shatu da turtsetsen cikinta. Cikin tsananin farin ciki Shatun ta fad'a jikin Mommah ta rungumeta shima Imran bai yi 'kasa a gwiwaba ya rungumeta. Mommah ta ce "Ikon Allah to ku kayar dani ku ba ku ga yarda kuka dawo 'katun-'katun ba, kamar ana hura ku." Dariya sosai khalil ya yi ganin yarda Shatu ta turo baki wai ance mata 'katuwa Mommah ta juya ciki ta ce "To sannu Shatu jaririya zan kiraki kenan kina shirin sake haihuwa ta biyu, don shiririta shine kuka taho ba sanarwa."
Hajja bud'e baki tayi da tsananin farin ciki tana dubansu "Lallai kun iya dirar bazata, zuwa haka bagatatan."
Shatu ta zube a gaban Hajja tana murmushi da mamakin ganin Hajjar ba wani had'in rai da ta ke mata da. Hajja ta ja hannunta mi'ke maza ki zauna a kujera, kawai ya wahalar dake ya kwasoki ra'be-ra'be da ciki, madadin ni ya kirani turkeyn na yi miki zaman da'baro" tsaki Mommah ta ja "Shashancin fa Hajja, ai idan Imran bai yi wautar d'an fari ba baya jin dad'i to waye ma ya san da cikin? Allah dai ya kyauta tunda sun zo lafiya." Shatu ta dinga yi masa dariya 'kasa-'kasa ganin yarda yake ta kumbura baki wai ance masa d'an fari. Mommah kuwa masifa ta cigaba da yi "Ni na san da cikin zan barta ta kai wannan lokacin a can? Kai dai Imran Allah ya kyauta maka." Cikin cunkushewar murya yace "Duk kun sama naji da na sani banzo ba, shima wanda ba d'an farin ba ai yana hanya cikin matarsa ma har yafi na Shatu." Hajja ta saka salati "Wato duk lalatar da za kuyi mana kenan, kuzo ku had'a uwarku da aiki to duk gidajenku zaku tafi." Mi'ke 'kafar Shatu Imran ya yi akan cinyarsa yana matsa mata ita ganin yarda ta kumbura Mommah d'auke kai kamar bata gansu ba, ta shiga kiran su Basirah a waya. Tana sauraran Imran da yake cewa "Ai dama tafiya za muyi." Tsaki ta ja "Saboda a garin mahaukata ake? Ai ko anan garin take a wannan 'katon cikin d'aukota gaba na zanyi balle ka kawota da kanka." Imran bai san sanda ya zaro ido ba ya ce "Mommah... please kada kiyi min haka."
Wani kallo ta watsa masa tana cewa "To idan baka da kunya ai sai ka d'auketa ku tafi." Hajja ta ja tsaki ta ce "Shirmen banza to dama wannan wata kunya ce da shi ji yarda fa ya ke lailayar 'kafarta yana sakin murmushi ko kunyar mu bai ji ba, ai kunya ta yi dama Imrana ya yi hagu, ba su had'a hanya ba ko kad'an gwara ma ki barsu su tarkata su tafi, kafin a gabanki ya dinga abinda zai saki ke kiji kunya, sak halayen ubansa Manga ne a tare dashi yana abu ido wu'ki-wu'ki. To dani kake zancen a d'akina Shatun zata zauna sai naga ko zaka zo ka hai'ke mata a gabana." Mommah mi'kewa ta yi ta shiga kitchen don kunya zantukan Hajja suka saka ta, Imran yana ganin Mommah ta tashi ya ce bari nayi maganin tsohuwar nan "Hajja rufe idonki." A zafafe ta ce "Ubanka Manga yazo ya rufe min, maras kunyar banza." Sosai ya kaiwa Shatu kiss a baki tana gocewa ya buge hannun, salatin Hajja ne yasa Mommah ta fito da sauri daga kitchen dai-dai lokacin da Imran ya ke gyara zamansa yace "Ai sai da nace ki rufe idon ki." Hajja ta ce "Dijah kada ki sake ki bar Imrana anan gidan wallahi
Nan gaba ma a gabana zai hai'kewa matarsa tana gocewa yana sake tura masa harshenta wai shi tantiri irin abinnan dai da ake nuno yahudu suna yi a t'v."
Mommah dariya ce ta so ku'buce mata, shigowar su Yaseerah ne yasa ba tayi ba, suna ganin Shatu suka shiga tsalle Yasirah ta ce wasu 'yan biyun kika 'kunso? Shatu ta zabga mata harara Mommah ta ce "Zaku fara ko ke Yaseerah da laulayinki bayan son warin tattasai wuce ki gyarawa su Imran d'akunansu don Ammar ma yana hanya, ke kuma Basirah wuce muje kitchen." Basirah ta turo baki "Wallahi Mommah 'karya ta ke miki ba wani ba ta san warin tattasai a can'bangarenta wa ke dafawa mijinta abinci?" Shatu ba tayi mamakin aurensu ba don Mommah ta sanar da ita Har ta aiko musu zannuwan gado da flasks. Ta ji dad'i kuma da Mommah ta barsu anan kusa da ita gashi har sun sake gogewa tsaf da su.