Follow me on my Wattpad
@Nazeefah381
Yanayin da ta riskesu ya fi gaban na rubuta, cikin zafin zuciya ta juya ta fice daga d'akin, Imran ya saki tsaki yana mamakin dabbanci irin na Shaheedah, ashe da gaske Shatu ta ke su d'inne suka zo? Ya shiga tunanin me ma ya kawo su? Mai kuma suka zo yi masa?.
'Ko'kari sosai yayi wajen daidaita nutsuwarsa ya mi'ke had'e da fad'awa toilet da kansa ya had'a musu ruwan wanka ya fito mata da wata riga da da kad'an ta wuce cinya mai yankakken hannu, za tayi musun sawa ya ce "Ita nake so ki saka ina son nunawa mutanennan yanzu ni ba sa'an aurensu 'yarsu bane, ina da matar da direct zan iya kiran ta fi kowa kyau a wajen diri kyan fuska kai everything ma." Ya fad'a yana gyara mata gashin da yayi mata drying d'inshi a lokacin.
A gefen jikinsa ya rungumeta (side hug) suka fice daga bedroom d'in cikin murmushi yana rad'a mata special words a kunne da ya sata sakin dariyar da bata shirya ba.
Dariyar da ta ja hankalin su Shaheedah da take zaune tana kuka, d'if gaba d'aya ji da ganinsu ya d'auke cikin matu'kar tashin hankali, su da kansu sun san Shatu ta riga ta zarce Shaheedah da komai ma. Idanunsa 'kasa-'kasa bayan sun zauna Shatu na jikinsa ya ce "Barkanku da sauka, me yake tafe da ku?" Zainab da taji tamkar ta tashi ta rufe shi da duka ta runtse idanunta kawai, Shuwa ce tayi 'karfin halin kawar da kanta ta ce "Imran alfarma muka zo nema duk da dai munzo ba shiri, amma kayi ha'kuri ka mayar da Shaheedah d'akinta tunda dai akwai sauran igiyar aure abinda yasa kenan muka yi tattaki takanas muka zo." Wani kallo ya bisu da shi kafin ya ce "Ki yi ha'kuri tun ina ganin sauran mutuncinku, ku fice min daga nan, Alhamdulillah a yanzu Allah ya tsamoni daga halakar da kuka cillani, ta 'kin bin umarnin mahaifiyata ku ka saka na dinga bijire mata shine yanzu kuke son ku sake mayar dani halaka, ba zan mayar da ita har abada kuma na haramtawa kaina aurenta, ko da ace ban auri Shatu ba balle Aysha ta fiye min duk wata mace in dai da sunan aurena a rayuwata, tana da Qualities da zan iya zama da ita ita kad'ai ba tare da kishiya ba, ta kuma tattare ni'imomi da yawa da ni kad'ai na san sirrinsu, ko na had'ata da wata macen ba zan iya koda kwatanta adalci a tsakaninsu ba balle na aikata adalcin. Kun bani mamaki ma da har kuka yi tunanin zan iya cigaba da zama da ita bayan kamata da nayi da aikata shirka 'kiri-'kiri, godiyata ma ga Allah da bamu had'a zuri'a da ita ba da abin sai ya fi min ciwo da wani ido zan kalli d'an a lokacin da ya tuhumeni me yasa ban samar masa uwa ta gari ba, Am sorry to say ba zan ta'ba sake mayar da aurenmu ba har gaban abada Allah ya bata miji wani kamar ni ko ma mafiyi na."Ji suka yi gaba d'aya kawunan su sunyi nauyi, zu'katansu na na hank'oron 'bacin rai wato duk ku'din da suka kashe ya tafi a banza kenan? Gaba 'daya kuma ku'dinna su suka kwashe a hidimar Shaheedah da niyyar ubangiji zai basu mafiyinsu idan ta koma gidan Imran.
Imran dai da Shatu suna zaune sun zuba musu ido suna mamakin k'arfin hali irinnasu.
Shaheedah ta mik'e cike da confidence ta yi hanyar 'dakin Imran, da sauri ya ce mata "Hey where are you go?" Idanunta da suka rine suka yi jajur ta zuba masa kafin ta ce "Zan tattaro kayana da suke bedroom 'dinka ko ka kwashe ne?" Shatu ta zabura hankalinta a tashe zuciyarta tana bugun kishi, da gaske kayanta na bedroom d'in Imran da su ya ke rayuwa wa ya sani ma ko tsawon lokaci sai ya gansu ya shinshina su ya ke jin da'di in banda haka me yasa bai fito dasu ba?
Ta ja hannunsa suka bi Shaheedahn da sauri cikin 'dakin saboda ba ta so ta saka mata wani abinda 'dakin.
Tsaye Shatu ta yi cak tana kallon ta tana packing kayanta da suke daga gefe 'd'ayansu wardrobe 'din Imran da take a kulle ya ce bai ga key 'dinta ba sai ga shi ita ya ciro key 'din ya bata.
Kamar ta fice amma kishi na cinta ba zata iya fita ta bar Shaheedah da Imran ka'dai a bedroom 'dinta ba don ba ta gama yarda da ita ba.Shaheedah tana kuka ta kwashe kayan tas har trolleys guda biyu, ta fice tana waige bedroom 'din ta cije baki. Akwai abubuwa da tayi targeting sosai a zuciyarta.
Gaba 'daya suka mi'ke suka fice daga gidan cike da sagaggiyar gwiwar rashin cikar burinsu.
Tun a cab d'in da zata kaisu hotel 'din da zasu sauka suke kitsa wacce za su fishshesu, Shuwa cikin zafin rai da takaicin dukiyar da ta 'batar ta ce "Wannan Imran an yi tabbataccen 'dan iska, amma akwai shawara ta 'karshe wadda zaki zage ki yita idan kuma kin 'ki wallahi zan tattara lamarinki na watsar abu 'daya nake so dole na mayar da dukiyoyina da na yi asara ko ku'din zuwa nan nawa ne?" Ta fa'da tana cizon yatsa. "Shawara ta 'karshe dole mu samu duk yarda za'a yi mu jawo Imran hotel 'dinnan ko magani na bugarwa mu zuba masa ya yi having sex dake, wanda zamu 'dau hotonsa mu kuma tabbatar masa idan har bai mayar da ke ba zamu baza hoton a duniya, mu kuma cire fuskarki mu saka ta wata na san wannan shawarar za ta yi aiki."
Zainab ta saki ajiyar zuciya kafin ta girgiza kai ta ce "Tabbas sai dai yarda zamu jawo shi zuwa Hotel 'dinne aiki." Shuwa tana girgiza kai ta ce "Babu wata wuya numberr wayarsa zamu samu, sai mu yi 'karyar Shaheedah ta mutu, na san dole ya zo daga nan sai mu san abin yi ko likita mu kira yayi masa allurar futar hankali ko da Ta 'karfi ne kuwa."
Shaheedah ta yi murmushi tana tantamar lamarin tunda ta san ba Nigeria bane hakan ba mafita bace" ta sanar da su tana girgiza kai, ku dai kira shi d'in idan yaso ni na san yarda zai yaudare shi dole ya kusanceni.Shatu kuwa suna fita daga gidan ta ja fuska ta tsuke da gaske lamarin ya bata haushi, fuskarsa da murmushi ya ke dubanta kafin ya kai hannu ya sakar mata cakulkuli da dole ta dur'kushe tana dariya cikin dariyar ta ce masa "Wallahi naji haushi, shine har da hanani key kace baka ganshi ba, ashe kaya mai amfani ka saka a ciki kayan Lovy d'inka."
Kyakkyawar sumbata ya kai mata bakinta hakan yasa ta yi shiru, yana murmushi ya janye jikinta a kunnenta ya rad'a mata "Shatu Danger!" Ya lumshe ido bayan ya hura mata wata iska a kunne....